Halayen Karuwa Daga Bakin Alhaji Akilu Aliyu: Nazari Cikin Wakar ‘Yar Gagara

    Cite this article as: Haruna Umar Maikwari da Ibrahim Alhaji Gado (2023) Halayen Karuwa Daga Alƙalamin Alhaji Aƙilu Aliyu: Nazari Cikin Waƙar ‘Yar Gagara. Takardar da aka buga a Mujallar Sashen Harsunan Nijeriya na jami’ar tarayya ta Dutin-Ma jihar Katsina.

    Halayen Karuwa Daga Bakin Alhaji Aƙilu Aliyu: Nazari Cikin Waƙar ‘Yar Gagara

     Haruna Umar Maikwari

    Department of Hausa Language.
    Federal College of Education (Technical) Gusau
    maikwariharuna@gmail.Com
    (+234) 07031280554

    Da

    Ibrahim Alhaji Gado

    Government Secondary School Sayinna
    ibrahinmalhajigado@yahoo.com
    (+234) 07039602059

    Tsakure

    Wannan maƙala ta mayar da hankali ne wajen nazarin halayen karuwa a cikin waƙar ‘Yar Gagara ta Alhaji Aƙilu Aliyu wadda aka buga a cikin littafin Fasaha Aƙiliyya. Manufar wannan maƙala ita ce, ta fito da halayyar karuwa a ma’aunin tunanin al’umma, tare da bayyana matsayin wannan halayya a addinance da kuma al’adance, bugu da ƙari za ta bayyana irin ci bayan da halayen karuwa suka kawo wa al’umma. Hanyar da aka bi wajen aiwatar da wannan maƙalar ita ce, ta karance-karancen bugaggun littattafai da kundayen bincike da littafin matani na Fasaha Aƙiliyya. An kuma zaɓi a ɗora wannan binciken (Maƙala) a kan Mazhabar Tsarin Al’adu ko Mazhabar Yanayin Al’adu (Cultural Schema Theory). Wannan mazhaba an samu wani masani Jean Piaget (1920s), ya rubuta maƙala inda ya fito da halayen yara ƙanana da al’adunsu, wannan ya sa na ɗauki mazhabar domin in fito da halayen karuwai kamar yadda Alhaji Aƙilu Aliyu ya zo da su a waƙarsa ta Yar Gagara. Sakamakon binciken da wannan maƙalar ta fitar shi ne, halayen karuwa galibi ba na gari ba ne. Domin daga abin da maƙalar ta gano na halayen akwai ƙarya, zamba, makirci, cin amana, yawon banza, cuta, da dai makamantan su. Ko shakka babu waɗannan halaye sun tattara ga karuwai. Maƙalar dai ta gano cewa waɗannan halaye barazana ne ga al’umma kowace iri. Don haka mata da suke da halaye na gari, su suke kawo wa al’umma ci gaba, matan banza (karuwai) kuwa, halayensu barazana ne ga al’umma.

    1.0 Gabatarwa

     Halayyar al’umma ita ce al’adarsu. Wasu mutane suna da keɓantacciyar al’ada wadda aka san su da ita. Idan aka dubi masu sana’a iri ɗaya kamar manoma, mafarauta, majema, masaƙa, marina, masunta, maƙera, mahauta, wanzamai, dukawa, da dai sauransu. Haka mutanen da suke a gari ɗaya za ka iske akwai wata al’ada da ta keɓanta gare su. irin wannan yanayi na al’ada shi ne ya haddasa wa karuwai yin tarayya a cikin halayensu. Alhaji Aƙilu Aliyu fitaccen marubicin waƙoƙin Hausa ne, kuma shi ya san mafi yawan halayyar karuwai, wanda wannan ya sa ya yi wata waƙa wadda ya ba suna “‘Yar Gagara”. Waƙar ƙar ‘Yar Gagara waƙa ce da mafi yawan manazarta harshen Hausa sun san wannan waƙa. Al’adun Hausawa ba su yadda da duk wata al’ada da karuwa ke da ita ba wadda ta kasance saɓanin wadda ɗaukacin al’ummar Hausa ke da ita ba. Wannan maƙalar za ta duba wasu al’adu da Alhaji Aƙilu Aliyu ya zo da su a cikin waƙarsa ta ‘Yar Gagara wadda aka buga a cikin wani littafi mai suna Fasaha Aƙiliyya.  

