Wasu Dabi’un Hausawa a Zubin Diyan Wakar Sa’idu Faru ta Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Maccido

    Citation: Ammani, Z. (2024). Wasu Ɗabiun Hausawa a Zubin Ɗiyan Waƙar Saidu Faru ta Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 355-361. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.050. 

    Wasu Ɗabi’un Hausawa a Zubin Ɗiyan Waƙar Sa’idu Faru ta Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo 

    Daga

    Zalihat Ammani (Ph.D).

    Hausa Department
    FCT College of Education Zuba-Abuja
    Phone no: 08034451096
    Email: zalihatammani@gmail.com

    Tsakure

    Babbar manufar wannan takarda ita ce zaƙulo yanayin wasu ɗabi’un Hausawa a cikin wasu ɗiyan waƙar makaɗa Sa’idu Faru, ta Sarkin Kudun Sakkwato. An zaɓi a ɗora wannan binciken a kan ra’in Ɗabi’a da Halayyar Ɗan’adam (Behaviourism Theory) wanda, John B. Watson ya ƙirƙiro a shekarar (1913). Wannan ra’i ne da ya samo asali daga makaranta da wasu masana suka kira da sunan, “Makarantar Tafarkin Horaswa’, wadda aka ƙirƙiro nazari kan ɗabi’u da halayyar ɗan’Adam, tun a zamanin Girkawa a ƙarni na 6K. An yi amfani da hanyoyin tattara bayanai guda biyu da suka haɗa da hanyar sauraron waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru, domin fito da wasu ɗiyan waƙoƙin masu ɗauke da furucin ɗabi’un Hausawa da kuma amfani da littafin Diwanin waƙoƙin baka, juziu’i na biyu da na biyar, na Gusau, (1996:27 da 2020:85). A sakamakon binciken, an gano makaɗan baka, sukan yi amfani da yanayin ɗabi’un al’umma a cikin zubin ɗiyan waƙoƙinsu, domin isar da ƙananan saƙonnin da ake son isar da su ga al’umma. Haka kuma, mun fahimci cewar akan yi amfani da kyawawan ɗabi’un al’umma wajen fito da daraja da ƙima ta wanda makaɗa suke waƙewa. Sannan kuma, sukan yi amfani da munanan yanayin ɗabi’un al’umma wajen kushe ko nuna gazawar abokin adawar gwaninsu, ko kuma abokin sana’arsu. Haka kuma, an gano cewar sarrafa ɗabi’un al’umma cikin waƙa kan sa waƙar ta yi armashi.

     1.0 Gabatarwa

    Al’ummar Hausawa kamar sauran al’ummu na duniya, suna da ɗabi’u na yau da kullum da suke wakana a tsakaninsu.Waɗannan ɗabi’u akwai kyawawa waɗanda ake so da kuma miyagun ɗabi’u waɗanda Bahaushen da kansa yake ƙyamar su, amma ana aiwatar da su. Kodayake gurɓatattun mutane suka fi aikata su. Wasu ɗabi’un sun samu tasirin zamani an daina yin su, wasu kuma an rage gudanar da su saboda samuwa ko ƙaruwar ilimin addinin Musulunci da na zamani. Wasu kuwa ingantasu aka yi suka zama kamar takalmin kaza a wurin Bahaushe, wato, mutu-ka-raba, ma’ana ba za a iya barin su ba. Kyawawan ɗabi’u su ne waɗanda ake so al’umma su ɗauka su kuma riƙa aiwatar wa a lokuta mabambanta domin a sami nagartacciyar al’umma. Ɗabi’u marasa kyau ko miyagun ɗabi’u, su ne waɗanda ake so al’umma ta guje musu. Nazari a kan ɗabi’u kan taimaka wajen tace kyawawa da kuma munanan ɗabi’u, musamman daga bakin mashahuran mutane. Wannan takarda ta fito da wasu ɗabi’un Hausawa ta hanyar bibiyar ɗiyan wannan waƙar ta sarkin Kudun Sakkwato kamar yadda Makaɗa Sa’idu Faru ya fito da su.

