Mahaifiyarsa Ta Umurce Shi Ya Aske Gemunsa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum wa rahmatulLah. Pls ina da tambaya. Malam Inada elder brother, yanzu shekara 1 da aurensa, duk biyayya yana ma mahaifiyar mu, sai dai abu 1 tak yaki yayi mata, tace mar ya aske gemunsa, shi kuma ya ce mata tayi hakuri bazai iya askewa ba, wallahi malam buɗewar bakin mamanmu tace mar in bai aske ba, bazai ga da-kyau ba. Malam hankalina ya tashi har kuka nayi. Malam elder brother na yana kiyaye bin sunna, ina tsoro kar bakinta ya kamashi. shin zai iya askewa malam?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikis salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.

    Babu shakka Allah shine yayi umurni kuma ya wajabta ma bayinsa muminai yin biyayya da kyautatawa ga mahaifansu. Misali irin wannan umurnin yazo acikin suratun Nisa'i inda Allah Yace

    وَاعْبُدُوا اللَّهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا...

    "KU BAUTA WA ALLAH KADA KUYI SHIRKA DASHI, KUMA (YA UMURCEKU)  KU KYAUTATA WA MAHAIFA..." (Suratul Nisa'i Aya ta 36)

    Acikin suratul Isra'i kuma Allah Yace:

    وَقَضَىٰ رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا إِمَّا يَبْلُغَنَّ عِندَكَ الْكِبَرَ أَحَدُهُمَا أَوْ كِلَاهُمَا فَلَا تَقُل لَّهُمَا أُفٍّ وَلَا تَنْهَرْهُمَا وَقُل لَّهُمَا قَوْلًا كَرِيمًا 

    "Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ku bauta wa kõwa fãce Shi, kum game da mahaifa biyu ku kyautata kyautatawa, ko dai ɗayansu ya kai ga tsũfa a wurinka ko dukansu biyu, to, kada ka ce musu 'tir' kuma kada ka tsãwace su kuma ka faɗa musu magana mai karimci. (Suratul Israa'i Aya ta 23)

    Kuma Manzon Allah (sallal Lahu 'alaihi wa aalihi wa sallam) yace "YARDAR ALLAH TANA CIKIN YARDAR MAHAIFA" . Wato duk wanda ke neman yardar Allah, to zai sameta ta cikin samun yardar mahaifansa.

    To amma duk wannan biyayyar da kyautatawar da Allah yayi umurni da ayi musu, awani wajen kuma yace idan suka kiraka zuwa ga saɓa ma Allah kada ka bisu akan haka. Don haka biyayya garesu tana takaituwa ne akan duk abinda ba Saɓon Allah bane. Shi kuwa aske gemu da gangan Saɓon Allah ne tunda Manzo (sallal Lahu 'alaihi wa aalihi wa sallam) yayi umurni acika gemu acikin wani hadisi ingantacce wanda Imamul Bukhariy da Imamu Muslim suka ruwaito, Yace : "KU SAISAYE GASHIN BAKI (WATO KU RAGESHI SAMA-SAMA) AMMA KU CIKA GEMU".

    Acikin wani hadisin kuma wanda Imami Muslim ya kebanta da riwayarsa, Manzon Allah (sallal Lahu 'alaihi wa aalihi wa sallam) ya faɗi dalilin  umurnin. Yace : "KU SAISAYE GASHIN BAKI KUMA KU CIKA GEMU DOMIN KU BAMBANTA DA MAJUSAWA (WATO MUSHRIKAI MASU BAUTAR WUTA).

    Malamai da yawa sun hakaito Ijma'in Maluman mazhabobin Musulunci baki ɗaya bisa wajibcin kiyaye wannan umurnin da kuma haramcin aske gemu. Misali kamar abinda Ibnul Muflihi ya hakaito daga Imam Ibnu Hazmin Al Andalusiy (rahimahul Lahu).

    Kuma yardar Allah da Manzonsa ita ce gaba da yardar Iyaye. Don haka bin umurnin iyaye yana wajabta ne idan ya dace da umurnin Allah da Manzonsa. Amma idan aka samu saɓani tsakanin umurnin mahaifa da kuma umurnin Allah da Manzo (sallal Lahu 'alaihi wa aalihi wa sallam), to umurnin Allah ɗin ake bi a kyale umurnin iyayen. Tunda Manzon Allah (sallal Lahu 'alaihi wa aalihi wa sallam) yace : "BABU BIYAYYA GA WANI MAHALUKI CIKIN SAƁA WA MAHALICCI".

    Wato kada kabi umurnin wani (ko waye, koda malamai ko iyaye) mutukar akwai Saɓon Allah acikin bin umurnin nasu.

    Don haka ki yiwa yayan naki nasiha cewa yayi hakuri yaci gaba da kyautata wa mahaifiyarku tare da tausasa harshe gareta acikin duk furucin da zai fito daga bakinsa. Koda kuwa ita ta gaya masa abinda bai masa dadi ba. Domin kuwa Allah Yace "KA GAYA MUSU ZANCE MAI DADI (CIKIN LADABI DA GIRMAMAWA).

    Mutukar ya kiyaye da wannan, to in sha Allahu babu wani mummunan abu da zai sameshi, sai dai ma alkhairi mai yawa ya biyo baya.

    WALLAHU A'ALAM.

    DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.