    1.1              Manufar Bincike

    Babbar manufar wannan binciken ita ce fito da wasu halayen karuwa da Alhaji Aƙilu Aliyu ya faɗa a waƙarsa ta Yar Gagara. Akwai kuma wasu manufofi da suka haɗa da:

    i.                    Bayyana matsayin wannan halayya a addinance da kuma al’adance.

    ii.                  Fito da irin ci bayan da halayen karuwa suka kawo wa al’umma.

    iii.                Fayyace barazanar da halayen suke yi ga al’umma Hausawa.

    1.2 Matsalolin Bincike

     An gudanar da nazarce-nazarce a kan mata musamman waɗanda suka zo da ci gaba ga al’umma. Sai dai dukkan binciken da aka gudanar ba su kawo wani ci gaba da mata karuwai suka kawo ba. Ko shakka babu idan aka dubi irin fasadi da naƙasu da karuwai suka haifar ba za a ga wani ci gaba da aka samu ba ta fanninsu. Halayen karuwai ba su kasance halaye da al’ada ta yadda da su ba. Don haka wannan maƙalar ta bijiro da halayen karuwai, da irin ci bayan da suka haddasa wa al’umma.

    1.3 Hanyoyin Gudanar da Bincike

     Wannan maƙalar ta kammala ne ta hanyar karance-karancen bugaggun littattafai da muƙalu da masana da manazarta suka gudanar. Lura da cewa, halayen da Alhaji Aƙilu Aliyu ya kawo a cikin waƙarsa ta ‘Yar Gagara duk na karuwa ne babu ko tantama ya sa maƙalar ta bi hanyar karance-karancen wasu littattafai don gano halayyar karuwa da kuma irin ci bayan da karuwai suka haddasa a rayuwar al’umma. Bin wannan hanyar shi ya ba da damar:

    i.                    Gano wasu halaye da suka tattara ga karuwai

    ii.                  Samun bayanai game da yadda za a gane karuwai don a ƙaurace masu

    iii.               Bambance al’ada da halayyar da ta keɓanta ga wani daban ko wasu masu sana’a iri ɗaya.

    1.4. Ra’in Bincike

     An zaɓi a ɗora wannan maƙalar a kan Mazhabar Tsarin Al’adu ko Yanayin Al’adu (Cultural Schema Theory), wadda Emmanuel Kant ya assasa. Wannan Mazhaba an samu wasu kamar Jean Piaget (1920) da Frederick Barttett (1930) da Lipset, (1993 da Nashida (1999) da Malcon (2002) suka gudanar da bincike a kanta. Kamar dai shi Jean Piaget (1920) ya yi bincike a kan al’adar Jarirai, shi kuma Lipset, (1993) ya yi nazari a kan matsayin al’umma, da dai makamantansu. Wannan maƙalar za ta mayar da hankali ne wajen nazartar halayyar karuwa a cikin al’umma.

    2.0 Ma'anar waƙa:

    Ra'ayoyi mabambanta na masana adabi sun ta cin karo wajen tsayar da ma'ana guda ɗaya ta waƙa. Sai dai abin sha'awa, duk ma'anonin za a same su suna magana ne da siga iri ɗaya. Kaɗan daga cikin su sun haɗa da: MB Umar (1980) yana ganin "waƙar baka a Hausa kamar sauran harsuna tana zuwa ne a rere, cikin sautin murya ko rauji. Rerawar da ake yi wa waƙa ya sa ba ta zuwa a shimfiɗe gaba ɗayanta sai dai ta zo gunduwa-gunduwa tare da amshi a tsakaninsu".

    Ɗangambo (1982) a wajen wani taro mai suna 'ɗaurayar gadon feɗe waƙa' a cikin takarda ya bayyana ma'anar da cewa:-

    "Waƙa wani saƙo ne da ake gina shi kan tsararriyar ƙa'ida ta baiti, ɗango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (ƙafiya), da sauran ƙa'idojin da suka shafi daidaita kalmomi, zaɓensu da amfani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke ba".

    Shi kuwa Yahya (2007) cewa ya yi "waƙa tsararriyar magana ce da ta ƙunshi saƙo cikin zaɓaɓɓun kalmomi da aka auna domin maganar ta reru ba faɗuwa kurum ba".

