𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Ɗaga murya da wasanni ko ma hayaniya sun fara yawa a cikin masallatanmu a yanzu, kuma har abin ya fara damun jama’a. Ɗazu liman yana cikin karatun sallar Isha’i sai wani yaro ya ƙwala wa ɗan’uwansa kira da ƙarfi, kamar a kasuwa ko a filin wasa ya ke! Menene hukuncin irin wannan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa
Barakaatuh.
Gaskiyar magana malamai da dama kamar daga cikin
Hanafiyyah da Malikiyyah sun karhanta - waɗansu ma sun haramta - shigar da yara a cikin masallaci,
saboda gudun aukuwar irin waɗannan matsalolin
da ake tambaya a kansu. Sun kuwa kafa dalili ne da cewa, ɗabi’ar yara a koyaushe ta wasa ce da ƙazantarwa ko lalata
abubuwa. Sannan kuma sun janyo hadisai da atharai a kan haka, kamar
Hadisin Wathilah Bn Al-Asqa’i (Radiyal Laahu Anhu)
cewa: Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce
«جَنِّبُوا مَسَاجِدَكُمْ صِبْيَانَكُمْ، وَمَجَانِينَكُمْ، وَشِرَاركُمْ،
وَبَيْعَكُمْ، وَخُصُومَاتِكُمْ، وَرَفْعَ أَصْوَاتِكُمْ وَإِقَامَةَ حُدُودِكُمْ،
وَسَلَّ سُيُوفِكُمْ، وَاتَّخِذُوا عَلَى أَبْوَابِهَا الْمَطَاهِرَ، وَجَمِّرُوهَا
فِي الْجُمَعِ»
Ku nisantar da masallatanku daga yaranku, da
mahaukatanku, da ashararanku, da cinikayyanku, da husumominku, da ɗaga muryoyinku, da tsai da haddodinku, da zare
takubbanku. Ku samar da abin tsarkakewa a ƙofofinsu, kuma ku riƙa sanya musu turare a lokutan taruwar jama’a. (Sunan Ibn Maajah: 750, Al-Arnaa’uut ya ce: Da’eef Jiddan ne.
Domin a cikin isnadinsa akwai Al-Haarith Bn Nabhaan matruuk, da Utbah Bn
Yaqzaan da’eef, da kuma Abu-Sa’eed As-Shaamiy majhuul).
Kodayake wannan hadisin mai rauni ne sosai, amma
dai saƙonnin da yake ɗauke da su sun dace da ruhin musulunci na tsaftacewa da
kiyaye masallatai daga dukkan abubuwan da suke ƙazantar da shi, ko suke cutar da masu ibada a
cikinsa.
Shiyasa malaman suka ƙarfafi wannan riwayar da irin sahihin atharin Umar
Ibn Al-Khattaab (Radiyal Laahu Anhu), wanda a cikinsa As-Saa’ib Bn Yazeed ya ce: Ina tsaye a cikin masallaci sai wani
mutum ya jefe ni da tsakuwa, da na duba sai ga ashe Umar Bn Al-Khattaab
(Radiyal Laahu Anhu) ne. Ya ce: ‘Tafi ka zo min
da waɗancan biyun.’ Sai na zo masa da su. Ya ce: ‘Ku su waye?’
Ko: ‘Ku daga ina ku ke?’ Suka ce: ‘Mu daga Ɗaa’if ne.’ Sai ya ce
«لَوْ كُنْتُمَا مِنْ أَهْلِ البَلَدِ لَأَوْجَعْتُكُمَا ، تَرْفَعَانِ
أَصْوَاتَكُمَا فِي مَسْجِدِ رَسُولِ اللَّهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ»
In da ku ’yan garin nan ne da jikinku ya gaya
muku! Kuna daga muryoyinku a Masallacin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam)! (Sahih Al-Bukhaariy: 470).
Amma riwayoyin da suke nuna halaccin shigar da
yara cikin masallacin, kamar riwayar Abu-Qataadah (Radiyal Laahu Anhu) cewa:
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce
«إِنِّي لَأَقُومُ فِي الصَّلاَةِ أُرِيدُ أَنْ أُطَوِّلَ فِيهَا،
فَأَسْمَعُ بُكَاءَ الصَّبِيِّ، فَأَتَجَوَّزُ فِي صَلاَتِي كَرَاهِيَةَ أَنْ أَشُقَّ
عَلَى أُمِّهِ»
Haƙiƙa! Ina tsayuwa a sallah
ina da nufin tsawaitawa a cikinta, amma sai in ji kukan yaro. Don haka sai in
taƙaita a cikin sallar, don
ƙyamar kar in takura wa
mahaifiyarsa. (Sahih Al-Bukhaariy: 707).
