Citation: Sulaiman, M., Agigi, A.M. & Madawaki, S.A. (2024). Habaici a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 349-354. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.049.
Habaici a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Na
Maimunatu Sulaiman
Department of Hausa Language.
Zamfara College of Arts and Sciences (ZACAS)
maimunatusulaiman7@gmail.com
(+234) 08032145373
Da
Aisha Muhammad Agigi
Department of Hausa Language.
Zamfara College of Arts and Sciences (ZACAS)
aishamuhammadagigi@gmail.com
(+234) 08062243738
Da
Saifullahi Ahmed Madawaki
Department of Hausa Language.
Zamfara College of Arts and Sciences (ZACAS)
madawakisahmed@gmail.com
(+234) 07068818980
Tsakure
Makaɗa Sa’idu Farusanannen
mawaƙin baka ne na ƙasar Hausa. Wanda ya ƙware sosai wajen
kiɗan fada.Yana da hikima ta tsara magana da ke kambama
wanda yake yi wa waƙa. Manufar wannan
maƙala ita ce: fito da wasu kalamai na
habaici da Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su a
cikin wasu waƙoƙinsa, da auna nauyin waɗannan kalamai na
habaici da yake yi domin fifita wanda yake yi wa waƙa a kan masu adawa, sannan kuma da bayyana matsayin waɗannan kalamai na
habaici a al’adance. Za a yi amfani da hanyar hira da ma’abota ilimi musamman
kan abin da ya shafi waƙar baka. Haka kuma za a yi amfani da hanyar sauraron wasu
daga cikin waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Farudomin samun hujjojin gina
wannan maƙala. Baya ga waɗannan kuma, za a yi amfani da hanyar karance-karancen
bugaggun littattafai da kundaye da mujallu da maƙalu da aka gabatar domin ƙara wa juna sani duk domin samun hujjoji da za su gina
wannan maƙala. Hanyar da aka
ɗora aikin a kanta kuwa, ita ce mazhabar waƙar baka Bahaushiya. Wannan bincike ya gano cewa mafi
yawan waƙoƙin makaɗa Sa’idu Farusuna ƙunshe da habaici. Sannan kuma nauyin wannan habaicin yana
tasiri ga zukatan masu sauraro. A mizani na al’ada kuwa ana danganta wannan
habaici da ƙazafi ko ƙirƙira wani abu ga
wanda ake yi wa wannan habaici. Haka kuma yin wannan habaicin yana nuna nauyin
yadda makaɗin ke kallon masu adawa ko abokan hamayyar wanda ake yi
wa waƙa.
Gabatarwa
Makaɗa Sa’idu Farumawaƙin baka ne wanda ya shahara a fagen kiɗan fada. Yana da
hikima ta tsara magana da ke kambama wanda yake yi wa waƙar, da kuma yin habaici ga abokan hamayyar ubangidan nasa. A cikin tubalan
ginin waƙoƙinsa yakan yi
amfani da habaici, wato wasu maganganu da yake faɗi a fakaice domin
rataya wa wani mutum ko wasu mutane ba tare da fitowa ƙuru-ƙuru ba, wajen bayyana wannan mutum ko
waɗannan mutane. Ganin yana yawaita amfani da waɗannan hikimomi
ne ya ƙarfafa gwuiwar wannan bincike domin
fito da habaice-habaicen da ya yi
a cikin wasu waƙoƙinsa, domin huce
takaicin abokin gabar ubangidansa, da kuma nuna matuqar girman da ubangidansan
yake da shi. Wannan maƙala tayi azamar bada tata gudunmuwa kan
taron ƙarawa juna sani da Jam’iar Gwamnatin
Tarayya ta dake Gusau jahar Zamfara ta shirya domin karrama makaɗa Sa’idu Faru,
lura da tarihi na neman shafe ƙwazon da makaɗan baka sukayi
musamman shi makaɗa Sa’idu Faru. Daga cikin hikimomin nasa na waƙa sai kuma ɗauki habaici domin bada tamu gudunmuwa.
