"Tajsimi" a Falsafar Aristotle da Akidar Asha'ira

    Aristotle shi ne Malamin 'Yan Falsafan da suke dangantuwa ga Muslunci, irin su al-Farabiy, Ibnu Sina, d.s.

    Aristotle yana daga cikin 'Yan Falsafa masu tabbatar da samuwar Allah, a matsayin mai motsa Duniya, amma ba Mahaliccinta ba, (المحرك الأول), don haka ya yi bayanin Siffofinsa, daga ciki akwai cewa; SHI BA JIKI BA NE.

    Yusuf Karam ya ce:

    ((نعود إلى المحرك الأول نتعرف ماهيته فنجد عند أرسطو ثلاث قضايا هي: أن المحرك الأول ليس جسميا - وأنه يحرك كغاية - وأنه معقول ومعشوق))

    تاريخ الفلسفة اليونانية - يوسف كرم (ص: ٢٣٤ - ٢٣٥)

    ((Mu dawo ga Mai Motsa Duniya na farko mu san hakikaninsa, za mu samu wasu mas'aloli guda uku a wajen Aristotle, su ne: Mai motsa Duniya BA JIKI BA NE - kuma yana motsa Duniyar ce a matsay…

    [9:32 pm, 08/09/2024] Umar Aliyu Misau: Shubuhar Masu Sukar Ijma'in Ahlus Sunna

    Ya tabbata Salaf da A'imma na Ahlus Sunna sun yi Ijma'i a kan Haramcin tawaye wa shugaba fasiki. A'imma da yawa sun hakaito wannan Ijma'i. Wannar mas'ala ce ta "Usul" na Mazhabar Ahlus Sunnati wal Jama'a, wacce duk wanda ya saba a wannar mas'ala to ya zama dan bidi'a.

    To sai wasu suke yada shubuhar cewa; -wai- wannan Ijma'i bai tabbata ba, -wai- an samu wasu cikin magabata sun saba, sun yi tawaye wa shugabannin da ake dauka a matsayin fasikai ko azzalumai.

    Alhali wannan sabani da suke rayawa ba sabani ne abin lura ba. Saboda Hussaini (ra) asali tun nada Yazeed bn Mu'awiya bai yi masa bai'a ba. Haka shi ma Abdullahi bn Zubair (ra) bai yi bai'a wa Abdulmalik bn Marwan ba. Kuma ya yi galaba a Hijaz.

    Abdullahi bn Mudee' (ra) kuwa har gida Abdullahi bn Umar (ra) ya je ya yi masa inkari, daga nan ya tuba.

    Sauran wadanda suke ambato cikin tabi'ai kuwa, a fitinar yakin Madina, da fitinar Ibnul Ash'ath d.s sun yi nadama, abin da yake nuni ga taraju'i.

    Saboda haka wannan sabani bai tabbata ba, balle ya zama abin lura.

    وليس كل خلاف جاء معتبرا * إلا خلاف له حظ من النظر

    Wadanda sabaninsu ya tabbata su ne Khawarijawa da Mu'utazila da sauran 'yan bidi'a da suke kan ra'ayin.

    Amma abin mamakin shi ne ka samu mai kwashe-kwashen da zai kwaso maganar su Ibnu Hazm, Alkali Iyadh, al-Bakillaniy, al-Juwainiy, al-Baidhawiy da sauran malaman Asha'ira da wasunsu, -wai- don ya soke Ijma'in Salaf da A'imman Ahlus Sunna suka hakaito, irin su Imamu Ahmad, Ibnul Madiniy, al-Bukhariy, Abu Hatim, Abu zur'ah, Abul Hassan al-Ash'ariy, al-Sabuniy, al-Isma'iliy, al-Dahawiy, Ibnu Batta, al-Lalaka'iy, Harb al-Kirmaniy, Ibnu Abi Zaid al-Qairawaniy, da Ibnu Taimiyya da sauransu.

    Yanzu duka wadannan A'imma na Ahlus Sunna da suka hakaito Ijma'in Salaf a kan mas'alar ba su san an yi sabanin ba kenan, har suka hakaito Ijma'in?

    Wa ya gaya maka sabanin da kake rayawa abin lura ne?

    Wa ya ce maka sabani ne tabbatacce?

    Saboda haka babu wani Ahlus Sunna da ya fahimci Manhajin Ahlus Sunna, da zai yi zaton wadannan A'imma da suka hakaito Ijma'in ba su san da abin da ya faru daga Hussain (ra) da Ibnu zubair (ra) ba, amma duk da haka ba su dauke shi a matsayin sabani tabbatacce ko abin lura ba, shi ya sa ba su lura da shi ba, sai suka hakaito Ijma'in.

    Saboda haka babu sabanin da zai soke Ijma'in Ahlus Sunna a kan haramcin tawaye wa shugaba. Don haka duk wanda ya yi tawayen ya saba Ijma'i, ya fita daga Sunna ya zama dan bidi'a.

    ✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

    Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.