    ƙamusun Hausa a tashi ma'anar waƙa na nufin "wata tsararriyar magana da ake yi kan kari ko rauji" (CHNH, 2006:466).

    Bayanin da aka yi a sama ya nuna cewa "waƙa wata manufa ce da akan bayyana a rere ta hanyar amfani da amsa-amo, ko kuma rerawar ta zama ta sautin murya mai zaƙi wata sa'a da haɗawa da kiɗa da sauran salon jin daɗi ga mai sauraro don jawo hankalinsa ga manufa kuma takan sha bamban da maganar baka ta yau da kullum da zube da kuma wasan kwaikwayo. (Auta 2001).

    Waƙa kamar yadda manazarta adabin Hausa suka ba da ma'anarta, salon isar da saƙo ne da ake rerawa wato rerawa cikin hawa da saukar murya mai tafiya tare da kiɗi ko kuma akasin haka kamar zance na yau da kullum ko kuma zantuttukan da ke yi lokacin hira.

    Waƙa ta bambanta daga taɗi ko magana ta yau da kullum. Aba ce wadda ake shirya maganganu daki-daki cikin azanci da nuna ƙwarewar harshe. Harshen waƙa a bisa kansa cikakke ne duk da cewar ya kauce wa wasu ƙa'idojin nahawu. (Gusau 2005).

    A irin gudunmuwa ta wannan aiki dangane da abin da ya shafi ma'anar waƙa da cewa, Waƙa tana nufin ƙololuwar hikima da fiƙira da basira da hazaƙa da fasaha ta sarrafa kalmomi bisa ga tsari madaidaici tare da amfani da baiti ko ɗiya a cikin rauji mai daɗin gaske domin nishaɗantarwa tare da jan hankalin mai sauraro ga abin da ake isarwa na saƙo a gare shi.

    3.0 Taƙaitaccen Tarihin Marubucin Waƙar ‘Yar Gagara

     Aƙilu Aliyu sananne ne, asalinsa mutumin ƙasar Kabi ne a ƙaramar hukumar Jega ta jihar Kebbi. An haife shi a Unguwar Ƙaurar Lailai a Jega ta jihar Kebbi a cikin watan Muharram, a shekarar 1918. Ya fara karatun Alƙura’ani a wajen Mahaifinsa wanda aka fi sani da malam Aliyu Madaha saboda shi ma’abucin Ishiriniya ne. Bayan rasuwarsa a lokacin Aƙilu yana ɗan shekara kamar sha biyu, sai ya ci gaba da ɗaukar karatu a wajen su Alhaji Mukhtar Tsoho da Malam Muhammad ɗan Takusa da Malam Ban-Allah da kuma Malam Abdulmumini, inda ya fara karatun ilimi yana da kamar shekara sha biyar, ya fara zuwa Kano. Yana zuwa neman ilimi da sana’a yana komawa, har dai ya ƙware da zama sosai a Kano ɗin, Babban malaminsa na ilimi shi ne Malam Mahmuda da malam Salga shaihinsu na ɗariƙar Tujjaniyya kuwa shi ne malam Salga. A zaman Aƙilu a Borno inda ya yi shekara ashirin da uku, ya yi siyasa da ƙarfinsa da hazaƙarsa. Haka kuma ya ci gaba da neman ilimi da yaɗa shi har ya rasu.

     Ta fannin waƙa kuwa Aƙilu tun yana yaro ya fara tsara ta, kusan ko yaushe a cikin halin ƙulla ta yake shi kansa bai san iyakar waƙoƙin da ya shirya ba, saboda yawa sun ɓace amma ba su kasa dubu.

     Bayanin da aka samu a cikin littafinsa na Fasaha Aƙiliyya ya nuna muna cewa, Alhaji Aƙilu Aliyu ya shahara wajen shirya waƙa, haka kuma an daɗe da sanin waƙoƙinsa, daga na addini da na gargaɗi har zuwa na siyasa don kuwa an buga wasu a littafi, waɗansu kuma a jaridu. Sau da yawa a kan ji shi a gidajen rediyo wasu waƙoƙin kuma akan ji su a fayafan garmaho. A lokacin da yana raye yakan shira waƙa musamman idan an gayyace shi a wani babban taro. Aƙilu ba ɓoyayye ba ne a wajen ma’abuta karatun waƙoƙi na zamani wato rubutattu”.