Hanyoyin Gudanar da Bincike
Wannan muƙala ta yi amfani da hanyar karance-karancen bugaggun littafai da kundayen
bincike da mujallu da muƙalu da aka gabatar
a taruka daban-daban na ilimi. Haka kuma, antattauna da ma’abota ilimi musamman abun da ya shafi waƙar baka. Harwayau, an yi amfani da
hanyar sauraron wasu daga cikin waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Farudomin samun hujjojin gina
wannan muƙala. An samo waɗannan waƙoƙi ne a zauren da aka buɗa don ƙarawa juna sani kan taron da za’ayi kan waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru. Haka kuma an nazarci waƙoƙin nasa ta hanyar saurarensu a kaset
da aka naɗi waƙoƙin.
Mazhabar da aka Ɗora Aiki a Kai
An ɗora wannan muƙala ne a mazhabar waƙar baka Bahaushiya. Wannan mazhabar ta fi raja’a ne da
bayar da ƙarfi wajen bayyana (tarihi, asali, da
salsalar waƙar baka ta Hausa da zurfafa bayani kan
turke da ayyana tubalan ginin turke da yanayin sassarƙuwar adabi da al’adu a waƙar baka da nazarin
awon baka da adon harshe da kuma aiwatar da harshe.) Gusau, S.M (2015:23).
Kasancewar aikin nan yana da alaƙa da wannan
mazhaba yasa aka ɗora aikin akanta. Hakan ya sa aka gano mafi yawan waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Farusuna ƙunshe da habaici. Sannan nauyin wannan habaicin yana
tasiri ga masu saurare.
Taƙaitaccen Tarihin Makaɗa Sa’idu Faru
An haifin Makaɗa Sa’idu Farua
garin Faru a cikin ƙaramar hukumar Maradun, Jihar Zamfara
wajajen shekara ta 1932. Ana kuma yi masa laƙabi da “Ɗan Umma” Wanda matar ƙanin ubansa ta sanya masa, saboda baya faɗin sunanta, sai
dai yana kiranta Umma. Sunan mahaifinsa shi ne Makaɗa Abubakar mai
Kotso ɗan Makaɗa Alu mai kurya. Ke nan Makaɗa Sa’idu Faru ya
gaji Kiɗa da Waƙa daga mahaifinsa, wanda shi kuma ya
gadane daga mahaifinsa. Mahaifiyarsa, Halimatu mutuniyar Banga ce da ke
masarautar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara. Duk da yake Makaɗa Sa’idu Farubai
samu ilimin Muhammadiya mai yawa ba, amma ya yi karatun Allo gwargwadon hali da
ya taimaka masa wajen sanin addininsa. Bai yi karatun boko ba, domin haka ne ya
buɗe idanu da sabgar gidansu wato Kiɗa da Waƙa tun yana ɗan karaminsa. Yana da misalin shekara Bakwai (7) aka fara fita yawon kiɗa da waƙa tare da shi, da ya kai kimanin shekara goma (10) ya
soma amshin waqa a ƙungiyar kiɗa ta mahaifinsa
tare da sauran ’Yan uwansa. Da yaga kamar ƙarfinsa ya kawo a sha’anin kiɗa da waƙa, sai ya dakatar da mahaifin nasa daga
wannan sabga, ya ɗauki jagorancin ƙungiyar ya ci gaba da gudanar da waƙoƙin sarakuna kamar yadda ya taras a
gidansu. Bayan soma cin gashin kansa, waƙar da ya fara yi
ita ce ta dagacin garinsu, wato Sarkin Yamman Faru, Ibrahim Abubakar. Misali:
Jagora/Y/Amshi: Bi da maza Ɗan joɗi na Rwahi,
: Iro magajin Shehu da Bello,
Jagora: Dawaya kora ɗimau
na Wakili,
‘Y/Amshi: Dawaya kora ɗimau
na Wakili,
Jagora: Dawaya kora ɗimau
na Wakili,
‘Y/Amshi: Dawaya kora ɗimau
na Wakili,
: Uban S/gida Bello da Yari,
Jagora: Ruwa da Kada…
‘Y/Amshi: Ɗibgau na Magaji,
: Sai tsohon wawa
ka shigas su,
Jagora: Kai ak ko yau ko gobe Maradun,
‘Y/Amshi: Kai ak ko yau ko gobe Maradun,
: Turawa sun bada
Wasiƙa,
Jagora/Y/Amshi: Babu mazan da ka ja maka,
: Jikan Atto bani Usumanu Atiku,
Jagora: Hasken fitila…
‘Y/Amshi: Ba ɗai
da wata ba,
: Tamraro hasken ka subahin,
Jagora: S/yamma inai maka fata…
‘Y/Amshi: Ya Allah ya yi ma tabaruka,
Jagora: S/yamma inai maka fata…
‘Y/Amshi: Ya Allah ya yi ma tabaruka,
: Don girman Lawali da Risala,
: Don hasken Yasin
da Muqama,
: Bi da ɗan Joɗi na Rwafi,
: Iro Magajin Shehu da Bello.
