Allah ya farlanta wa al'ummar Annabi (saw) Salloli guda biyar a cikin kowace rana, haka kuma ya shar'anta mana nafilfili da rawatib (nafilan bayan sallolin farilla) da Witri wadanda suke biye da farillai, saboda abin da yake cikinsu na amfani da fa'idoji da suke na dole a rayuwa da wadanda suke na cikato a rayuwar, a rayuwa ta Addini da ta duniya.
Allah ya ce:
{أَقِمِ الصَّلَاةَ لِدُلُوكِ الشَّمْسِ إِلَى غَسَقِ اللَّيْلِ وَقُرْآنَ الْفَجْرِ إِنَّ قُرْآنَ الْفَجْرِ كَانَ مَشْهُودًا } [الإسراء: 78]
"Ka tsayar da Sallah a lokacin da rana ta yi zawali (ta karkata daga tsakiyar sama), har zuwa duhun dare, da kuma karatun alfijir (Sallar Asubah), lallai karatun alfijir ya kasance abin halartowa ne".
Dukkan sallolin farilla
guda biyar sun shiga cikin wannar ayar, saboda Sallar Azahar da La'asar suna
cikin lokacin da yake bayan zawali zuwa farkon dare, Sallar Magriba da Isha'i
kuma suna cikin lokacin duhun dare ne, sai kuma Sallar Asubahi da Allah ya kirata
da karatun alfijir.
Kuma hadisai mutawatirai game da Sallolin farilla sun zo da bayanin lokutansu da sharudansu da wajibansu da abin da yake cikasu, da kuma bayani a kan falalolinsu da yawan lada da sakamakonsu.
Daga cikin falalolinsu:
1- Su ne ibada mafi
girma da bawa yake samun kaskantar da kai ma Allah, da cikar zuciya da imani da
Allan da girmama shi, wannan kuwa shi ne sinadarin rabautar zuciya rabauta ta
har abada, da samun ni'imarta.
2- Sallah ita ce abincin
zuciya mafi girma, da ruwan da yake shayar da bishiyar imani da jijiyoyinta
suke kafe a cikin zuciyar.
Ita Sallah tana tabbatar
da imani a cikin zuciya, tana girmar da shi, kuma tana girmar da abin da yake
kara imani na aikata aiyukan alheri, kuma tana hani a kan munanan aiyuka da
sharri, kamar yadda Allah ya ce:
{إِنَّ الصَّلَاةَ تَنْهَى عَنِ الْفَحْشَاءِ وَالْمُنْكَرِ } [العنكبوت: 45]
3- Yana daga cikin
falalolin Sallah, kasancewarta ita ce mai taimako mafi girma a kan abin da zai
amfani bawa a lamuransa na Addini da rayuwa.
Allah ya ce:
{وَاسْتَعِينُوا بِالصَّبْرِ وَالصَّلَاةِ } [البقرة: 45]
"Ku nemi taimako (a kan dukkan lamuranku) ta hanyar yin hakuri da yin Sallah".
Taimakon da Sallah take
yi wa bawa a lamuransa na Addini:
Amma ta yadda Sallah
take taimaka wa bawa a maslahohinsa na Addini, lallai idan bawa ya dauwama a
kan yin Sallah ya kiyayeta, kwadayinsa a kan aikata aiyukan alheri zai karfafa,
kuma za ta saukake masa aiyukan da'a, da kyautata wa mutane cikin nitsuwar zuciya
da neman sakamako a wajen Allah, kuma za ta tafiyar ko ta raunana masa abin da
yake kaiwa ga aiyukan sabo.
Wannan kuwa abu ne da yake bayyana a zahiri, ake jinsa a jiki, saboda ba za ka ga wanda ya kiyaye Sallah, na farilla da na nafila ba, face sai ka ga tasirin hakan a kan sauran aiyukansa, saboda haka ne Sallah ta zama tambarin samun rabauta.
Amma kuma ta yadda take
taimakawa a kan maslahohin duniya, shi ne ta yadda take saukaka wa bawa
wahalhalu, kuma take sanyaya masa rai a kan masifu da suke samunsa, kuma Allah
zai yi sakamako wa ma'abocin Sallah da saukake masa lamuransa na rayuwa, Allah zai
sanya masa albarka a cikin dukiyarsa da aiyukansa da dukkan abin da yake hade
da shi.
4- Daga cikin
falalolinta, duk wanda ya cikata, kuma ya kyautatata to ya rabauta.
Annabi (saw) ya ce:
"إن أول ما يحاسب به العبد يوم القيامة من عمله
صلاته، فإن صلحت فقد أفلح وأنجح"
"Lallai farkon abin da za a fara yin hisabi wa bawa a kansa a ranar Qiyama daga cikin aiyukansa shi ne Sallarsa, idan ta gyaru to hakika ya rabauta kuma ya ci nasara".
Daga littafin Sheikh Ibnu Sa'adiy (r): Al- Riyadhun Nadhirah.
A sha ruwa lafiya.
✍️ Dr Aliyu Muh'd
Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.