    Ɗabi’a wata hanya ce ta ɗan’adam wadda yake aikatawa domin son kansa. Kazalika, ana ganin cewa ɗabi’a halittaccen hali ne wanda mai shi ke aikatawa domin ya biya wa kansa buƙatu. Don haka ne ma Hausawa kan ce: “ Wane yana da halin ƙwarai.” Idan mutum ya aikata ɗabi’a mai kyau, ko kuma akasin hakan, sai a ce, wane ba halinsa ba ne. Wato idan mutum ya aikata wata ɗabi’ar da ba a tsammanin ta daga gare shi (Dunfawa, 2011:3) da (Adoro, 2013:4) da kuma (Ado, 2017:97)

    Kazalika,, Muhammad, (2020:10), ya bayyana cewar: “Ɗabi’a kamar wutsiya ce mai shi takan bi, kuma zanen dutse ne wanda ba a kankare shi, ɗabi’a ko haliya ko taskiya ko al’ada, wasu abubuwa ne da aka san mutum yana aikata su, yau da kullum. Haka kuma, ɗabi’a ita ce abin da aka san mutum yana aikatawa yau da gobe, wanda ba a zaton zai bar shi. Har ila yau, akwai kyawawa da munanan ɗabi’u, waɗanda suke kamantuwa ko ginuwa da wasu halaye da aka san mutum ko dabba ko tsuntsu da aikata su. Ɗabi’a suna ta tara, kamar yadda Bahaushe ya karkasa ta kamar haka:

    Akwai ɗabi’ar halittar ɗan’adam, ita ce wadda Allah ya halicci ɗan’adam da ita, ana iya cewa kowa yana yin ta.

    Haka kuma akwai ɗabi’ar gado, ita ce wadda mutum kan gaje ta daga wajen iyaye ko zuriyyarsa, musamman ta ɓangaren uwa. Bahaushe yayi imani da cewa, an fi gadon wasu halaye daga uwa, bisa dalilin tsotson nono da akan yi. Tabbas, nono daga jini Allah kan samar da shi, to haka shi ma gado ana yin sa ne daga ƙwayar halitta ta jini, wadda ita ma a cikin jini take. Kamar yadda Hausawa ke cewa: “Nono mazaunin hali.”

    Ɗabi’ar naso/ɗauka, ita ce wadda ake koyo ko ɗauka sanadiyyar zama wuri ɗaya da abokan hulɗa. Wannan ne ma ya sa Bahaushe yake cewa: “Zama da maɗaukin kanwa shi ke kawo farin kai” ko “abokin ɓarawo ɓarawo.” Ɗabi’ar sauyin yanayin rayuwa, sakamakon shiga wani yanayi a rayuwa, mutum kan tsiri wasu sababbin ɗabi’u a bisa tilas, ba tare da son ransa ba, (Muhammad, 2020:111).

    1.2 Tarihin Makaɗa Sa’idu Faru Ɗan’umma Rungumi a Taƙaice

    An haifi Makaɗa Sa’idu Faru a garin Faru cikin ƙasar Maradun, Ƙaramar Hukumar Talatar Mafara a wajajen shekara ta 1932. Ana kuma yi masa laƙabi da ‘Ɗan’umma’ wanda matar ƙanen ubansa ta sanya masa, saboda ba ya faɗin sunanta, sai dai yana kiran ta Umma. Shi ya sa ita ma kuma ta dinga kiran sa Ɗan’umma, amma wannan laƙabi bai shahara a tsakanin mutane ba, balle ya danne sunansa na yanka watau, Sa’idu. Shi kansa Sa’idu Faru yakan yi wa kansa kirari yana cewa:

    Ɗan Umma Rungumi,

    Ɗan Tumba Rungumi.

    Sunan mahaifin Sa’idu Faru[1] shi ne makaɗa Abubakar ɗan Abdu, shi kuwa makaɗa Abdu, Alu Maikurya ya haife shi. Ashe ke nan Sa’idu Faru shi ne ɗan Abubakar ɗan Abdu da Alu Maikurya. Asalinsu Gobirawa ne na cikin Sabon Birnin Gobir. Dukkan waɗannan Makaɗa, Makaɗan iko ne, kuma an yi su ne a garin Faru. Amma mahaifiyar Sa’idu Faru mutuniyar Banga ce ta cikin Ƙasar Ƙaura-Namoda[2].

    Sa’idu Faru kamar sauran makaɗan Fada, ya yi gadon kiɗa ta wajen mahaifinsa. Kakansa makaɗa Alu makaɗin kurya ta kiɗin yaƙi ne wadda ake yi wa kirari da, “ Kurya gangar mutuwa.”

