Bayanin Nau'in Bincike a Binciken Ilimi

    Za a iya rubuta manazartar wannan rubutu kamar haka: Sani, A-U. (2024). Bayanin nau'in bincike a binciken ilimi. https://www.amsoshi.com/2024/09/bayanin-nauin-bincike-binciken-ilimi.html

    Bayanin Nau'in Bincike a Binciken Ilimi

    Abu-Ubaida SANI

    Department of Languages and Cultures,
    Federal University, GusauZamfara State, Nigeria
    Email: abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng | abuubaidasani5@gmail.com
    Site: www.abu-ubaida.com | www.amsoshi.com
    WhatsApp: +2348133529736

    Binciken ilimi ba nau'i ɗaya ba ne. Yana da nau'uka daban-daban, tun daga kan kundayen digiri har zuwa nau'ukan maƙalu da ake bugawa a mujallu ko waɗanda ake gabatarwa a tarukan ƙara wa juna sani, da dai makamantansu. Kusan kowane irin nau'in bincike aka yi, akwai buƙatar rubuta bayanin binciken a wuri na musamman da ake keɓancewa domin yin hakan. Bugu da ƙari, ba kara zube ake rubuta bayanan ba. Akwai tsari da ƙa'idojin da ake bi domin rubutawa. Ƙa'idojin sukan danganta ga abubuwa kamar haka:

    i. Nau'in binciken kansa (shin kundin digiri ne ko maƙala, da sauransu)

    ii. Wurin da aka gabatar (ƙa'idar rubuta bayanin bincike yana iya bambanta daga jami'a zuwa jami'a, ko daga cibiya zuwa cibiya)

    iii. Lokaci ko shekarar da aka gudanar da binciken (jami'o'i da cibiyoyin bincike sukan sabunta tsarin rubuta bayanin nau'in bincikensu daga lokaci zuwa lokaci)

    Bayanin nau'in binciken ilimi yakan ɗauki ƙwarya-ƙwaryan bayani ne game da abubuwa kamar haka:

    a. Binciken da aka gudanar

    b. Wurin da aka gudanar da binciken

    c. Dalilin da ya sa aka gudanar da binciken

    d. Lokacin da aka gudanar da binciken

    Misalai:

    1. Misalin bayanin binciken kundin digiri na uku:

    A Thesis

    Submitted to the

    Postgraduate School

     USMANU DANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA

     In fulfillment for the Degree of 

     DOCTOR OF PHILOSOPHY 

    (An ɗauko wannan daga wani kundin digiri na uku wanda aka gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, 2012)

    2. Misalin bayanin binciken kundin digiri na biyu

    A DISSERTATION SUBMITTED TO THE POSTGRADUATE SCHOOL, USMANU DANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO,

    IN PARTIAL FULFILMENT OF THE REQUIREMENTS FOR THE DEGREE OF MASTER OF ARTS (HAUSA CULTURE)

    (An ɗauko wannan daga wani kundin digiri na biyu wanda aka gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, 20)

    3. Misalin bayanin takardar da aka gabatar a wurin taron ƙara wa juna sani

    Being a paper presented at an International Conference on the Life and Songs of Alhaji Sa’idu Faru, organized by the Department of Languages and Cultures, Federal University Gusau, Zamfara State, Nigeria, 3rd to 6th May, 2024

    (An ɗauko wannan misali daga wata takardar da aka gabatar a wurin taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al'adu, Jami'ar Tarayya Gusau).

    4. Misalin bayanin takardar da aka gabatar a matsayin jagaban maƙalu (lead paper) a wurin taron ƙara wa juna sani

    Jagabar Muƙaloli wadda aka gabatar a Taron Qara wa Juna Sani na ƙasa da ƙasa a kan Rayuwa da Waƙoƙin Alhaji Sa'idu Faru domin karramawa ga marigayi Sarkin Musulmi na 19 Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar na III wanda aka gudanar a Babban Ɗakin Taro na Tsohon Sashen Yanar Gizo a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau daga 3 -6 ga watan Mayu, 2024.

    (An ɗauko wannan misali daga maƙalar da aka gabatar a matsayin jagorar maƙalu a wurin taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al'adu, Jami'ar Tarayya Gusau).

    5. Misalin bayanin takardar da aka gabatar a matsayin jinga a ajin digiri na uku

    Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto, Nigeria 

    HAU 933: Hausa Culture and Islam

    6. Misalin takardar da aka gabatar a matsayin jinga a ajin digiri na biyu

    A group assignment submitted in the class of HAU 802: Hausa Syntax in the Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto, under the lectureship of Prof. Amfani, A. H, on 7th July, 2019. 