Baya ga Sarkin Yamman Faru, Sa’idu Faru
ya ci gaba da waƙoƙinsa ga sauran
uwayen gidansa kamar Sarkin Yaƙin Banga Sale
Abubakar da Sarkin Kiyawan Kaura Namoda Abubakar Garba da Sarkin Zamfara Zurmi
Sulaiman Muhammadu Sambo, kafin haɗuwarsa da babban ubangidansa, Sarkin
Kudun Sakkwato, Alh. Muhammad
Macciɗo Abubakar III a Shekarar 1953, lokacin da aka kawo shi
Talata Mafara a matsayin uban ƙasa.
Makaɗa
Sa’idu Faru yana da fasaha da naƙaltar harshen da yake waƙa da
shi, kuma ya iya zubin waƙa yadda za ta yi kyawo da ma’ana,
fahimtarsa ga waƙa shi ya sa yake kiran kansa Malamin Waƙa. Ga abin da yake cewa a cikin waƙar da ya yi wa Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo ta Farin cikin Musulmin duniya:
Jagora: Sa’idu Malamin Waƙa,
: Mai kwana ɗumi na Mamman na
Balaraba (Maimaitawa)
‘Y/amshi: Ban wuce gonata da Irina ba,
inda Sarkin Kudu nattsaya.
(Gusau: 1996)
Makaɗa Sa’idu
Farubai yi wa kowa waƙa sai Sarki ko wanda ya jiɓinci Sarauta. Ya kan faɗa cewa idan zaka yi wa talaka waƙa ba
ya da nasabar da zaka danganta shi da ita, musamman ta iyaye da kakanni, amma
idan basarake ya ɓata
maka rai, sai kayi masa habaici cikin waƙar ka, to sai ransa ya ɓace domin ba ya buƙatar abin da zai ɓata nasabarsa (Gusau, 1996:117).
Makaɗa Sa’idu
Faru ya rasu a shekarar 1987, ya bar matan aure guda biyu da “yaya goma sha
biyu, maza shida da mata shida. Ya zuwa yanzu gidansa bai mutu ba a fagen kiɗa da waƙa, domin ɗansa
Alh. Ibrahim Sa’idu Farushi yake jagorantar ƙungiyar kiɗa da ya bari.
Ma’anar Habaici
Habaici, magana ce mai ɓoyayyar manufa.
Akan yi magana da niyyar nufin wani abu ga wanda aka yi maganar dominsa. To
amma, shi habaici, idan ba mutum ya san kan zance ba, ba kasafai ake gane wanda
aka yi habaicin dominsa ba (Ɗangambo, A. 1982).
Habaici shi ne wasu maganganu da ake faɗi
a fakaice domin ratayawa wani mutum ba tare da bayyana mutumin da ake nufi ba ƙuru-ƙuru.
