Ticker

6/recent/ticker-posts

Sunayen Wasu Na'urori Da Injunan Turawa Da Hausawa Suka Fassara Zuwa Hausa

Waɗannan wasu na'urori da injuna ne waɗanda Hausawa suka yi musu suna da Hausa. Ku turo mana ƙarin wasu da kuka sani domin mu ƙara a kan waɗannan. Za ku iya turowa ta ɓangaren comment da ke ƙasa.
  1. Ford = Hodi 
  2. Bedford = Bilhodi 
  3. Mercedes = Marsandi 
  4. Peugeot = Fijo
  5. Volkswagen = Besuwaja
  6. Volkswagen Beetle = Ladi ba ɗuwawu
  7. Fiat = Fet 
  8. Austin = Ostan-Ostan 
  9. Bus = Kiya-kiya (borrowed from Yoruba)
  10. Station wagon = Dafa-duka
  11. 1973 Mercedes-Benz W114/W115 = Bagobira
  12. 1982 Toyota Corolla = Bana ba harka
  13. Hatchback/coupe = ‘Yar kumbula
  14. Long bus = Safa 
  15. Ten-wheel = Tangul 
  16. Mercedes 911 truck = Roka 
  17. Mercedes 1413-1414 truck = Bargazal
  18. Mercedes 1312 (and similar sizes) truck = 'Yar Fakas
  19. Max Diesel = 'Yar Rasha (Kirar Kurma) 
  20. Man Diesel (12-Wheeler) = Kwamanda
  21. Truck with wooden body = Shorido
  22. Hiace = Motar gawa
  23. Towing van = Janwe
  24. Tractor = Tantan
  25. Trailer = Titiri 
  26. Pick-up van = A kori kura 
  27. Bulldozer = Katafila 
  28. Conductor = Kwandasta
  29. Scrutiniser = Sakwaneza
  30. Brake = Birki
  31. Gear Box = Giyabos
  32. Bumper = Bamba
  33. Radiator = Lagireto
  34. Carburator = Kafireto
  35. Distributor = Disfuto
  36. Coil = Kwayil
  37. Valve = Bawul
  38. Bearings = Boris
  39. Rings = Ringi 
  40. Plug = Fulogi
  41. Crank Shaft = Karanshaf
  42. Grand Overhaul = Garanbawul 
  43. Screw driver = Sikun direba
Ranar Hausa ta Duniya

Post a Comment

0 Comments