Ticker

6/recent/ticker-posts

Albarkacin Ranar Hausa: Zuwa ga Rabiu Isah Hassan

Albarkacin #RanarHausa

Zuwa ga Rabiu Isah Hassan

Hausawa sun rayu a doron ƙasa sama da shekara dubu 60!

Da alama dai naka binciken na daban ne, domin ba ka ma iya bambancewa tsakanin Hausawa da harshen Hausa ba. Idan ba Hausawa a doron ƙasa cikin shekara dubu 60, to ina suka maƙale sai shekara dubu 5 da suka wuce aka sako su? Shi kuma harshen Hausa da kake magana ya fito daga tsatson ahalin Afrika da Asiya ya wanzu ne a tsakanin shekara dubu 9 zuwa 10, ka ga ke nan maganar shekara dubu 5 da ka ce ya samu, kana zancen zamanin Annabi Musa ne da makusantan sa, wanda mun bayyana dangantakar wannan da rayuwar Hausawa ta dauri a maƙalun da muka buga na ilimi a lokutta mabambanta a baya, a leƙa ƙila a ƙara samun haske!

Idan ba ka sani ba ina ƙara sanar da kai cewa Hausawa mutane ne ba aljannu ko mala'iku ba, sun wanzu tun farkon halittar Adamu da Hawwa'u, sun kuma wanzu ko bayan ruwan ɗufana, wato a cikin halittar ahalin Annabi Nuhu da suka rayu a cikin kwale-kwale na kusan shekara biyu. Sun kuma fito daga tsatson mutanen da suka samar da al'ummar duniya na zamani daga yankin Omo-Kibish a ƙasar Habasha ta yau, sama da shekara dubu ɗari da hamsin da suka wuce. Bulaguro ya kai wasu daga cikin su zuwa da kuma wanzuwa a nahiyar Asiya da yankin Larabawan dauri tun daga shekara ta dubu 60 zuwa dubu 40 da suka zaunu a waɗannan yankuna.

Haka daga shekara dubu 20 a daidai lokacin da yankin Amurka ya fara ginuwa; (idan ba ka sani ba, yankin Amurka duka-duka ya wanzu ne shekara dubu 15 da suka wuce) ko a wannan lokaci  waɗannan al'umma ta Hausawa suna a doron ƙasa, sun rayu a Kudancin Masar, inda yawancin ahalin Hausawa ta ɓangaren Uba suka wanzu, suka rayu da kuma musamman yankin Siwa, wanda ke a Yammacin ƙasar Masar da iyakar ƙasar Libya kusan shekara dubu 20 da suka wuce.

Idan ka nazarci harsuna da al’ummar waɗannan yankuna, musamman daga yankin Maleshiya a Asiya da yankin Larabawa, musamman ɓangarorin Yemen da Falasɗinu da Saudi Arabiya da Masar da Isira’ila za ka tsinci wasu al’adun Hausawa da addinai da wasu kalmomi na harsunan waɗannan yankuna a cikin rayuwar Hausawa ta yau; dubi lamarin bautar rana, abinci da sutura da soyayya da mulki da waƙe-waƙen gargajiya. Akwai misalai na kalmomin Hausa na yau da suka samo asali daga waɗannan yankuna da addinai da al'adu in kana son ƙarin ilimi.

Bayan wannan zama na tsawon tarihi a Arewacin Afirka, a tsakanin ‘yan uwa da abokan hulɗa kamar su Kibɗawa da Yahudawa da Misirawa, wannan al'umma ta yi hijira zuwa yankin kogin Chadi da ke a tsakiyar Afirka, a wannan lokaci yankin mai dausayi ne da lema da ke ɗauke da manyan dabbobin ruwa da na daji. A zamansu ne na wannan yanki aka samar da harshen da aka yi wa laƙabi da Ahalin Afrika da Asiya a daidai shekaru dubu 9 zuwa 10, KHA, nan kuma aka samar da tsatson Ahalin  harsunan Chadic, wanda ya haifar da harshen Hausa da 'yan uwansa, irin su Gwandara da Ron da Tangale da Warji  da Bade da Angas da Barawa da Kare-Kare da sauran su. Sai daga baya da dausayi da lemar da ke a wurin suka bushe, hamada ta bayyana, al'ummar Hausawa suka watsu zuwa sassa daban-daban na tsakiyar Afrika da suka haɗa da Habasha da Libya da Kamaru da sassan ƙasar Hausa da dama na yanzu.

Wannan shi ya haifar da damar da aka samu suka sake haɗuwa da sauran 'yan uwansu, musamman na ɓangaren jinin Uwa da ba su yi bulaguro zuwa ko'ina ba a sassan duniya, suna zaune a nahiyar Afirka a tsawon shekaru. Wannan haɗakar barbarar 'yan'yawa ita ta samar da kai da ni da duk wani Badauri ko Bagobiri ko Bakatsine ko Bazamfare ko Bakabe ko Bazazzage ko Basantolo ko Bakano ko Bagunge ko Bahaɗeje ko Barane da wasu ƙasashe da al'ummun Hausawa da dama da suka yi rayuwa suka ɓace a tsawon tarihi.

Wannan ba komi yake nuna mana ba sai cewa Hausawa ba na yanzu ba ne, shi harshen Hausa ne na yanzu, shi ma ba yanzun-yanzu irin na yau ba ne, shekara dubbai ne ake magana.

Na ɗauki wannan tsawon lokaci ina maka wannan taƙaitaccen bayani ne domin na fahimci kana ƙishirwar ilimin asalin Hausawa da harshen Hausa, sai dai da alama ba ka neman ruwan sha mai sanyi domin kawar da ƙishin, shi ruwan zafi da kake sha, ba abin da zai ƙara maka sai ƙone maƙoshi, ba dai ya biya buƙata ba!

Bincike ake yi Malam Rabi'u ba shaci-faɗi ba ne, bincike ne na sanin asali ba kuma na kunne ya girmi kaka ba ne, bincike ne da ya haɗa da na tarihi, labarin ƙasa, kimiyyar halitta da na ƙwayar halitta da na hijira da bulaguro da samuwar harsuna da addinai da ginuwar zamantakewar al'umma tun daga samuwar ɗan Adam na zamani.

Allah ya sa ka tsinci wani abu daga wannan jawabi. Idan kuma akwai wani ƙarin haske da kake da shi kan wannan batu, muna jira da buƙata domin mu ɗaliban ilimi ne ba na hasashe da jita-jita ba!

Daga Prof. Ibrahim Malumfashi

Allahu a’alam!

Ranar Hausa Ta Duniya (International Hausa Day)

Post a Comment

0 Comments