Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Hucewa Ta Gaban Mai Sallah

Assalamu alaikum waramatullah

Malan dan Allaah tambaya na ke  son na yi gameda wucewa ta gaban mai sallah yaya abin yake nake

AMSA

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIIM ALHAMDULILLAH

Hucewa ta gaban mai sallah ta inda shari'a ta hana haramun ne babu shakka, kuma haqiqa akwai hadaisai da yawa sunyi nune akan haka, da kuma ijma'in malamai

Ma'ana Hucewa ta gaban mai sallah  tsakanin sa da sitra ko wanda ba sitra a gaban sa idan shi kadai ya ke salla ko shine liman to bai halatta  a huce ta gabansa ba, amma idan mamu ne to babu komai idan anhuce ta gaban su domin sitrar liman itace sitrar su. [adisi ya zo akan haka bukhari ya rawaitu a hadisi mai no {471} kuma muslim {504}]

(1) DALILIN HAKA DAGA SUNNAH

An karbo daga juhaim dan haris (r.d) annabi (s.a.w) ya ce: da wanda ya ke hucewa ta gaban mai salla ya san abun da ya ke kansa (na zunubi) da ya kasance yatsaya arba,in da ya fi alkhairi gare shi daga ya huce ta gaban mai sallah , abun nadir ya ce: ban sani ba shin ya ce kwana arba'in ne, ko wata arba'in ne, ko shekara arba'in ne.

[bukhari (510) da Muslim (507) sukarawaitu shi]

fadin sa: ((A BIN DA YA KE KAN SA )) ma'anar sa: da yasan abin da ya ke kansa na zunubi, da tabbas ya zabi ya tsaya arba'in, akan abin da ya afka na wanchan zunubi, (na hucewa ta gaban mai sallah) sai hakan yai nune akan qarfin hanin da akayi, da kuma narko (azaba) mai tsanani cikin hakan. (wato hucewa ta gaban mai sallah) [sharhun nawawii alaa Muslim (4/225)].

An karbo daga baban sa'iidil-khudriy (r.d) ya ce: annabi (s.a.w)ya ce: idan dayan ku yana salla izuwa wani abu da zai suturta tsakanin sa da mutane sai wani yai nufin ya huce ta gaban sa, to ya hana shi, idan yaqi to ya yakeshi domin kadai dai shi shaidan ne. [bukhara (509) da muslim (505) suka rawaitu shi ]

Alqadi iyad ya ce cikin sharhin fandin sa (s.a.w) (KADAI DAI SHI SHAIDAN NE): ....... Dalilin cemasa haka kai tsaye shi ne haqiqa shi ya aikata irin aikin shaidan.

Kuma aka ce: ma'anar sa kadai shaidan ne ya sa shi ya huce ta gaban sa kum shine ya hana shi ya  koma. (lokacin da aka hana shi) zancan sa ya kare

Bai halatta ba ga mai sallah ya yaqi wanda zai huce ta gaban sa da makami ba.

Dalili akan haka kuwa shi ne ijmaa'in malamai akan fidar haka: ibn abdul-barri ya ce malamai sunyi ijmaa'i akan haka da alqadi iyadh, da alqurdubiy.

Ibn abdul-barri ya ce: (malamai sunyi ijmaa'i ce wa haqiqa shi bazai yaqe shi da takofi ba kuma ba zai mai magana ba, kuma bazai kai makora ba wajan tare shi ba irin makorar da zai bata sallar sa ba, sai ya kasance hakan da ya aikata yafi cutar da shi sama da hucewar sa ta gaban sa.... I zuwa qarshan maganar sa (attamhiid 4/189).

A wannan hadisin na baban sa'iidil-khudri zamu fahimci abubuwa kamar haka

1- bai halatta ba hucewa ta gaban mai salla, kuma wajibine ga wanda zai huce tagaban mai salla idan ya hana shi ya dakata ko ya chanza hanya,

2- kuma ya halatta mutum ya tare wanda zai huce ta gabansa (wato tsakanin sa da sutra) a yayin da yake salla, idan kuma yaki hanuwa ya yake shi,

3- mutum ya sanya wani abu mai dan tsaye agaban sa yayin da zai yi sallah  da zai shi ga tsakanin sa da mutane. ( kamar sanda ko kujera ko wani  abu mai tsayi wanda tsayin sa ya kai tsawan siddin abin hawa (kamr rakumi da sauran su) )

DALILI DAGA IJMA'IN MALAMAI AKAN HANA HUCEWA TA GABAN MAI SALLA

Ibn hazam ya ce: malamai sun hadu akan kyamatar  (wato hani akan haka) hucewa ta gaban mai sallah tsakanin sa da sitrar sa, kuma haqiqa mai yin hakan mai zunufi ne. [maraatibul-ijmaa'i shafi na 30]

Kuma a yayin da jaki, ko mace (baliga), ko bakin kare su ka huce ta gaban mai sallah to sallar sa ta lalace, Hadisi ya tabbata akan haka hadisi ruwayar muslim (510) daga abdullah dan samit shi kama ya ji daga abii zharrin (r.d)

Amma kuma idan ba ya daga cikin abubuwan nan uku da annabi (s.a.w) ya lissafa kuma ya ce idan suka huce ta gaban mai sallah sallar ta baci, to su sauran da ba suba, ba sa fata sallah sai dai suna  rage ladanta (wato sallar).

Babu laifi idan mutum ya huce ta nesa da mai yin sallah kamar tazarar zira'i uku, idan babu sitra agaban sa.

WALLAHU A'ALAM.

Amsawa (abu abdullah)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments