Assalamu alaikum, warahmatullahi wabarakatuhu
Muna yiwa yan uwa da iyayenmu
dake cikin wannan zaure na TAMBAYA DA AMSA fatan kuna lafiya
Ya aka ji da ibtila'in jarabawar
rayuwa - to Allaah ya bamu ikon Nasara akan kowacce jarabawa da Allaah ya tsara
mana
Bayan haka !
Saqonnin ku dayawa sun riske ni,
inda wasu suke tambaya a game da group na musamman wanda zasu gyara ibada don
bautawa Allaah kamar yanda Annabi Rahama Sallallahu alaihi wasallam ya koyar
damu wasu kuma sun bada shawarar a bude wani group din da za'a saka littafin
koyarda Sallah kamar yanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya koyarda
sahabbansa
Ina son duk wanda yake karanta
wannan saqon, yayiwa kan sa tambaya
"SHIN SALLAR DA NAKE YI A
KULLUM SAU 5 IRIN TA CE ANNABI YA KOYAR A ADDINANCE KO KUMA INA YI NE KAMAR
YANDA NA TASO NAGA ANA YI A AL'ADANCE❓
Ka maimaita tambayar kanka kamar
sau 3. Anan take zaka ji hankalin ka ya dawo jikin ka sannan zaka fara
kwokwanto akan anya sallar tawa ma an amshe ta kuwa ?
Tunda ga dai Hadisin Abu Hurairah
nan a cikin Sahihul Bukhari da Muslim wanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam
yace: Sallu kama ra'ayta Muni usalli" Bi ma'ana: "Kuyi sallah kamar
yanda kuka gani Ina yi" Kadai sake tambayar kanka: Anya irin sallar Manzon
Rahama nake yi❓
To kada ka samu damuwa domin kuwa
ga wata dama ta samu cikin sauqi da zaka gyara ibadarka idan har kana da niyyar
gyarawa din
Da akwai littafin: SIFATU SALATIN
NABY - MINAT TAKBIRI ILAT TASLIM - KA'ANNAKA TARAHA" Ma'ana: "SIFFAR
YANDA ANNABI YA KE SALLAH - TUN DAGA TAKBIR (ALLAHU AKBAR) HAR ZUWA TASLIM
(ASSALAMU ALAIKUM) - KAMAR KANA GANIN ANNABI DIN YANA SALLAH A GABANKA"
Wanda ya wallafa littafin shine:
Allamatish Shaikh Muhaddith Mujaddid Muhammad Nasiriddin Ibn Nuhu Al-Albaany
(Rahimahullah - ya rasu a 1999 a kasar Jordan) wanda malaman duniya suke
kiransa da likitan ilimin Hadisi. Malamai irinsu: Shaikh Abdulaziz Bin Baaz
(shugaban committee na Fatawa Lajnah ad-Da'imah dake a kasar Saudiyya kafin ya
rasu a shekarar 1999), Shaikh Saleh al-Uthaymeen da Shaikh Ali Shaikh da Shaikh
Saleh Al-Fawzaan duk sun sallamawa Shaikh Al-Albaany indai magana ake ta ilimin
Hadisai
Na karanta littafin Kuma na
fahimce sa ba sau 1 ko 2 ba amman duk da haka ji nake da akwai gyararraki a
cikin sallata to ina kuma ga wanda bai karanta littafin ba ko Kuma wani
littafin makamancinsa na koyon sallah
Dalilin da yasa na aminta da fara
karatun littafin a cikin sabon group din da zamu bude shine
1️⃣Domin na qara gyara Sallah ta yanda zanyi koyi da irin Sallar Annabi
Sallallahu alaihi wasallam kamar yanda yayi umarni
2️⃣Domin dubunnan musulmi da suke a group dinnan su dinga koyi da Sallah irin
ta Ma'aiki Sallallahu alaihi wasallam - Wanda a yanzu haka Zan iya zayyano
kura-kurai sama da guda 100 da masu Sallah suke yi
3️⃣ Domin mu samu ladan koyi da Sunnar Annabin Rahama Sallallahu alaihi
wasallam
Idan har muna son mu zamo muminai
da Allaah Azzawajallah ya saukar da Surah musamman mai sunan Suratu Muminuun to
fa sai mun saka Tawadu'u wato Khushu'i (Tsoron Allaah) a cikin sallar mu, kamar
yanda Allaah Subhanahu wata'ala yace
( قَدْ أَفْلَحَ
الْمُؤْمِنُونَ )
المؤمنون (1) Al-Muminoon
Lalle ne, Mũminai sun sãmi babban
rabõ.
( الَّذِينَ
هُمْ فِي صَلَاتِهِمْ خَاشِعُونَ )
المؤمنون (2) Al-Muminoon
Waɗanda suke a cikin sallarsu mãsu tawãli'u
ne.
To ta yaya zamu samu Khushu'i a
cikin sallar mu indai har bamuyi koyi da fiyayyen halitta ba❓
Mu sani cewar Sallah itace Ibadar
da za'a fara tambayar mu a ranar Alqiyama, kamar yanda Annabi Sallallahu alaihi
wasallam ya faɗa: idan tayi komai zaiyi kyau ammanfa idan ka tozar ta to sauran ayyukan
naka ma ba'a magana. Domin kuwa ka ga ita musamman Annabi Sallallahu alaihi
wasallam ya je ya karbo ta a can saman 7, ba kamar Azumi, Hajji da Zakkah da
Mala'ika Jibril Alaihis salam aka aiko ba
Dan Haka duk Wanda yake da ra'ayi
da Kuma niyya: Namiji ko Mace, Tsoho ko Tsohuwa, Miji ko Mata, Babba ko Yaro
sai ya yi min magana ta private yaji tsare tsaren da ake bi daganan sai a
sakashi a group din: "USMANNOOR ACADEMY"
Zamu fara karatun littafin:
SIFATU SALATIN NABY din duk ranar Asabar da Lahadi da daddare, (daga
Asabar/Lahadi ta sama) in Sha Allaah
A tura saqon sanarwan zuwa ga
sauran yan uwa da abokan arziki da basa wannan zauren. Wanda yake buqata
yayimin magana ta private idan so samu ne a kirani ta WhatsApp call ta Yanda
Zan saurin ganewa saboda yawan saqonnin da ake turowa
Ya Allaah ka bamu ikon bauta maka
yanda ka umarci a bauta maka ba yanda muka taso muka ga ana bauta maka ba
Ya Allaah kamar yanda muka hadu a
wannan zaure na TAMBAYA DA AMSA, Allaah ka sada fuskokinmu a ALJANNATIL FIRDOUS
( اتْلُ
مَا أُوحِيَ إِلَيْكَ مِنَ الْكِتَابِ وَأَقِمِ الصَّلَاةَ ۖ إِنَّ الصَّلَاةَ تَنْهَىٰ
عَنِ الْفَحْشَاءِ وَالْمُنكَرِ ۗ وَلَذِكْرُ اللَّهِ أَكْبَرُ ۗ وَاللَّهُ يَعْلَمُ
مَا تَصْنَعُونَ )
العنكبوت (45) Al-Ankaboot
Ka karanta abin da ake yin wahayi
zuwa gare ka daga Littãfi, kuma ka tsayar da salla. Lalle salla tanã hanãwa
daga alfãsha da abni ƙyãma, kuma lalle ambaton Allah ya fi girma, kuma Allah Yanã sane da abin da kuke aikatãwa.
Subhanakallahumma wabi hamdika
ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk
SANARWA
Usman Danliti Mato
(Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.