    Makaɗa Sa’idu Faru yana da fasaha da naƙaltar harshen da yake waƙa da shi, kuma ya iya zubin waƙa yadda za ta yi kyau da ma’ana. Fahimtarsa ga waƙa shi ya sa yake kiran kansa da malamin waƙa. Dangane da yawan waƙoƙin da Sa’idu Faru ya yi shi kansa ba zai iya ƙididdige yawansu ba, sai dai ya nuna cewa tun sa’ar da ya fara waƙa, bai taɓa komawa cikin wata ba, kuma bai ɗauki waƙar mahaifinsa ya sake maimaita ta ba. Sa’idu Faru yana cewa:

    “Ni kam ba ni iya faɗa maka yawan waƙoƙin da na yi domin na yi waƙoƙi da yawa nawa na kaina tun ranar da na fara tawa ta kaina nike ƙagawa ban yi ta mahaifina ba. Ka san mutum yana iya ɗaukar waƙar babansa ya yi, amma ni tun ran da na tashi ban yi waƙar babana ba, tawa nike yi wadda na ƙaga da kaina kuma na yi su da yawa. Saboda haka da wuya in ce ga yawan waƙoƙina, sai dai wadda ka ji kawai.”

     

    Makaɗa Sa’idu Faru ya fara cin gashin kansa ne a lokacin da ya shirya wata waƙa wadda take ƙunshe da tarin hikimomi[3].

    A fagen kiɗa da waƙa, Makaɗa Sa’idu Faru yana da iyayen gida aƙalla guda huɗu tun daga fara waƙarsa zuwa rasuwarsa. Ga dai jerin sunayen iyayen gidan Makaɗa Sa’idu Faru daga na farko zuwa na ƙarshe. Wato su ne kamar haka:

    1.      Dagacin Banga, Sarkin yaƙin Banga, Alhaji Sale Abubakar, ya yi Sarauta daga (1934-1960).

    2.      Sarkin Kiyawan Ƙaura-Namoda, Alhaji Abubakar Garba, ya yi Sarauta daga (1952-1960.)

    3.      Sarkin Zamfarar Zurmi, Alhaji Suleman Muhammadu Sambo, ya yi Sarauta daga (1991-1971/2).

    4.      Sarkin Kudun Sakkwato, Alhaji Muhammadu Macciɗo, ya yi Hakimta daga (1956-1958). Daga ba ya aka yi masa Sarautar Sarkin Musulmi.

    Makaɗa Sa’idu Faru ya ci gaba da riƙar Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo a matsayin uban gidansa har rasuwarsa. Makaɗa Sa’idu ya yi wa Muhammadu Macciɗo waƙoƙi masu tarin yawa kuma masu ma’ana. Bayan waɗannan iyayen gida na Makaɗa Sa’idu Faru, ya tsallaka wasu Masarautu kamar Kano da Wurno da Kwantagora da Dutsin-Ma da sauran Ƙasashe ya yi musu kiɗa. Makaɗa Sa’idu Faru Makaɗin shiri ne. Wato yana zama da shi da yaransa su shirya waƙa kafin su sadar da ita (Furniss 1996:177). Haka nan idan waƙa ta samu yana yin ta a ko’ina ba tare da ya zauna ya shirya ta ba (Gusau, 1996:121). Ashe ke nan, Makaɗa Sa’idu Faru Makaɗin shiri ne kuma na ƙire. Wasu daga cikin yaran Makaɗa Sa’idu Faru akwai Mu’azu da Muhammad Ɗandodo da Kwaɗo da Aliyu da Ɗandada da Bawa da ‘ya’yansa Ibrahim Abamu da Ibrahim Dage.

    Makaɗa Sa’idu Faru yana da matan aure guda biyu; Zahra’u da Aminatu. Yana kuma da ‘ya’ya maza da mata guda goma sha biyu (12). Zuwa yau Makaɗa Sa’idu Faru yana da jikoki guda arba’in da biyu (42). Makaɗa Sa’idu Faru ya rasu a shekara ta 1987. Watau, ya rasu yana da shekara 55 ke nan a duniya, idan aka yi la’akari da cewa an haife shi ne a shekarar 1932 kamar yadda bincike ya tabbatar ( Gusau,1988 da 1996 da 2011) da (Furniss, 1996).