    ***

    Madogara

    Al-Shaibani, G. K. S. (2016). The language of academic writing [PowerPoint slides]. https://www.slideshare.net/DrGhayth2015/presentations.

    APA. (2022). Updates and additions to APA style. American Psychological Association. https://apastyle.apa.org/style-grammar-guidelines/updates.

    Bunza, A. M. (2019). Ƙwarya a farfajiyar adabi da al’adun Bahaushe. East African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature, 2(12), 720-727.

    Bunza, A.M. (2017). Dabarun bincike (A nazarin harshe da adabi da al’adun Hausawa). Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Bunza, A.M. (2018, January 17). Mathematical heritage in Hausa number system: (A proposal for teachingmathematics using Nigerian languages). University Seminar Series, University Research Center, Federal University Gusau, ICT Twin Theatre 1, Federal University Gusau. https://www.amsoshi.com/2018/06/mathematical-heritage-in-hausa-number.html.

    Charles, S. C. (2016). A Six Step Process to Developing an Educational Research Plan. https://medicine.ecu.edu/clinicalsimulation/wp-content/pv-uploads/sites/246/2019/02/SixStepProcessToDevelopingAn-EducationalResearchPlan.pdf.

    Creswell, J. (2015). Educational research: Planning, conducting, and evaluating quantitative and qualitative research (5th ed.). Boston, MA: Pearson Education, Inc.

    Gobir, Y. A. & Sani, A-U. (2019). Witchcraft in the Light of Hausa Culture and Religion. In Academic Journal of Current Research. Vol. 6, No. 12; Pp., 23-30. ISSN (2343–403X); p–ISSN 3244–5621. Available at: http://cird.online/AJCR/wp-content/uploads/2020/01/CIRD-AJCR-19-12033-final.pdf.

    Johnson, B. & Christensen, L. (2004). Educational research: Quantitative, qualitative, and mixed approaches. (2nd ed.). Pearson Education, Inc. 

    Kabir, S.M.S. (2016). Writing research report. https://www.researchgate.net/publication/325546150_WRITING_RESEARCH_REPORT.

    Kauru, A.I. (2015). A handbook for writing project reports, theses, and journal articles. ISBN: 978-937-850-0.

    Livingston, S.A. (2012). How to write an effective research report. https://www.ets.org/Media/Research/pdf/RM-12-05.pdf.

    Murdoch University. (2023). APA - Referencing guide. https://libguides.murdoch.edu.au/APA.

    Online Library Learning Center (n.d.). Steps in the research process. https://www.usg.edu/galileo/skills/unit01/infoage01_04.phtml.

    Purdue University. (n.d.). APA formatting and style guide (7th edition). https://owl.purdue.edu/owl/research_and_citation/apa_style/apa_formatting_and_style_guide/index.html.

    Sani, A-U. & Kurawa, H.M. (2023). Kama da wane ba ta wane: Matakan rairaye bincike daga ba bincike ba. The Nasara Journal of Humanities, 11(1&2), 247-258. ISSN: 1118-6887.

    Sani, A-U. & Jaja, M. B. (2020). Siddabarun zamani: Daga kimiyya da fasaha zuwa dabarbarun daburta tunanin bami. In Al-Nebras International Journal 4th Edition, 2, 28-41.

    Sani, A-U., Buba, U. & Mohammad, I. (2019). Wanda ya tuna bara...: Biɗa da tanadi a tsakanin hausawa matasa a yau. Global Academic Journal of Humanities and Social Sciences, 1(2), 44-50. www.doi.org/10.36348/gajhss.2019.v01i02.001.  

    Shehu, A. (2022). Jaki a rayuwar Bahaushe [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya.

    Shehu, M. (2018). Matakan gudanar da binciken ilimi. https://www.amsoshi.com/2017/07/matakan-gudanar-da-bincike-na-ilimi-2_13.html.

    Shibly, A. (2016). Referencing and Citation. https://www.researchgate.net/publication/305911163_Referencing_and_Citation.

    Sidi, M. (2023). Bature a rubutattun waƙoƙin Hausa [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya.

    Sonmez, S. (2018). "11 Steps" Process as A Research Method. Universal Journal of Educational Research, 6(11), 2597-2603. https://www.doi.org/10.13189/ujer.2018.06112.

    Strongman, L. (2013). Academic writing. Cambridge Scholars Publishing.

    University of Michigan. (2017). Introduction to the research process. https://www.press.umich.edu/pdf/9780472036431-Sec1.pdf.

    University of Otago. (2017). What is Referencing and why is it important? https://www.otago.ac.nz/hedc/otago615365.pdf.

    Yahaya, S. U. (2021). Damben Hausawa a zamanance [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya.

    Federal University Gusau

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.