Hanyoyin Magance Saduwar Jinnul Ashiq

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum malam inada tambaya : Dan Allah malam ina so a taimaka mun da addu'ar da idan mutum yana mafarkin jannul ashiq (baqin aljani, Namijin dare)  yana kokarin ya sunbanceshi ko kuma ya sadu dashi amma aljanin bai Samu dama ba, dan Allah wata addu'a zai dunga karantawa domin kariya daga gareshi ?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikis salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.

    In dai neman kariya ne daga sharrin kowanne shaiɗanin Aljani, babu kamar ayatul kursiyyi da falaqi da Nasi.

    Idan kinzo kwanciyar barci kiyi alwala kafin kije kan shimfidarki. Sannan idan kinje kafin ki kwanta ki zauna kan shimfidarki ki karanta waɗannan surori da ayoyi kamar haka

    1.Fatiha.

    2. Ayoyi huɗu na farkon baqarah.

    3. Ayatul kursiyyi da ayoyi biyu na gabanta.

    4. Amanar Rasulu har zuwa karshen surah.

    5. Suratul Mulk.

    Duk waɗannan karantasu kawai zakiyi. Amma Qul huwa da falaki da nasi, zaki karantasu ne sau 3-3 (uku-uku)  kina yi kina tofawa akan tafin hannayenki kina shafawa ajikinki.

    Idan kin karanta kafa 1-1 sai ki shafe kashi ɗaya cikin uku na jikinki. Sannan ki sake karanta kafa 1-1  ki shafe tsagin jikinki na dama, sannan ki Qara karantawa ki tofa akan tafukan hannayenki ki shafe tsagin jikinki na haggu.

    Akwai wani magani mai suna Muhrikul Jinn ki nemeshi ki rika shafawa ajikinki. In shaAllahu babu wani shaiɗanin da zai iya kusantowa inda kike.

    Hakanan ki rika turara gabanki da Qaron lubban zakar. In shaAllahu babu shaiɗanin dazai iya zuwa ya sadu dake. Idan ma akwai ajiyarsa agabanki to zaki samu lafiya daga haka. In shaAllahu.

    WALALHU A'ALAM.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.