     2.0 Wasu Ɗabi’un Hausawa a Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

    Hausawa suna da ɗabi’u da yawa, musamman ta wajen mu’amalarsu da take wakana a tsakaninsu da suka haɗa da kyawawa waɗanda kowa kan so ya aikata su, ko kuma a san yana da su. Sai kuma munanan ɗabi’u waɗanda babu mai son ya yi su, ko kuma ya ji ɗan’uwansa na aikatawa koda a ɓoye ne. Wasu daga cikin ɗabi’un Hausawa da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su, a cikin waƙoƙinsa, akwai:

    2.1 Imani

    Ɗabi’a ce ta mutumin da ya ba da gaskiya ga Allah da mala’ikunSa da annabawanSa da littattafanSa da ranar tashin ƙiyama da ƙaddara mai kyau da marar kyau. Ko tausayi ko jin ƙai ko yarda ko amincewa ko gaskatawar wani abu (CNHN,2006:206). Imani kalmar Larabci ce, kasancewar yadda addinin Musulunci ya yi matuƙar tasiri a wurin Hausawa, sai kalmar ta zama ta Hausawa. Makaɗa Sa’idu Faru, ya yi ƙoƙarin fito mana da halayen Muhammadu Macciɗo nagartattu sai ya yi amfani da wannan kalmar a cikn wani ɗa na 17 da ke cikin waƙarsa. Ga abin da ya ce:

    Jagora        :Diba ƙafarka zuwa bisa hannuwa,

    :Zaman Shaihu ne ba wata za’ida,

    :Sarkin Musulmin wataran kake,

    :Da Imani da mu’ujjiza.

     ‘Y/Amshi:Na nan ga malam Macciɗo.

     

    A layi na 4 da ke cikin wannan ɗa na waƙar da muka kawo, Sa’idu Faru yana nuna wannan ɗabi’ar Macciɗo ce, domin shi mutum ne mai yadda da ƙaddara mai kyau da marar kyau, ga tausayin al’umma ga sanin Allah da manzonSa. Irin waɗannan halaye ya sa Makaɗa Sa’idu Faru ya ce “ Da imani da mu’ujjiza na nan ga Mallam Macciɗo.

    2.2 Kyauta

    Kalmar kyauta na nufin ba wa mutum wani abu don ra’ayi ba tare da ya yi wani aiki ba (CNHN, 2006:233 da 271). A she kenan, kyauta wata ɗabi’a ce da Bahaushe ya ɗauke ta da muhimmanci, wadda yake kallon ta a matsayin wata igiya ce mai ƙulla zumunci ko kuma ƙara wa babba girma. Kyauta ita ce ka yi wa wani mutum alheri ko hassafi na kuɗi ko tufafi ko abinci ko dabba da dai sauran makamantansu (Muhammad, 2020:173).

     Makaɗa Sa’idu Faru ya nuna mana ƙarara irin muhimmancin da wannan ɗabi’a ta kyauta take da shi a wurin Hausawa, kamar yadda ya kawo a cikin ɗa na 34, da ke cikin waƙarsa.

    Jagora : Shi ad da halin ga na Bubakar.

    ‘Y/Amshi : Ba da doki garai ba komi ba ne,

    : Shugaban Bauci da Gwambe da Ankara,

    : Baƙon Ƙaura baƙon Zariya,

    : Kana shirye baban ‘yan ruwa,

    : Na Bello jikan Ɗanfodio.

    (Gusau,2020:85).

     

    Idan muka dubi wannan waƙar ta Makaɗa Sa’idu Faru, za mu ga yadda ya bayyana hali ko ɗabi’a a matsayin wata aba ce mai kyau da ake iya gadonta domin ya danganta halin gwaninsa da na mahaifinsa a matsayin masu kyauta, kyautar ma ba ƙarama ba a layin farko da na biyu na waƙar: “ Shi ad da halin ga na Bubakar.” Wato yana da halin sarkin Musulmi Abubakar, amma wane irin hali ko ɗabi’a sai ya ƙara da cewa a layi na biyu: “ Ba da doki garai ba komi ba ne”. Abin nufi a nan dukkansu masu kyauta ne. Dangane da wannan ɗabi’a ta kyauta da yake da ita, ya nuna cewar shi ba ƙaramin mutum ba ne, domin ga al’ada, ba da kyautar doki sai manya masu halin girma.

    2.3 Ƙyuya/Ƙuiya

    Wannan kalma kan ɗauki ma’anoni guda uku (3). Da farko akwai ƙin bin umarnin na gaba, na sanya aiki ko aike. Na biyu kuma shi ne ana danganta kalmar “ƙyuya” da “kasala”, sai ka ji Bahaushe ya ce: “Yau ƙyuya nake” ma’ana “kasala”. Na uku kuwa, akan danganta wannan kalmar ga jariri, misali, in suka ƙi yarda da wani mutum ya ɗauke su, sai a ce: “Yaron nan ƙyuya yake” ( Muhammad, 2020:199).

