Tana Yawan Tunanin Abin Da Ta Aikata Na Sabon Allah A Baya

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum malam ina da wata tambayar. Malam barka da wannan lokaci da fatan anhuni lafiya, malam tambayar itace wata  baiwar Allah, ta kasance abaya tana aikata Saɓon Allah sai kuma yanzu saita gane abin da takeyi bashida kyau sai ta tuba kuma sai ya kasance tana tunana abinda tayi Na saɓon Allah, kuma ta tuba amma malam tanaso ta daina tunawa shin malam shin wata addu'a za'a bata ta daina tunawa??

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikis salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.

    Allah maɗaukakin Sarki da ya halicci Ɗan Adam, ya huwace masa hanyar tuba ne saboda sanin da yayi tun asali cewa lallai Mu 'yan Adan mafiya yawancinmu ajizai ne, wato gajiyayyu. Muna iya aikata abu yanzun nan, kuma bayan nan muyi nadama mu tuba. Wasu lokutan kuma mukan ɗauki watanni ko shekaru cikin aikata miyagun ayyuka cikin saninmu ko rashin saninmu, sannan daga baya mukan tuba mu nemi hanyar komawa zuwa ga samun yardarsa.

    Don haka abu ne mai kyau ga Mumini ya rika yawaita kallon laifukansa tare da Qara neman gafarar Ubangijinsa, domin watakil wannan zai taimakeshi wajen tsaftace zuciya, kaifafa hankali, tare da zage damtse wajen ayyukan alkhairi.

    Duk da cewa kuma awasu lokutan shaiɗan yakan yi amfani da irin waɗannan lokutan domin neman cusawa mumini kokwanto acikin addininsa, ko ruɗani acikin imaninsa, to amma dai tunda kin riga kinyi nadama kuma kin tuba, sai ki cigaba da istigfari da kokari wajen aikata ayyukan alkhairi kamar yadda Allah ya siffanta bayinsa salihai, Yace

    إِلَّا مَن تَابَ وَآمَنَ وَعَمِلَ عَمَلًا صَالِحًا فَأُولَٰئِكَ يُبَدِّلُ اللَّهُ سَيِّئَاتِهِمْ حَسَنَاتٍ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا

    "Sai dai waɗanda suka tuba kuma suka (karfafa)  imaninsu kuma suka aikata ayyuka na kwarai, waɗannan sune waɗanda Allah yake canza munanan ayyukansu zuwa kyawawa. Lallai Shi Allah Ya tabbata mai gafara ne, mai jin kai". (Suratul Furqan Aya ta 70).

    Yana daga cikin sharuɗan tuba, bayan nadama da istigfari da kyautata ayyuka, kuma mutum ya guji kusantar duk abinda zai iya kaishi zuwa ga sake aikata irin wancan kusakuren da ya riga ya tuba daga garesu.

    Misali idan abun ya shafi zina ne ko wasu miyagun Laifuka, to ana so mutum ya nisanci abokai ko Qawaye masu aikata irin waɗannan laifukan domin cigaba da yin tarayya dasu zai iya haifar da matsala. Sannan mutum yayi kokari yayi aure domin kange kansa daga motsawar mummunar sha'awa.

    Idan kuma sata ne ko zamba, to mutum yaje ya nemi sana'a domin gujewa zaman banza, kuma ya kaurace wa duk wasu miyagun abokai da sauransu.

    Hakika Allah mai yawan gafara ne mai jin kai ne ga bayinsa. Kuma yana son masu tuba. Allah ya gaya wa Annabinmu (sallal Lahu 'alaihi wa aalihi wa sallam)

    قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَىٰ أَنْفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِنْ رَحْمَةِ اللَّهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ

    "KACE "YAKU BAYINA WAƊANDA SUKAYI ƁARNA GA KUWUNANSU!! KADA KU FIDDA TSAMMANI DAGA (SAMUN) RAHAMAR ALLAH. HAKIKA LALLAI ALLAH YANA GAFARTA ZUNUBAI BAKI ƊAYANSU, HAKIKA SHI MAI GAFARA NE MAI JINKAI". (Suratul Zumar Aya ta 53)

    Kuma Manzon Allah (sallal Lahu 'alaihi wa aalihi wa sallam) Yace "Hakika Allah yana shimfida rahamarsa da daddare domin karɓar tuban waɗanda suka aikata zunubbai da rana. Kuma yana shimfida rahamarsa da rana domin waɗanda suka aikata zunubai cikin dare su tuba. (Bazai gushe yana yin haka ba) har zuwa sanda rana zata ɓullo daga mafadarta".

    WALLAHU A'ALAM.

    DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.