Amma shi wanda ake nufi wani lokacin da wuya ya gane abin da ake nufi da shi
ake yi. (Adamu, 2008:130). Habaici kalmomi ne da ake amfani da su wajen
muzantawa ko tozarta mutum a fakaice, musamman idan ana son a sa mutum a baƙin ciki ko kuma ya
ji haushi, sai a dinga yin magana a kan abin da ya shafe shi ko kuma wasu ɗabi’unshi.
Yahaya
da Zariya da Gusau, da kuma ‘Yar’aduwa (1992) sun ce: “Habaici kalmomi ne da
ake amfani da su a fakaice don muzanta mutum”. “Ɗangambo
(1984) cewa ya yi “Habaici, wata hanya ce ta zagin mutum a fakaice”.
Zarruk
da wasu (1986:47) sun faɗi cewa, “Habaici shi ne ko gugar zana
duk ana nufin abu ɗaya
ne. Habaici shi ne yi da mutum a kaikaice. Habaici ya fi yawa inda kishi ko ƙyashi”.
Habaici
Magana ce da Hausawa ke amfani da ita domin isar da saƙo, a hikimance, azanci da ƙwarewa a cikin
magana. Ana yin habaici saboda dalilai masu tarin yawa ga wasu daga cikin su:
a) Jan kunne
b) Ramuwar gayya
c) Tsokanar faɗa
d) Rowa
e) Hassada
f) Aikata wani muhimman aiki, da dai
sauransu.
Habaici magana ce da ake yi a dunƙule cikin duhu ba kai tsaye ake fito da maganar ba, sai dai
wanda ake yi dominsa ya san da shi ake yi. Kowane ɗaya daga cikin abubuwan da aka zayyana da ma wasunsu, in
suka Faru sai a yi amfani da habaici a cusa wa wanda ake magana da shi haushi.
Makaɗan Hausa sukan yi habaici a cikin waƙoƙinsu. Musamman makaɗan fada, makaɗa Sa’idu Faru yana daga cikin makaɗan fada kuma ya yi habaice-habaice a mafi yawa daga waƙoƙinsa.
Ga wasu daga cikinsu.
Ginidin waƙar: Ba
jinin gidan Mamman na yari,
: Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya.
Jogora: Shi wane girma shi kai bai da
wayo,
Y/Amshi: ya togu daidai shina nan bani
na,
: ya bar azumi da kono da sunnah,
: sai ya ji goge shi ɗauko kujera,
: a shisshirya benci matsata su zanna,
: a aika a ɗauko kwalabe a buɗe,
: da ka gane ka
koma ma Allah,
: ko da inyamuri
yab bi Allah,
: shi ad da shi
babu mai tsarguwatai.
Wannan habaici ne, da makaɗa Sa’idu Faru ya
yi a cikin waƙar da ya yi wa ubangidansa Sarkin Kudu Macciɗo. Inda ya yi wa
abokin adawarsa habaici, inda ya bayyana shi a matsayin wanda ba ya azumi da
kono, da Sunnah. Ga al’adar Bahaushe idan aka ce mutum ba ya ɗaya daga cikin
shikashikan Musulunci to ana yi mashi kallon mutumin banza, duk girmansa duk
asalinsa. Balle ga shi ya lissafa ɗabi’un banza ga mutumin. Waɗannan kalmomi da
ya rataya wa abokin adawar ubangidansa, suna da muni sosai ga rayuwar Bahaushe,
sannan kuma suna da nauyi a zukatan masu saurare. Suna kuma da tasiri da sosa
rai ga wanda aka yi masu. Haka, ya ƙara kwatanta shi
da wanda ba ya farilla, balle ya yi nafila, wato ba ya yin ibadar dole balle ya
yi wadda ba dole ba, wato azumin da kono da ya ce.
Haka, dai ya ƙara fito da habaici a wata waƙa da ya yi wa
Sarkin Yawuri Muhammad Tukur. Ga
abin da yake cewa:
Gindin Waƙa: Koma shirin daga na Bubakar
Jagora: Amma shi ko har da dama-dama,
‘Y/Amshi: Ga wani
Sarki na ta kumburi,
: Da yara nai sun
sha mashi hura.