    A nan ma’ana ta farko ita ce ta yi dai dai da ɗabi’ar da Bahaushe ya fi ƙyama ko rashin ƙauna. Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da karin maganar Hausawa a kan wannan ɗabi’ar domin ya nuna illarta. Ga abin da Makaɗin ya ce a ɗa na 39 layi na farko:

    Jagora :Laifin yaro ƙyuya,

    :Lafin baba shi yi rowa,

    :Ina ƙaunarka Muhammadu,

    :Na tabbata ƙaunata kakai,

    :In kai niyyab ba mu dawakuna,

    :Sabnan bafade sara yakai,

    :Ya ce ko ka ba mu dawakuna,

    ‘Y/Amshi :Ran da salla da tashi ƙaura shi kai,

    :Kana shire baban ‘yanruwa,

    :Na Bello jikan Ɗanfodiyo.

     

    A wannan ɗa na waƙar Makaɗin ya nuna matuƙar cewar shi fa mai biyayya ne, da kuma bin umarni na shugabansa. Shi ya sa ya kawo wannan kalmar a ɗa na farko in da ya ce: “ Laifin yaro ƙyuya”.Yana nuna cewar, ko me ake so ya yi, ya yi, to saboda haka kamar yadda Hausawa kan ce: “ Yaba kyauta tukuici”. Tunda da akwai ƙauna, sai ya yi gugar zana, ko a ce jirwaye mai kamar wanka, in da ya ce: “Laifin babba shi yi rowa”. Makaɗa Sa’idu Faru ya yarda cewa shi yaro ne, na mai gidansa, amma bai son ya tashi bai sami wasu abubuwa muhimmai ba.

    2.4 Rowa

    Wata ɗabi’a ce wadda mutum kan yi na hana ko ƙin ba wa wani abin hannunsa. Rowa ta kasu zuwa kashi biyu (2), mai dalili da marar dalili. Mai dalili ita ce saboda ƙarancin abu ko rashinsa. Marar dalili kuwa ita ce ɗabi’a ko hali da mutum ya gada ko ya koya. Ana iya samun wasu mutanen, rowa halinsu ne, ko da kuwa suna da wadata ko talauci (Muhammad, 2020:210).

    Makaɗa Sa’idu Faru ya siffanta wannan mummunar ɗabi’a da “fuskar shanu” a ɗan waƙarsa layi na 3, kamar haka:

    Jagora : Bisa albarka ɗan Amadu,

     ‘Y/Amshi: Su wane ana miƙa mana,

    : Amma su wane huskar shanu yakai,

    : Macciɗo roƙon doki niz zaka,

    : Kai bari na ci iyakar gargare,

    : Mai roƙon doki don sukuwa,

     : In an ba shi mota karɓa yakai,

    : In an ba shi shabka karɓa yakai,

    : Mai roƙon riga ‘yar Bidda,

    : In an ba shi kore karɓa yakai,

    : Kana shire baban ‘yanruwa,

    : Na Bello jikan Ɗanfodiyo. ( Gusau, 2020:85).

    Idan muka kalli wannan ɗa na waƙar a layi na biyu da na uku, ya kwatanta wani mai kyau da kuma wani marowaci inda ya kira shi da, “fuskar shanu”, mai ake nufi da fuskar shanu? Shi ne turɓune fuska ko rashin annuri da fara’a, wanda ake ganewa ta hanyar yanayin da fuska ta nuna. Bahaushe kan yi karin magana da irin wannan ɗabi’a da cewa: “Sa baka dariya sai hamma”, ko “ shimfiɗar fuska ta fi ta tabarma. Wannan ya nuna cewar ɗabi’ar marowaci idan bai son ya ba da abinsa, sai ya ɓata rai, ya murtuke fuska don ka da ka doso wurin da yake ka tambaye shi ko ka roƙe shi wani abu, saboda haka nema, Hausawa kan ce: “Wasa ma wuri yake da shi”. Makaɗin ya yi amfani da fasaha da ƙwarewa wajen nuna wani marowaci ne, sai ya faɗi halin da ya gan shi a ciki na rashin annuri.

    Haka kuma, a cikin wannan waƙar ta Sarkin Kudun Sakkwato, Makaɗa Sa’idu Faru a ɗa na 39 layi na biyun waƙar, ya sake nuna ɗabi’ar “rowa” ba aba ce mai kyau ba in da ya ce: “Laifin babba shi yi rowa”.