Da kamar riwaiyarsa mai cewa
«أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ -
كَانَ يُصَلِّي وَهُوَ حَامِلٌ أُمَامَةَ بِنْتَ زَيْنَبَ بِنْتِ رَسُولِ اللَّهِ
- صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ -، وَلِأَبِي العَاصِ بْنِ رَبِيعَةَ بْنِ عَبْدِ
شَمْسٍ ، فَإِذَا سَجَدَ وَضَعَهَا ، وَإِذَا قَامَ حَمَلَهَا»
Haƙiƙa! Manzon Allaah (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yana yin sallah a halin yana rungume da
Umaamah Bint Zainab Bint Rasuulil Laah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam), ’yar wurin Abul-Aas Bn Rabee’ah Bn Abdi-Shams. Idan zai yi sujada sai ya ajiye ta,
idan kuma zai miƙe sai ya ɗauke ta. (Sahih
Al-Bukhaariy: 516).
Kuma da kamar riwayar Amr Bn Shu’aib daga babansa,
daga kakansa cewa: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce
«مُرُوا صِبْيَانَكُمْ بِالصَّلَاةِ ، إِذَا بَلَغُوا سَبْعًا
، وَاضْرِبُوهُمْ عَلَيْهَا، إِذَا بَلَغُوا عَشْرًا ، وَفَرِّقُوا بَيْنَهُمْ فِي
الْمَضَاجِعِ»
Ku umurci yaranku da yin sallah idan suka kai
shekaru bakwai, kuma ku buge su a kan barin ta idan suka kai shekaru goma. Kuma
ku rarrabe a tsakaninsu a wurin kwanciya. (Ahmad: 6689, Al-Arnaa’uut ya hassana
shi, amma Al-Albaaniy ya sahhaha shi a cikin Al-Irwaa’: 1/266).
Da sauran riwayoyi dai irinsu, waɗanda suke nuna halaccin shigar da yara a cikin
masallacin, malamai sun ƙayyade su ne da irin abin da ya gabata cewa
* Lallai ya zama yaran waɗanda suke iya natsuwa a cikin masallacin ne, ba waɗanda suke da taurarewa, ko ƙin jin magana ba.
* Kuma ya zama ba waɗanda masallacin ke iya cutuwa da samuwansu a ciki ba ne,
kamar masu lalata kayan masallacin, da ƙazanta shi, da sauransu.
* Kuma su zama waɗanda mala’iku da sauran jama’ar masallacin ba su cutuwa
da su, kamar ta hanyar wasannin banza, da ɗaga muryoyi da maganganun da ba su dace ba.
A ƙarƙashin wannan, lallai
iyaye da jami’an masallaci su ɗauki wannan al’amarin da matuƙar muhimmanci tare da yi masa kyakkyawar fahimta:
* Idan yara wayayyu ne kuma natsattsu waɗanda suke ji da biyayyar maganar manya, ba za a hana su
shiga masallaci ba. Shiyasa ma tun tuni malamai suka yarda da su zauna a
cikinsa cikin natsuwa, domin ɗaukan karatu a
bisa jagorancin malami mai ikon ladabtar da su.
* Amma duk sanda ya zama yaran ba za su kiyaye
wannan alfarmar ta masallaci ba, kamar idan ba za a iya tsare su daga yin
wasanni da aikata sauran abubuwan da ba su kamata ba a cikinsa, to ya wajaba a
nisanta su daga gare shi, domin kare darajarsa da kwarjininsa da mutuncinsa.
* Kuma lallai mu san cewa alhakin duk abin da
yaran suka yi na laifi, yana a kan waɗanda suka ba su
daman shiga cikin masallacin ne, kamar iyayen da sukan turo ’ya’yansu alhali
sun san ba masu natsuwa ba ne. Haka da jami’an masallacin da suke ƙyale yaran suna aikata
wannan ɓarnar, ba tare da tsawa ba.
Kuma dole iyaye da sauran manya su fara zama abin
koyi ga yara a nan. Duk lokacin da manya suka mayar da cikin masallaci wurin
hira da ba’a da raha, har da ɗaga murya da
dariya ko ma tafawa da juna, to zai yi wuya yara su kasa yin koyi da su a wurin
aikata abin da ya fi hakan muni. A yau muna ji da ganin yadda muka kasa
tsarkake masallatanmu daga ƙarar muryar sheɗan daga cikin
wayoyin jama’a. Duk kuwa da tsawa da jan kunne da malamai suke ta yi. Waɗansu matasa ma ban da chatting da ’yan mata, har kallon
fima-fimai suke yi a cikin masallacin! Waɗansu fima-fiman
ma na batsa!!
Laa haula walaa quwwata illaa bil Laah.
Allaah ya shiryar da mu gaba-ɗaya.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
+2348021117734
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.