Jagora: Ga wani Samɓolon uban ƙasa,
‘Y/Amshi: Da yara
nai wajjen guda huɗu,
: Ba ko mai
Suturar kwabo huɗu,
: Ya shiga mota ya yi tagumi,
: Da kwandon ɗunya yay yi guzuri.
(Gusau, S.M (2009:171)
Idan muka dubi waɗannan ɗiyan
waƙar da kyau, za mu ga cewa habaici ne da makaɗa Sa’idu ya yi ga wani Sarki, da wani
ubanƙasa, inda ya kwatanta Sarkin da kumburi wato ya sha toka,
yana fushi, sakamakon ganin ubangidansa.
Wannan shaguɓe ne ya yi ga wani Sarki da yake adawa da ubangidansa.
Kumburi kalma ce da ke nuni da ɓata fuska, sakamakon rashin jin daɗin rayuwa, bisa ga wani abu da ka ji, ko ka gani. Haka kuma
ya yi habaici ga wani ubangidansa da yake adawa da ubangidansa ko kuma ya ɓata masa rai. Wato ya kwatanta shi da
samɓolo, a
al’adar Hausawa samɓolo
yana nufin samna ko sakarai wanda bai san ciwon kansa ba. Don haka, duk wanda
yake da waɗannan
halayen ba zai iya zama sarki ba, don ko kansa ba zai iya riƙewa ba
balle al’umma. Haka dai makaɗa Sa’idu Faru ya ƙara yin habaici a cikin waƙar da
ya yi wa Sarkin Kudu Macciɗo inda ya ce:
Gindin Waƙa: koma shirin daga na Bubakar,
: Gamɗarin Alƙali wan maza.
Jagora: Ga wani Sarki ba shi da zagi,
: To kuma sannan bai da guzuri,
: Garin rogo ɗai suka ta ci da
guru,
: Kowane na aza
ruwa.
Sa’idu Faru ya yi habaici a wannan ɗan waƙa domin ƙara nuna martabar
ubangidansa, da kuma yin shaguɓe ga abokan adawarsa, inda ya nuna ba
ya da zagi. Zagi shi jami’i ne mai shiga a gaban dokin Sarki. Danganta shi da
rashin zagi, tamkar zubar ƙima ce da daraja
ga idon Hausawa. Ya kuma ƙara kwatanta shi
da tawagarsa da rashin guzuri, wato Sarkin talaka ne da garin rogo suke guzuri.
Garin rogo ba cimar Bahaushe bace asali, wahala da yunwa da rashin tabbas kesa
Bahaushe cinsa da kuma yawaitar shi a kasuwanninsu, alama ce ta yunwa a kasarsu.
Ya yi wannan habaicin ne, don ya nuna ƙima da darajar
wanda yake yi wa waƙar, da kuma ƙasƙanta abokan adawar ubangidan nasa.
Sanannen abu ne, a ƙasar Hausa Sarki mutum ne mai arziƙi da cikakken iko, don haka bayyana shi a matsayin akasin
haka, tabbas zai sosa masa zuciya, dama kuwa, wannan shi ne dalilin yin
habaicin: domin ya sosa zuciyar ‘yan adawa ya kuma ƙara ɗaukaka
ubangidansa. Ya kuma huce takaicin zamansa ɗan adawar, da kuma ƙoƙarin tasirantar da hakan, ga zukatan
masu sauraro. Haka kuma, ya yi habaicin ne don ya cusa takaici ga zuciyar wanda
ya yi wa habaicin da kuma fadawansa, ko ‘yan tawagarsa. A cikin waƙarsa ta Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Alhaji Ahmad Muhammad Asha, ya yi habaici kuma ga abun da yake
cewa:
‘Y/amshi: Sarki
yai sarki cigari,
: ya gado rinjaye abu,
: Toron giwa jikan isau,
: Mashasha banwaren Alu.
Jagora:
Kana ta harare-hararenka Daudu,
: Ni dai ban gane
kanka ba,
: Sa babba sata
nig gani,
: Tsohon ɗan sarkin mai kwaɗai,
: Tsohon Ɗan Sarki Angulu,
: Kolo komi
namanka na,
: Kolo komi
namanka na,
: Komi dai kas
samu ka ci.