     Ita kuma wannan waƙar ta ‘Yar Gagara tana daga cikin waƙoƙinsa na sha’awa, kuma ya yi ta ne saboda lura da irin munanan halayen da ke tattare da karuwa (‘Yar Gagara). Aliyu A (2007:i-ii)

    4.0 Karuwanci

    A cewar Balbasatu I. Y. (2000:11) ta bayyana karuwanci da cewa “Wata al’ada ce da wasu mata ke amfani da ita don sayar da kansu ga mazajen da ba su da hulɗar aure tsakaninsu”.

    A gudummuwa irin wannan, za a iya cewa, karuwanci wata ƙazantacciyar sana’a ce ta sayar da mutunci wadda ta ƙunshi hulɗa da saduwa tsakanin wata da wani ba tare da aure ba. Wasu mata suka tsinci kansu a cikin wannan sana’ar a sakamakon auren dole, ko tallace-tallace, ko jaraba, ko talauci, ko cuɗanya tsakanin mata da maza, ko sha’awar ɗabi’un wasu al’ummu da dai makamantansu.

    3.1 Dalilin Karuwanci

     Galibi mafi yawan abin da ke sa mace ta shiga karuwanci kashi 90% cikin 100% auren dole ne. Kuma ko ba shi ba ne idan ka tambayi karuwa dalilin da ya sa take wannan sana’a ta karuwanci za ta gaya make cewa wannan ne. Alhaji Aƙilu Aliyu a cikin waƙarsa ta ‘Yar Gagara ya bayyana cewa wannan shi ne dalili kamar yadda su karuwan suke faɗa.

    4.1.1 Auren Dole

     Auren dole wani nau’in aure ne da ake yi ba tare da amintar wani sashe (miji ko mata) daga cikin waɗanda ake son a haɗa ba. Idan aka yi wannan aure za a taras zaman ba zai yi daɗi ba. Sau da yawa akan yi wannan aure ba a dace ba[1]. Aƙilu ya yi amfani da salon hira inda ya zo da hoton karuwa tana zantawa da wani a baiti na 14-17. Ga dai abin da yake cewa.

    14. “Tare da wane akai mana ƙunshi,

     Mai daraja haka”-domin ƙarya.

    15. Ƙinsa nake yi, na ƙi na zauna,

     Abba ya ce mini ba wani sai shi.

    16. Na zama babu dare ba rana,

     Kullum in riƙa faman kuka.

    17. Fatana shi ne a raba mu,

     Ko da zan rasa mai aurena.

      (Aƙilu Aliyu: Waƙar ‘Yar Gagara)

     Idan aka lura da abin da ke cikin waɗannan baituka za a fahimci cewa, karuwa tana bayar da labarin an yi mata auren dole. Kuma da shi ta kafa hujja cewa, shi ne ya saka ta a harkar karuwanci.

    5.0 Halayen Karuwai

     Halaye dai su ne ko yaushe ke bayyana ga mutum har a iya cewa ga daga inda ya fito ko ga salsalarsa. Halaye suna bayyana irin girman da ke ga mutum ko ƙimarsa. Kuma halaye su ke yi wa mutum kwalliya in sun kasance masu kyau, in kuma akasin masu kyau ne su ke jagoranci wajen zubar da girma da wulaƙancin da mai su kan fuskanta. Al’ada ba ta yadda da wasu halaye ba, musamman masu muni kwatankwacin na karuwai kamar dai ƙarya, zamba, sata, biyar bokaye, cin amana, yawon banza, zaman banza, magangannun batsa, da dai makamantansu. Alhaji Aƙilu Aliyu ya zo da wasu halaye waɗanda suka rataya ga karuwa waɗanda suka haɗa da:

    5.1 Ƙarya

     Wannan hali yana daga cikin ƙananan jigogin da suka gina babban jigon waƙar ‘Yar Gagara wato “Gyaran Hali” (wato a lurar da al’umma da su guji neman karuwai). Don haka sai aka bayyana cewa su karuwai maƙaryata ne, za su iya yin ƙarya domin su samu abin da suke nema ga wanda suke da buƙata da abinsa. Wannan jigon ya fito a baituka kamar 2, 10, 14, 30, 31 da kuma 48. Misali.

    2. Mai fitina, mai ƙaryar banza,

     Ba ta nufin zikiri sai batsa.

    10. Mai ƙaryar daraja da muƙami,

     San da ta sauka a baƙon birni.

    14. “Tare da wane akai mana ƙunshi,

     Mai daraja haka”-domin ƙarya.

    30. Kin ban haushi, tsawa zan maki,

     Domin kin mini zancen ƙarya.

    31. Ke tafi can, kinibabbar banza,

     Mai kirkin baka, ƙaryar gaɗa!

    48. Karuwa ba ta da niyyar aure,

     Sai dai zamba da ɗimbin ƙarya.

      (Aƙilu Aliyu: Waƙar ‘Yar Gagara)

     Idan aka lura da waɗannan baituka za a fahimci cewa a kowane baiti akwai kalmar ƙarya da aka danganta da Karuwa (‘Yar Gagara). Wannan yana nuna kena karuwai maƙaryata ne, kuma duk abin da suka faɗa ba abin da ya dace a yarda da shi ne ba. Don haka da mutum ya ci karo da karuwa to mafi alhairi gare shi, shi ne ya ƙaurace mata.

    5.2 Makirci.

     Makirci wani abin ƙi ne wanda ya keɓanta ga halayen wasu. Shirya wani abin da ba na daidai ba, tare da raka shi da wasu ɗabi’u domin gamsar da wanda aka shirya wa shi. Ana kiran mai aikata shi da suna makiri, idan mace ce kuma makira. Aƙilu Aliyu ya yi amfni da wannan kalma ta makirci domin ya bayyana halayen karuwai, don masu nemansu su san halin da za su tsinci kansu. Ga abin da yake faɗa a baiti na 34.

    34. Don iya makircin ‘Yar Gagara,

     Wai ita ba ta da haushin kowa.

      (Aƙilu Aliyu: Waƙar ‘Yar Gagara)

    Wannan ya nuna cewa, karuwa za ta iya shirya maka makirci wanda za ka gamsu ka yadda cewa ita mai kirki ce, mai sauƙin hali, maras ganin ƙyashi. Domin ƙwarewar karuwa ga makirci idan ta shirya maka shi to yana da wuya ka tsallake.

    5.3 Rashin Kunya.

     Rashin kunya wani yanayi ne na yaruwa wanda mutum kan tsinci kansa a ciki. Wannan na iya faruwa a sakamakon rashin tarbiyya ko rashin ilimi ko rashin riƙa addini da muhimmanci. Duk wannan yanayi galibi yana tattare ga karuwai. Aƙilu ya yi amfani da wannan jigon don ya fito da babban jigonsa na Faɗakarwa/Gyaran Hali. Ga yadda abin yake a cikin waƙarsa ta ‘Yar Gagara.

    11. Sai ka ji ta raɗa sabon suna,

     Ba kunya ba take ‘yar kashi.

    35. Ba ta kunya, ba ta namada,

     Yaushe ta ka tuna zancen tuba?

      (Aƙilu Aliyu: Waƙar ‘Yar Gagara)

    5.4 Cuta

     Cuta kalma ce mai harshen damo. Tana iya kasancewa wani yanayi na rashin lafiya da ka iya kama jiki. A wata ma’anar kuma tana kasancewa wani yanayi na zaluntar wani ko yaudara da duk wani abu mai kama da waɗannan. Aƙilu ya yi amfani da wannan kalmar domin ya nuna wasu daga halayen karuwai. Misali idan aka duba baiti na 33 da na 53.

    33. Ga ta da sakarci da gadara,

     Ga cuta da riga kai ƙara.

    53. Gara akwara akwai ta birki,

     Cutar Karuwa ba ta makanga.

      (Aƙilu Aliyu: Waƙar ‘Yar Gagara)

     

     Waɗannan baituka suna bayyana irin yanayin halayen karuwai. Aƙilu ya bayyana waɗannan halaye ne domin masu neman karuwai su guji halayen karuwan su kuma ƙaurace masu.

     Abin nufi a nan shi ne, baiti na 33 ya bayyana cewa, karuwa za ta fara cutar mutum kuma ta kai shi ƙara ko ta fallasa shi a matsayin wanda ya cuceta. Shi kuma baiti na 53 yana bayyana cewa, cutar karuwa ba ta da abin da ke tare ta sai dai in ba a yi hulɗa ba. Saboda haka ƙauracewa shi ne maganin cutar karuwai.