    Anan yana ƙara fayyace wa mai sauraro cewar shi fa wanda ya isa, to ba a san shi da ƙaranta ba, domin rowa ƙaranta ce, gazawa ce. Ɗan’umma ya ƙara da cewa laifi ne a wajen wanda ya isa. Saboda haka, halin rowa ba halin girma ne ba ga al’ummar Hausawa. Haka kuma a irin kyaututtukan da suka nema, sukan samu abun da ya fi hakan ga wanda ya isa, kuma suke roƙo, sannan kuma ga mai rowa ba ya iya ba da abun ma ballantana ya zarce.

     

    2.5 Sara

    Ɗabi’a ce ko al’ada ta mutum da ya saba ko ya keɓanta da ita, ta hana ko sukan wani a wurin wani don ka da a yi masa kyauta ko a ba shi wani abu, ko ma a ɗauke shi da daraja ko ƙima. A ƙasar Hausa an fi sanin irin wannan ɗabi’ar a wajen neman aure. Makaɗa Sa’idu Faru ya nuna wannan ɗabi’ar a kan wani Bafade a wani ɗa na 39 a cikin waƙar Sarkin Kudun Sakkwato layi na 6. Ga abin da makaɗin ya ce:

    Jagora :Laifin yaro shi ƙyuya,

    :Lafin babba shi yi rowa,

    :Ina ƙaunarka Muhammadu,

    :Na tabbata ƙamnata kakai,

    :In kai niyyab ba mu dawakuna,

    :Sabnan bafade sara yakai,

    :Ya ce ko ka ba mu dawakuna,

    ‘Y/Amshi:Ran da salla da tashi ƙaura mukai,

    :Kana shire baban ‘yanruwa,

    :Na Bello jikan Ɗanfodiyo.

     

    A wannan ɗa da muka kawo a sama mun ga in da makaɗa Sa’idu Faru yake nuna ɗabi’ar wasu mutane wacce idan za ayi alheri, su kuma burinsu su hana, sai sukai suka ( sara) dubi layi na 6 in da makaɗin ya ce: “ Sabnan Bafade sara yakai”

    A nan ya kira shi da suna “sabna” wato shashasha wanda bai san mai yake yi ba, domin yakan kai sukan su cewa ko an ba su dawakai to fa su ba mazaunan gari ba ne, ana gama sabgogin sallah za su koma garinsu. Irin wannan ɗabi’a cike take a cikin al’umma, kai ba ka bayar ba, ba ka kuma bari an bayar ba. To duk mai irin wannan ɗabi’a ta sara wato kawo sukan mutane, domin kar su samo wani alkhairi ya zama “sabna” in ji Ɗan’umma.

    2.6 Roƙo

    Shi ma ɗabi’a ce ta mutum, ma’ana neman kyauta ta wani abu daga wajen wani (CNHN, 2006:374). Duk da cewa wannan ɗabi’ar gazawa ce, domin duk mutumin da yake maroƙi ko maroƙiya to wanda ya gaza ne. Amma, a ƙasar Hausa a kan kira makaɗa da sunan maroƙa duk da cewar kamata ya yi kiɗi a kira shi da sunan sana’a, ba roƙo ba. Amma makaɗa Sa’idu Faru a waƙarsa ta Sarkin Kudun Sakkwato ya nuna mana cewar shi maroƙi ne, kuma ɗan gado ne. Ga abin da yake cewa a ɗa na 21:

    Jagora :Ko ni makaɗinka uban zagi,

    ‘Y/Amshi :Na gaji a ba mu dawakuna,

    :Na gaji a ba mu jakunkuna,

    :Na gaji a ba mu garuruwa,

    :Muhammadu in Allah yai nufi,

    :Ka ba mu gari da mutane nai duka,

    :Kana shire baban ‘yanruwa,

    :Na Bello jikan Ɗanfodiyo.

     

    A wannan ɗa na 21, a cikin waƙar Makaɗa Sa’idu Faru ya nuna cewar waƙa da roƙo gado ne a wurinsa. Domin kuwa, ya nuna cewar daman can ana ba su waɗannan kyaututtuka na dawakai da jakunkuna kai har ma da garuruwa da ya zayyano, saboda haka, roƙonsu na musamman ne. Misali a ɗa na layi na 4 inda ya ce: Macciɗo roƙon doki niz zaka. Makaɗin yana nema da a ba shi irin waɗannan kyaututtuka da ya gada, har ma ya yi masa addu’ar idan ya zama sarkin Musulmi gaba ɗai a layi na 5 in da ya ce: “ Muhammadu in Allah yai nufi.” Ma’ana, idan ya zama sarkin Musulmi to ya yi masa kyautar sarauta in da ya ce a layi na 6: “ Ka ba mu gari da mutane nai duka”.