A waɗannan ɗiyan waƙar, habaici ne makaɗa Sa’idu Faru ya yi ga abokin adawar
Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda. Daudu shi ne Dangaladiman
waƙa, ko kuma duk wani mai jiran gadon
Sarauta ana kiransa da Daudu. A nan Makaɗa Sa’idu Faru yana nuni ne ga Dangaladimansa
Mu’azu cewa ya lura da wani ɗan sarki yana ta harare-harare. Harara wata ɗabi’a ce da take nuna jin haushi game da wani abu da ya damu
mutum.
A nan yana nuna cewa wancan ɗan sarkin yana jin haushin Sarkin kiyawan Kaura. Harwayau,
ya ƙara kwatanta shi da kwaɗayi, kuma ga shi kwaɗayi mummunar ɗabi’a ce wadda take zubar da kima da mutumcin mai yin ta a
idon mutane. Kwatanta shi da ɗan
Sarki muzantawa ne gare shi, da kuma idanun masu saurare. Ɗan Umma ya ƙara yi masa
habaici da cewa Angulu. Angulu dai wani tsuntsu ne, wanda yake cin komai. Wato
komai ya samu zai ci har da ƙazanta. Hakan ya
sa musulunci ya yi hani da cin naman angulu. Ba wanda aka yi wa habaicin ba ko
wanda ya saurari habaicin zai tabbatar da cewa kalamai ne da suke nuna
muzantawa ga wanda aka yi wa su. Musamman a ce ɗan sarki mai
cikakkiyar nasaba. A baya an faɗi cewa, ana yin habaici ne domin huce
takaici ko don mayar da martani da sauransu. Waɗannan kalamai da
suka gabata suna nuna nauyin adawar da yake yi da ubangidansa da kuma huce
takaici game da adawar da yake yi da ubangidansa.
Makaɗa Sa’idu Faru ya kara yin wani habaici
a wata waƙar tasa inda yake cewa:
Jagora: wanga yana haka gurun kolo,
: Wanga na nan haka tandun ba’u,
: Marag gaɓoɓi wat taba,
: Sarki da hangaham baki ya twaɓe?
(Waƙar Sarkin Zamfaran
Zurmi Suleimanu Muhammadu)
A wannan habaicin ya kwatanta abokin adawar maigidansa da
gurun kolo. A zahirin kalmar gurun kolo shi ne sassan jikin kolo idan aka
yayyanka aka soya. Amma a al’adance idan ake ce gurun kolo, shi ne abu wanda ba
ya da wani amfani. Duk yanda ya ji suya ba za a iya cin sa ba, saboda an yi
hani da cinsa a musulunci. Kenan, suyarsa ba shi da wani amfani. Bahaushe yana
yi masa kirari da “gurun kolo ba ka kashin kunya’’ wato duk yadda ya soyu ba
zai yiwu a tarbi baƙi da shi ba. Makaɗa Sa’idu Faru ya nuna cewa duk girmansa ba ya da wani
amfani, kuma ba ya kashin kunya, wato shi sarkin da yake yi wa habaicin. Haka
kuma, ya kwatantashi da tandun ba’u. Wannan
wani tandu ne da ba a iya saka mashi mai domin tsiyaya yake yi saboda haka man
zai zube ne ga banza. Kenan dai wannan ɗan sarkin da aka jefa da wannan kalmar ta habaici ta nuna ba
shi da amfanin komai. Haka kuma ya kwatanta shi da marar gaɓoɓi, kuma mai hangaham baki kuma bakin taɓaɓɓe.
A nan Ɗan Umma yana nuna cewa ɗan sarkin ba shi da wani kuzari ko karsashin da zai iya zama
sarki, kuma halittar bakinsa kaɗai
ba za ta ba shi damar zama sarki ba.