    5.5 Saɓo.

     Wani yanayi ne na kauce wa dokoki musamman abin da ya shafi dokokin addini. Addini ya yi hani da wasu munanan ayyuka, amma wasu sun kasance suna aikatawa. Misali addini ya yi hani da zina, amma wasu ba su daina ba. Yin zina da ma duk wani abu da ya ci karo da dokar addini saɓo ne. Ita kuwa karuwa mafi yawan harkokinta duk na saɓo ne. Aƙilu ya bayyana wannan a baiti na 4, da na 36. Ga yadda abin yake.

    4. Karuwa ba ta nufin ta yi aure,

     Kai dai bar ta ga saɓon Sarki.

    36. Ban da nishaɗa ba ta da aiki,

     Ma halwa tata saɓon Sarki.

      (Aƙilu Aliyu: Waƙar ‘Yar Gagara)

     Yin aure sunna ce ta Annabin rahama SAW. An yi umurni a ayoyin Alƙur’ani Maigirma da Hadisai daban-daban kan cewa a yi aure. Ita kuma karuwa ta ƙi yi. An yi hani ga zina ko ma kusantar ta, ita karuwa ta ɗauke ta sana’a. Ba a buƙatar duk wani abu da ya keta dokokin addini, ita karuwa su ne halayenta. Don haka Aƙilu ya bayyana wannan a cikin halayenta, cewa ita mai saɓo ce, shi kuma mai saɓo, ba ya halatta a zauna tare da shi sai da lalura.

    5.6 Cikin Shege

     A al’adance duk wadda ta samu juna biyu ba tare da aure ba, to ta yi cikin shege. Shi kuma cikin shege wani al’amari ne mai girma a al’adun Hausawa da ma Musulunci. Babu mamaki idan karuwa ta yi cikin shege, saboda daman sana’arta kenan ta yi karuwanci don ta samu kuɗi. Aƙilu ya zo da wannan zance a baiti na 50-51. Misali.

    50. Ko ta sami ciki ɗan birni,

     Don a sayan ta itacen wanka.

    51. Kayan yaji, tare da ƙauri,

     Har a saya mata ragon suna.

      (Aƙilu Aliyu: Waƙar ‘Yar Gagara)

     

     Aƙilu bai kira cikin shege ƙarara a nan ba, amma kuma idan aka bi ma’anar ɗangonsa na farko a baiti na 51 za a fahimci cewa cikin shege yake nufi wato ciki ɗan birni da ya faɗa shi ne cikin shege. Abin nufi a nan shi ne duk karuwar da ta ƙwanƙwashe birni take komawa inda ba wani wanda ta sani, kuma akwai jama’a da yawa waɗanda za ta iya yin mu’amula da su ta samu kuɗi.

    5.7 Cututtuka

     Wannan kalma ta samu ne daga cuta, ita kuma cuta wata ƙwara ce da ke shiga a cikin jikin mutum ta raunata lafiyarsa. Adamu, (1998), ya bayyana cewa, “Cuta tana nufin rauni da raɗaɗi tare da wahala da mutum kan gamu da su a sanadiyar gazawar wata halitta a jiki ko kuma damuwa a zuci”. Wannan kalma ta cuta ba irin waccan ce da muka yi bayani ba da farko. Aƙilu ya yi amfani da wannan kalma a baiti na 49. Misali.

    49. Sai ta harbu da ƙazuwar birni,

     Ko ta gangara rafin sanyi.

      (Aƙilu Aliyu: Waƙar ‘Yar Gagara)

     A wannan baiti Aƙilu ya bayyana cewa, karuwa na samun wasu cututuka da suka haɗa da ƙazuwar birni, wato wani ciwo mai ɓata jikin mutum, ko ma mai karya garkuwar jiki. Haka kuma tana iya kamuwa da ciwon sanyi wanda aka sani ana samu ga mata ko maza.

    5.8 Yawon Garuruwa

     Karuwai suna yin yawace-yawace daga wani gari zuwa wani domin gudanar da sana’arsu ta karuwanci. Aƙilu ya bayyana haka a cikin wannan waƙa. misali a baiti na 73 da 74 da kuma 75.

    73. Sai ka ga na shiga jirgin yamma,

     Ga ni a Zariya tun sassafe.

    74. Ka san can ɗin ma da gwanina.

     Wanda ya damu da aike kullum.

    75. Har a tasha zai zo tarba na,

     San da ya sami wayar na taso.