    2.7 Rauni

    Ɗabi’a ce ta nuna rashin ƙarfi ko rashin kuzari (CNHN, 2006:369 ). Wannan ɗabi’ar takan kasance wani rauni ne a zuciya, bayan rauni na zahiri wato rashin kuzari. Raunin zuciya shi ne mutum ya kasa taɓuka wani abun alheri ko alfahari, sai ka samu mutum cikakke, amma yana da rauni a wurin tarbiyya ko a wurin mulki ko a wurin kyauta da sauransu. Makaɗin ya fito mana da kalmar rauni a cikin ɗa na 22 a layi na 8 a cikin waƙarsa. Ga abin da ya ce:

    Mu’azu :Tun ran da Allahu yai duniya,

    :Nan yay yi mutum mai ƙoƙari,

    :Nan yay yi mutum mai kyawo,

    :Kuma yay yi mutum mummuna,

    :Nan yay yi mutum mai haske,

    :Kuma yay yi mutum mai dauni,

    :Nan yay yi mutum mai samu,

    :Kuma yay yi mutum mai rauni,

    :Nan yay yi mutum ɗan Sarki,

    :Kuma ya aza bawan Sarki,

    :Nan yay yi mutum mai iko,

    :Kuma ya aza mai roƙo nai,

    :Albarkar Nana Uwad Daje,

    ‘Y/Amshi :Ku ba mu doki Mamman Sarkin kudu,

    :Kana shire baban ‘Yanruwa,

    :Na Bello jikan Ɗanfodiyo.

     

    A wannan ɗa na waƙar Sarkin Kudu, makaɗin ya fito da halaye da siffar Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo tare da kore wasu raunannun ɗabi’u ko halaye. Ɗabi’u irin su “ƙoƙari”, “iko”, da siffofi irin su “kyawo” da “haske” da “samu” tare da matsayi na “ɗan sarki” duk yabo ne da zuga da ɗaga darajar wanda ake waƙewa. Kuma ya ɗora masa su a matsayin ɗabi’unsa da siffarsa da matsayinsa. Amma, munanan ɗabi’u da siffofi sai makaɗin ya jingina su ga “Bawa” da kuma “mairoƙo”. Ɗabi’u irin su rauni da siffofi irin su mummuna tare da matsayi na ƙasa a cikin al’umma, duk sai ya jingina su gare su. A nan, ya nuna cewar Sarkin Kudun Sakkwato Alhaji Muhammadu Macciɗo ba mai rauni ba ne, mutum ne mai ƙwazo da kuzari da himma da sauran makamantansu.

    2.8 Gaba

    Ita ma ɗabi’a ce marar kyau a cikin al’umma, da take nufin ƙiyayya(CNHN, 2006:147). Gaba dai ita ce mutum ya daina yi wa mutum magana ko sallama, har ya yi ta neman ɗan’uwansa da sharri da mugun alkaba’i ya sami mutum. Akan sami masu irin waɗannan munanan ɗabi’u a cikin al’umma. Makaɗin ya yi amfani da wannan ɗabi’a a ɗa na 6 layi na 4. Ga abin da ya ce:

    Jagora :‘Yan Jidda suna tariya da kyau,

    ‘Y/Amshi :Domin sun ga Muhammad Macciɗo,

    :Bajimi jikan Ɗanfodiyo,

    :Mai gaba da kai ba zai sha daɗi ba,

    :Kana shire baban ‘yanruwa,

    :Na Bello jikan Ɗanfodiyo.

     

    A nan makaɗin ya fayyace irin farin jinin da Muhammadu Macciɗo yake da shi, dubi yadda mutanen Makka suka nuna masa ƙauna, kawai domin sun gan shi. To, mutumin da ya sami irin wannan ɗaukakar ka ga maƙiyinsa, wanda yake gaba da shi, ba zai ji da daɗi ba sai dai ya mutu.