Makaɗa Sa’idu
Faru ya ƙara yin wani habaicin inda yake cewa:
Jagora: Ga shi kamar malami,
: Ga sanda tare da mala,
: Kabag gani nai rike da casbaha,
: Bai iya ba sin ba”
A cikin waƙar Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda Abubakar Garba ne aka ciro ɗan waƙar da yake a sama. Waɗannan ɗiyan
waƙar da makaɗa Sa’idu Faru ya yi, habaici ne ya jefi wani sarki da su ya
siffanta shi da siffar malamai ta riƙe sanda da casbaha da mala. Mala na
nufin Gafakka/jaka ta fatar dabbobi da ake saka Alqurani ko wasu littafai na
addini a cikinta. Dukkan waɗannan
siffofi suna nuna cewa ya yi shigar malamai, amma kuma ba malami ba ne kenan ya
jefe shi da kalmar jahilci a fakaice.
A Bashaushiyar al’ada idan aka ce wannan jahili ne, to ba
shi da wata ƙima ko daraja a idon Hausawa.
To balle a ce ko farkon fara karatun addinin musulunchi bai
iya ba, kenan jahilcin nasa ya kai maƙura.
Haka makaɗa Sa’idu yaƙara yin habaicin ya ce
Jagora: Kakan wani ba shi da yaƙi ko can
: Ɗan daudu na shi,
: Kaka nai ka suna,
: Da madubi nai da hoda,
: Da hwarar riga da kore,
: Da gani nai ka
ga kure,
: Geme cim jim da shuni.
‘Yan Amshi: Babban bajimin gidan Sambo,
: Shirin ka daban da raggo,
: Jikan Mamuda Sarkin Nasara baban Baraya.
A cikin waƙarsa ta margayi maigirma Sarkin Zamfaran Zurmi Suleiman Muhammadu Sambo. A
wannan ɗan waƙar habaici ne makaɗa Sa’idu Faru ya
yi wa wani ɗan sarki cewa kakansa bai iya yaƙi ba, har ya
kwatanta shi da daudanci, da shafa kwalli, har da madubi da hoda. Kenan ya soki kakansa da ragwanci,
har ta kai ga daudanci da rashin iya yaƙi.
Ga al’adar Hausawa, abin takaici ne
a samu namiji da kwaikwayar ɗabi’un mata. Ya kuma ƙara jifar kakan da cewa kure ne. Kure dai, shi ne namijin kura wato ya
danganta shi da ɗabi’ar kure ta rashin amana da rashin sabo. Sannan kuma ya ƙara da cewa ya shafe gemu da shuni. Shuni dai wata kala
ce da ake amfani da ita don yin kwalliya, wato dai shi kakan ba shi da aiki sai
ɗabi’ar mata da kwaikwayar halayensu. Duk da ga shi an ce yana da kamalar
maza ta gemu.
Kammalawa
Habaici dai ɗan’uwan zambo ne,
sai dai shi habaici bai yi tsananin zambo ba. Habaici wasu kalmomi ne da ake
ratayawa mutum, ba tare da kama sunansa ba kai tsaye. Waɗanda suka fi yin
habaici a cikin al’ummar Hausawa su ne mata, sai kuma makaɗan fada, kamar
makaɗa Sa’idu Faruda makamantansa. Muradin wannan mukala shi ne zaƙulu wasu habaice-habaice da makaƙa Sa’idu Faru ya yi a wasu waƙoƙinsa da kuma nuna nauyinsu a al’adar Hausawa, da ma
bayyana ma’anar wasu daga ciki.
Manazarta
Ɗangambo, A. (1982) Adabin Hausa da rabe-rabensa. Zariya: NNPC
Zarruk, R.M da Kafin Hausa A. da
Bello S.Y (1986). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare. Ibadan: University Press plc.
Gusau, S.M (2015) Mazhabobin Ra’i da
tarke a adabin da al’adu na Hausawa: Century
Research and Publishing Limited.
Gusau S.M (1996) makada da mawakan Hausa Usman A/amin Publishing
Company Kano, Nigeria.
Gusau S.M (2014) Diwanin waƙoƙin baka juzu’i na biyu. Kano: Century Research and Publishing Limited.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.