      (Aƙilu Aliyu: Waƙar ‘Yar Gagara)

     Wannan ya nuna cewa karuwai suna barin garin da suke, su je wani gari yawon karuwanci. Marubucin waƙar ya yi amfani da salon yin hira tsakanin Malam da karuwa. Idan muka dubi abin da karuwar take faɗa wa Malam a cikin hirar ta bayyana cewa tana barin garin da take ta shiga jirgin safe ta je wani gari wato Zariya.

    5.9 Shiga Malamai da Bokaye

     Wannan wani tsari ne da wasu kan shiga wanda ya ta’allaƙa ga biyan buƙatunsu na rayuwa. Wasu sukan shiga domin su yi cuta wasu kuma domin su samu kariya. A fanni karuwanci kuma shiga malamai ko bokaye ba wani abin kunya ba ne. Aƙilu ya bayyana wannan halayyar a waƙarsa domin ya ƙara fito da babban jigonsa na Faɗakarwa/Gyaran Hali. Ga yadda abin ya ke a baiti na 19.

    19. Sai fa na dinga shiga malammai,

     Bokaye, a haɗan wani dauri.

      (Aƙilu Aliyu: Waƙar ‘Yar Gagara)

     

     Wannan ya nuna cewa, karuwai suna shiga malamai ko don sa’a ko kuma domin kariya ga wasu cututuka. A wannan baiti dai abin da karuwar ke faɗa shi ne, an yi mata auren dole wannan ya sa ta shiga malamai don ta kashe auren ta fito. Amma fa ya bayyana cewa ita mai ƙarya ce don haka ko ta shiga malamai da bokaye wata kila ba don abin da ta faɗa ba.

    6.0 Kammalawa da Sakamakon Bincike

    Nazarin waƙoƙin Hausa musamman rubutattu na da matuƙar muhimmanci, domin yanaye-yanayen waƙoƙin da sigoginsu, shi ya sa bincike kan su zai zama mai fa’ida sosai, musamman idan aka yi la’akari da irin saƙon da suke son isarwa. A yayin nazarin halayyar karuwa, waƙar “’Yar Gagara” ta Alhaji Aƙilu Aliyu, an tsinkayi wasu muhimman saƙonni da yake son isarwa ga jama’a, musamman ƙoƙarinsa na faɗakar da jama’a kan abin da ya shafi ILLAR KARUWANCI. Da nazarin ya yi zurfi sai aka lura da akwai hangen nesa irin na magabata da zai sa mutane su lura da illar da ke tattare ga karuwanci. Wannan ya sa Aƙilu ya yi amfani da damarsa ya yi kira ga al’umma da su guji karuwai. Sakamakon binciken da aka gano a wannan maƙala, ya fito da halayyar karuwa fili kamar yadda Alhaji Aƙilu ya zo da su a cikin waƙarsa (‘Yar Gagara). Inda ya zo da halayya kamar ƙarya, cuta, cin amana, yawon garuruwa, biyar bokaye da dai makamantansu.

    MANAZARTA

    Auta, A. L. (2017) Faɗakarwa a rubutattun waƙoƙin Hausa, Kano: BUK Press

    Aliyu, A.A (1979): Fasaha Aƙiliyya, Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.

    Bargery, G.P (1934) A Hausa English Dictionary & Hausa Vocabulary, London: Oxford University Press.

    CNCH, (2006), Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, Zaria: Ahmad Bello University Press

    Ɗangambo, A. (2007) Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa, Kaduna: Amana Publishers Limited.

    Gusau, S.M (1995): Jagoran Nazarin Waƙar Baka, Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Gusau, S.M (2008), Waƙoƙin Baka a ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu, Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Sarɓi S.A (2007) Nazarin Waƙen Hausa, Kano: Samrib Publishers.

    Yahya, A.B. (2007) Jigon Nazarin Waƙa, Kaduna: Fisbas Media Services.



    [1] Sanin al’umma ne cewa auren dole akasari shi ke kai ‘ya’ya mata ga karuwanci. A al’adar Hausa uba yana da ikon ya aurar da ‘yarsa ga wanda ya so, ko da yarinyar ba ta yadda ba. Sai dai kuma yanzu da addinin musulunci ya zo ya yi hani a kan wannan aka rage. Don haka wannan na daga cikin manyan dalilan da suka haddasa karuwanci ga ‘ya’ya mata.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.