Wata rana mun yi rubutu, a ciki sai muka yi ishara cewa; Muslunci shi ne Addinin da Turawa suke yaka. To sai wani daga cikin yaran Turawan masu izgilanci ga Addinin Muslunci yake cewa; ta yaya Turawa za su tsaya su bata lokacinsu wajen yakar Addinin jahilci da cibaya?!
To abu ne sananne cewa; Yaki da yake gudana a yau yaki ne a kan Madogaran tsarin rayuwa. Yaki ne tsakanin tsarin rayuwa da ya ginu a kan Addini, da kuma tsarin rayuwa da ya ginu a kan watsi da Addini (secularism & modernism).
Ita madogarar tsarin rayuwa ta Addini, Addinin Kiristanci da
Addinin Yahudanci sun fadi warwas a gaban tsarin rayuwa bisa madogara ta watsi
da Addini (secularism & modernism). Ma'ana; Addinin Kiristanci da Yahudanci
duka sun gaza wajen tunkarar tsarin watsi da Addini (secularism &
modernism), saboda Addinai ne da aka lalata su aka gurbata su, aka gurbata
littatafan da aka saukar musu.
Shi dai Yahudanci da ma Addini ne na gado da kabilanci ba
Addini ne na kiran mutane su shiga cikinsa ba, mutum ba zai zama Bayahude ba
sai in iyayensa Yahudawa ne, musamman uwarsa mahaifiya. Don haka Addini ne na
kabilanci. Wannan ma yana daga cikin dalilai da suka sa Yahudancin ya kasa
tunkaran tsarin rayuwar watsi da Addini (secularism & modernism).
Amma shi kuma Kiristanci tun tuni ya fadi a gaban madogarar
watsi da Addini (secularism & modernism), tun lokacin da aka gurbata shi
aka shigar da almara masu yawa cikinsa. Babbar almarar da suka kirkira ita ce
cewa; Allah uku ne Allah daya. Da almaran cewa; Allah ya shiga jikin Annabi Isa
(as). Har kuma lokacin da aka shata fagen yaki tsakanin Malaman Coci da Malaman
Kimiyya da Fasaha, inda Coci ya yaki duk wani binciken Kimiyya da aka yi aka
gano Nazariyya da abubuwa na hakika da suka saba ma karantarwan Coci da Bible.
To a nan ma dai Kiristanci ya gaza a wannan dagar da suka yi
da Malaman Kimiyya, wannan ya sa aka yi watsi da Kiristanci a Turai, a koma
tsarin rayuwa bisa madogarar watsi da Addini (secularism & modernism).
Don haka daga nan babu Addinin da ya saura ya tsaya a gaba
tsarin rayuwa bisa madogarar watsi da Addini (secularism & modernism) sai
Addinin Muslunci kawai. Shi ya saura a tsaye tsayin daka babu girgiza a gaban
tsarin watsi da Addini. Saboda babu tufka da warwara a cikinsa, kuma Addini ne
na da'awa da yake kiran mutane a shiga cikinsa, kuma Allah ya tsare Littafinsa
daga gurbata, kuma har yau babu wani binciken Kimiyya na hakika da ya zo ya ci
karo da tabbataccen Nassi na Addinin Muslunci. In kuwa ka samu abin da ya ci
karo da tabbataccen Nassin, to Nazariyya ce kawai ba ta tabbata a bisa hakika
ba.
Amma babu binciken Kimiyyar da aka tabbatar da hakikaninsa
amma kuma ya saba ma tabbataccen Nassi na Addinin Muslunci.
Sa'annan kuma kasancewar Addinin Muslunci cikakke ne ya
shafi dukkan fagagen rayuwa, ya iya yin jawabi a kan dukkan matsalolin rayuwa
gaba daya; fagen Siyasa da Tattalin arziki da Zamantakewa. Kuma Addini ne da
dalilansa dalilai ne na yakini masu karfi da ingancin da babu shakka a cikinsa.
Wannan ya sa tsarin watsi da Addini (secularism &
modernism) ya tabbatar da cewa; lallai babu kalu-bale a gabansa sai Addinin
Muslunci kawai shi kadai. Wannan ya sa ta ko'ina Muslunci aka sa a gaba, saboda
shi ne wanda ya tabbata a tsaye a bisa hakika, babu shiririta ko tufka da
warwara a cikinsa, shi ne Addinin da ba a gurbata shi ba, kuma binciken Kimiyya
da fasaha na hakika ba ya cin karo da shi.
Saboda haka a yau babu yaki na hakika face tsakanin tsarin
rayuwa bisa Madogarar Addinin Muslunci da kuma tsarin rayuwa bisa madogarar
watsi da Addini (secularism & modernism). Don haka Turawa suka tabbatar
cewa; ba su da abin da za su yaka sai Addinin Muslunci.
Babban abin da ya ba da karfi wa madogaran Addinin Muslunci
shi ne saboda Allah ya kare shi, ba a gurbata shi an yi tahrifin Littafinsa ba,
kamar yadda aka samu cikin wadancan Addinai. Kuma Allah ya yi alkawarin kare
wata Kungiya da za ta dawwama a kan wannan Addini, babu abin da zai girgiza su
har sai Alkiyama ta tsaya.
✍️ Dr Aliyu Muh'd Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.