    3.0 Sakamakon Bincike

     A wannan bincike, an gano makaɗan baka, sukan yi amfani da yanayin ɗabi’un al’umma a cikin zubin ɗiyan waƙoƙinsu, domin isar da ƙananan saƙonnin da ake son isar da su ga al’umma. Haka kuma, mun fahimci cewar akan yi amfani da kyawawan ɗabi’un al’umma wajen fito da daraja da ƙima ta wanda makaɗa suke waƙewa. Sannan kuma, sukan yi amfani da munanan yanayin ɗabi’un al’umma wajen kushe ko nuna gazawar abokin adawar gwaninsu, ko kuma abokin sana’arsu. Haka kuma, an gano cewar sarrafa ɗabi’un al’umma cikin waƙa kan sa waƙar ta yi armashi.

    3.1 Kammalawa

    A wannan bincike kamar yadda aka gani, an nazarci wasu ɗabi’un Hausawa daga cikin waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. A nazarin, an zaƙulo wasu ɗabi’u daga cikin ɗiyan waƙoƙin Sa’idu Faru da aka samar domin su. Daga cikin waɗannan ɗabi’un Hausawa guda takwas (8) guda biyu kyawawa ne sannan guda shida kuma marasa kyau ne. Masu kyau da su ne imani da kyauta. Yayin da marasa kyau ɗin, sun haɗa da rowa da ƙuiya da sara da roƙo da rauni da gaba. An ƙalailaice yadda makaɗin ya sarrafa su a cikin azancinsa. Sannan aka fito da sakamakon da binciken tare da kammalawa .

    Manazarta

    Ado, A. (2017), Ra’o’in Bincike kan Al’adun Hausawa. Katsina: Kanki Classical Media Enterprises.

    Alhassan, H. D. (1982), Zaman Hausawa. Lagos: Islamic Publication Bureau.

    Bunza, A.M. (2006), Gadon Feɗe Al’ada. Lagos: Tiwal Nigeria Limited.

    Bunza, A.M. (2009), Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic Publication Centre Ltd.

    CNHN, (2006), Ƙamusun Hausa. Jami’ar Bayero. Zaria: Ahamdu Bello Uniɓersity Press.

    Dunfawa, A.A. (2003), Ma’aunin Waƙa. Sokoto: Garkuwa Publishers.

    Ɗangambo, A. (1984), Rabe-raben Adabin Hausa da Mahimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph Publication.

    Ɗangambo, A. ( 2007), Ɗauraya Gadon Feɗe Waƙa. Zaria: Amana Publishers Limited.

    Furniss, G. (1996), Peotry, Prose and Popular Culture in Hausa. International African Library. London: Edinburgh University.

    Gusau, S.M. (1988), “Waƙoƙin Makaɗan Fada: Sigoginsu da Yanaye-yanayensu a Ƙasar Sakkwato”. Kundin Digiri na Uku. Kano: Jami’ar Bayero.

    Gusau, S.M. (1993), Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Gusau, S.M. (1996), Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kaduna: Ɗab’in Fisbas Media Services.

    Gusau, S.M. (2011), Tarihi da Hanyar Nazarin Waƙar Baka Bahaushiya a Taƙaice. A Cikin Waƙoƙin Baka na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Ltd.

    Gusau, S.M. (2014), Diwanin Waƙoƙin Baka, Juzu’i na Biyu. Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau, S.M. (2020), Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i na Biyar, Matanonin Wasu Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Baka. Sudawa: Commercial Printing & Publishing.

    Muhammad, Y.M. (2003), Adabin Hausa. Zaira:Ahmadu Bello University Press.

    Muhammad, M.S. (2020), Bahaushiyar Al’ada. Kano: Bayero University Press.



    [1] Alu Maikurya Makaɗin Sarakunan Gobir ne wanda ya yi musu kiɗan yaƙi a lokacin da ake yaƙe-yaƙe. Bayan Turawa sun ci Arewa da yaƙi a shekara ta 1903, sai aka canja yanayin kiɗan yaƙi da na noma, ya koma kiɗan fada, wannan ya sa kakan Makaɗa Sa’idu Faru da mahaifinsa Abubakar Maikotso suka koma kiɗan kotso suna yi wa Sarakunan Maradun da na Faru da Sauran Sarakuna na wannan yanki nasu.

    [2] A garin Banga ne aka yi jegon cikin Sa’idu Faru kuma a nan ne aka haife shi.

    [3] Wannan waƙa ta Sa’idu Faru ta farko ita ce wadda ya yi wa Sarkin Yamman Faru Alhaji Ibrahim. Gindin waƙar shi ne :

    G/Waƙa : Bi da maza Ɗanjoɗi na Iro,

    : Iro magajin Shehu da Bello.                          

     Get the full PDF here:

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.