𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, Allah ya kara wa malam basira, ya halasta mutum ya ji yana so ya mutu ko ya ringa addu'a ya mutu ya huta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salám, 'yar uwa bai halasta mutum ya
ji yana son ya mutu ya huta ba, saboda hadisi ya tabbata daga Abu Huraira Allah
ya qara masa yarda cewa: Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce:
"Kada ɗayanku ya yi burin
mutuwa, kuma kada ya roqi mutuwa ɗin tun gabanin
ta zo masa, domin idan ɗayanku ya mutu
ayyukansa sun yanke, shi kuwa mumini rayuwarsa ba ta qara masa komai sai
alheri." Muslim (2682).
A riwayar Albukhariy kuwa Manzon Allah Sallallahu
alaihi Wasallam cewa ya yi: "Kada ɗayanku ya yi
burin mutuwa, ko dai ya kasance mai kyakkyawan aiki ne wata qila ya qara, ko
kuma mai mummunan aiki ne wata qila ya tuba". Albukhariy (7235).
Wannan sai ya nuna cewa bai halasta mutum ya yi
burin mutuwa ba, kuma bai halasta a roqi Allah ya kawo mutuwa ba.
Harwayau, hadisi ya tabbata daga Sahabin Manzon
Allah Sallallahu alaihi Wasallam Anas ɗan Malik cewa:
Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya ce: "Lallai kada ɗayanku ya yi burin mutuwa saboda wani abin cutarwa da ya
same shi, idan ya zama dole sai ya aikata hakan, to sai ya ce: Ya Allah ka
rayar da ni matuqar rayuwa ce ta kasance mafi alheri a gare ni, ka karɓi raina idan ta kasance mutuwa ce mafi alheri a gare
ni". Albukhariy (5671), Muslim (2680).
Lura da dalilan da suka gabata, bai halasta mutum
ya yi burin mutuwa ba, ko ya roqi Allah mutawa ba, inda ya halasta mutum ya yi
burin mutuwa shi ne idan mutum ya ji tsoron fitinuwa a cikin addininsa, to a
nan mutuwa nesa da fitunuwa a addini ya fi alheri. Haka nan ya halasta mutum ya
yi burin samun mutuwar shahada, akwai hadisai da malamai suka fahimci hakan
daga gare su.
Allah Ta'ála ne mafi sanin dai-dai.
Jamilu Ibrahim, Zaria.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.