Bature bai Tsara Nigeria don ta Cigaba ba

    Da alama babu saɓani a kan cewa; a yau a Nigeria ana cikin mawuyacin halin rayuwa - Allah ya kawo mana sauƙi -, kuma ana ta tattaunawa a kan sababin shiga wannan yanayi, da kuma neman mafita.

    Ni abin da nake fahimta shi ne; daga cikin manyan sabuba da suka janyo mana halin da muke ciki akwai cin hanci da rashawa. Tushensa kuma shi ne yadda kowa ya ƙudurta cewa; hanyar tara dukiya cikin sauƙi ita ce; siyasa da aikin gomnati. Kowa ya ƙudurta cewa; zai shiga aikin Gomnati ne don ya tara dukiya, ya zama hamshaƙin mai kuɗi. Zai shiga siyasa ya nemi muƙamin shugabanci, ya tara dukiya ya zama hamshaƙin mai kuɗi.

    Alhali a bisa tsarin ƙasashen da suka cigaba a rayuwar Duniya, aikin gomnati da siyasa ba hanyoyi ne na tara dukiya ba. Hanyar tara dukiya ita ce noma da kiwo da kasuwanci. In na ce noma da kiwo, ina nufin noma da kiwo na kasuwanci ba na al'ada ba. Ina nufin wanda mutum zai yi don ya yi kasuwanci, ya nemi riba, ya tara dukiya da su.

    In ka bibiyi ƙasashen da suka cigaba a rayuwa, waɗanda ba su da babbar matsalar cin hanci da rashawa, sai ka samu galibi shugabanninsu da manyan ma'aikatan gomnatinsu ana jera su a layin talakawa ne, ba hamshaƙan masu kuɗi ba. Masu kuɗinsu su ne ƴan kasuwa masu kamfanoni na kimiyya da fasaha da ƙere-ƙere da sauran kamfanoni na noma da kiwo da masu sayan hanun jari a kamfanonin d.s.

    Saboda haka matuƙar Ɗan Nigeria bai cire wannan tunani a zuciyarsa ba, to matuƙar ya samu aikin Gomnati, ko ya zama shugaban siyasa, ko ya riƙe muƙami na siyasa, sai ya ci hanci da rashawa, sai ya tara dukiya ba ta halastacciyar hanya ba. Kuma sai ya lalata ƙasarsa ya kashe ta, daga ƙarshe talakawa su shiga wahala, na yunwa da talauci.

    Yanzu halin da ake ciki na tsadar kayan masrufi, da rashin kuɗi a hanun mutane, kusan a ƙasashe masu yawa ana yin irinsa, amma mu saboda matsalarmu da muke da ita mu kaɗai, a dalilin cin hanci da rashawa, shi ya sa namu talaucin ya fi munana.

    Kuma daga cikin abin da ya janyo haka akwai rashin kishin ƙasa ko ƙarancin hakan. Abin da yake janyo rashin kishin ƙasa kuma akwai rashin haɗin kan 'yan ƙasa. Banbancin Addini da ƙabilanci ba zai bari a samu haɗin kai mai haifar da kishin ƙasa, mai kawo cigaban ƙasa ba.

    To miye maganin wannar matsala?

    Shi Bature a nan rashin hankali ya yi, babu yadda za a yi ka ci nasara wajen jogarantar mutane har sai in ka ɗora tsarin mulkin da kake yi wa mutane bisa abin da mutanen suka yi imani da shi. Kuma galibi hakan yana kasancewa a ɗayan abubuwa biyu:

    1- Al'adu.

    2- Addini.

    Ka duba duk wani wuri da aka samu cigaba a Duniya, za ka samu tsarin Mulkinsu ya ginu ne a kan abin da ya dace da al'adunsu, ko Addininsu. Hatta irinsu Amurka da Birtaniya da Faransa da sauran ƙasashen Turai. Da China da Rasha da sauransu, za ka samu tsarin mulkinsu ya ginu ne kan abin da suka yi imani da shi, na al'adunsu da Addinansu.

    Amma kai a Nigeria, babu al'ada ta bai ɗaya, babu Addini na bai ɗaya, sai aka yi gwamnatin tarayya, to dole ƙyashi ya shigo ciki, a rasa kishin ƙasa, kowane ɓangare ba zai tsaya ya yi abin da zai kawo cigaban ƙasa baki ɗaya ba. Imma saboda ƙabilanci, ko ɓangaranci ko banbancin Addini. Kuma dole sai an wayi gari masu manufa suna danne marasa manufa, su rinjayar da maslahar al'adunsu da Addininsu.

    Misali in ka ɗauki tsarin Shari'a a Nigeria, a kullum danne mabiya Addinin Muslunci ake yi, saboda duk hukuncin da aka yanke wanda ya dace da Shari'ar Muslunci a kotuna na jihohi, to a can sama kotun koli za a warware shi. Sai ya zama a Shari'a an danne Musulmai, an yi watsi da tsarin Shari'ar Addininsu.

    To a haka ta yaya za a samu kishin ƙasa, ta yaya za rabu da cin hanci da rashawa?!

    Don haka tsarin da ake kai a Nigeria ba zai taimaka a samu kishin ƙasa ba, daga nan kuma ba zai taimaka a kawar da cin hanci da rashawa ba, in kuwa akwai cin hanci da rashawa a ƙasa, to ba za a taɓa samun cigaba ba, saboda a kullum sace dukiyar ƙasa za ana yi, a rasa manya aiyuka na gina rayuwa, sai kullum a cigaba da nitsewa cikin tekun yunwa da talauci da jahilci da lalacewar rayuwa.

    ✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

    Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.