As-Salaam Alaikum.
Wani ne ya turo wani saƙon hoto ta shafin Whatsapp, kamar haka
Sunnis
Vs Salafis (Tsakanin Sunnah da Salafiyyah). A ƙasa kuma ya rubuta: Hands in
Prayer (Mazaunin Hannuwa a Sallah). A ƙasa da wannan kuma hotunan mazaje guda
biyar ne a tsaye: Huɗu a haɗe, ɗaya kuma a ware. Na farko daga hagu ya sa masa
suna Shafi’i shi ne: Ya ɗora hanun dama a kan tsintsiyar hanun hagu a ƙasan
ƙirji. Na biyu shi ne: Hanbali, ya riƙe wuyan hanun hagu a ƙasar cibiya. Na uku
shi ne Hanafi: Ya ɗora hannun dama a kan tsintsiyar hanun hagu a ƙasar cibiya.
Na huɗu kuma shi ne: Maliki: Ya sauke hannuwansa a gefe jikinsa. Waɗannan ne ya
nuna su da cewa: Ahlus Sunnah Wal Jamaa’ah. Mutum na biyar shi ne ya kira da
Salafi: Ya ɗora hannun dama a bayan tafin hanun hagu da wuyan hanun da sashen
tsintsiyar hanun, dukkansu a kan ƙirji. Wannan kuma ya nuna shi da cewa:
Separate Sect (wai mazhaba ta daban). A ƙarshen rubutun da ke haɗe da hoton mai
suna: Sunnis Vs Wahhabis (Tsakanin ’Yan Sunnah da Wahabiyawa) ya siffata su da
cewa: ‘one of the most deviated sects (Wahhabis)’. Wato: Ɗaya daga cikin mafiya
fanɗarewar mazhabobi (Wahabiyawa). Sannan ya zarge su da: ‘Upholding the old
Sunnah of Christians/Jews’ (Wato, raya Sunnar Kiristoci da Yahudawa).
Wanda
ya turo saƙon ya ce: Ko me za ka ce a kan wannan mas’alar? Da ma na daɗe ina
son yi maka wannan tambayar.
Amsa:
A869
Wa
Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
Abin
da zan ce shi ne
[1]
Da farko dai
1.
Tattaunawa a kan wannan mas’alar ta wannan hanyar a yau kuma a halin da ake
cikin ɓata lokaci ne, kuma taya ɓera ɓari ne kawai. Domin neman tayar da
jayayya da musu ne kawai.
2.
Mai neman fashin baƙi ko ƙarin bayani a kan irin waɗannan mas’alolin komawa ga
malamai yake yi a zaurukansu ko majalisinsu na karantarwa domin su fayyace masa
komai.
3.
Mai aika saƙo irin wannan tun farko a cikin social media ba neman amsa yake yi
ba. Kawai dai zargi ko kaskantarwa ne ga Salafiyyah, daga nan kuma a tayar da
fitinar musu da jayayya.
4.
Idan ba haka ba, meyasa ya ware Salafiyyah daga sauran mazhabobin uku, alhali
shi kansa ya nuna cewa Salafiyyah ɗin sun yarda da ɗora hanuwa, kamar sauran
mazhabobin uku?
5.
Meyasa bai ware Malikiyyah, waɗanda shi kansa ya nuna su a matsayin waɗanda
suka fanɗare ba? Su suka sauke hannuwa ba su yarda da ɗorawa ba, saɓanin sauran
mazhabobin uku?
6.
Idan har Malikiyyah ba ta zama fanɗararriya a kan wannan mas’alar ba, ta yaya
Salafiyyah za ta zama fanɗararriya a hakan, don kawai sun zaɓi ɗora hannuwa a
kan ƙirji ba a ƙasa da ƙirjin ba?
7.
Mazhabobi uku ne: Ɗora hannu a kan ƙirji, ɗorawa a ƙasan ƙirji, sai kuma wanda
bai yarda a ɗaga hannuwan ba. Waɗanne biyu ne suka fi kama da juna a cikinsu?
Amsar
a fili ta ke ga duk mai adalci.
[2]
Ware Salafiyyah daga cikin Ahlus-Sunnah kamar yadda mai hoton ya nuna babban
kuskure ne, domin
1.
Salafiyyah su ne Ahlus-Sunnah wal Jamaa’ah. Su ne Ahlul-Athar. Su ne
Ahlul-Hadeeth. Kuma su ke da siffofin Al-Firqatun Naajiyah da At-Taa’ifatul
Mansuurah da kuma Ahlul Ghurbah.
2.
Salafiyyah su suka kafe a kan karantar da Aqeedah Sahihiya a cikin al’umma,
kamar yadda Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da sauran
Annabawa suka yi.
3.
Wannan kafewar ce ta janyo tattaruwar maƙiya da yawa a kansu, daga cikin
al’umma da wajen ta, kamar dai yadda Annabawa suka sha wahala kowanne a cikin
jama’arsa.
4.
Duk muna jin yadda ’yan bidi’a suke ta ƙoƙarin bayyanar da munanan aƙidunsu na
shirka da maguzanci, amma Salafiyyah ce kan gaba a wurin mayar musu da martani
da taka musu birki.
5.
Ta yaya Salafiyyah za su tsaya magana a kan ɗora hannuwa a sallah, alhali ga waɗansu
ba su san bambancin Allaah Ta’aala da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam) ba!
6.
Ana ji da ganin maganganunsu na bai wa Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam) matsayin Allaah na neman taimako ko agaji daga gare shi a
lokacin aukuwar masifa!
7.
Duk kuwa da suna karanta Surah Al-Faatihah kullum a cikin sallolinsu, kuma suna
maimaita gaya wa Allaah cewa
{إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ}
Gare
ka kaɗai muke bauta, kuma daga gare ka kaɗai muke neman taimako. (Surah
Al-Faatihah: 5).
8.
Sanan kuma ga maganar Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)
suna karantawa cewa:
إِذَا سَأَلْتَ فَاسْأَلِ
اللَّهَ، وَإِذَا اسْتَعَنْتَ فَاسْتَعِنْ بِاللَّه
Idan
za ka yi roƙo ka roƙi Allaah ne, idan kuma za ka nemi taimako ka nemi taimakon
Allaah ne. (At-Tirmiziy: 2516, kuma ya hassana shi).
9.
Wanda bai gama gamsarwa ko wayar da kan jama’arsa ko mabiya ɗariƙarsa a kan waɗannan
abubuwan ne ba, har zai samu daman tattaunawa a kan waɗannan ƙananan
mas’alolin?
[3]
Ɗaukar Salafiyyah a matsayin wata mazhaba fanɗararriya ba daidai ba ne, domin
1.
Salafiyyah ba mazhaba ba ce, da ta fita daga cikin sanannun mazhabobin malaman
Ahlus-Sunnah wal Jamaa’ah, balle a zarge ta da fanɗarewa daga Mazhabobin da aka
sani.
2.
Salafiyyah tana da mabiya daga cikin malamai da ɗaliban ilimin na gaskiya, har
a cikin waɗannan ƙungiyoyi da mazhabobin na Ahlus Sunnah.
3.
Salafiyyah ita kanta ba wata ƙungiya ba ce da ta ware daga sauran al’ummar
musulmi. Shiyasa ba ta da wani shugaba mai tsara mata dokoki da ƙa’idojin
gudanar da al’amurranta.
4.
Salafiyyah sun amince da haɗin kai ko gwiwa da duk ƙungiyar musulunci mai neman
gaskiya kuma mai son bin Sahihiyar Sunnar Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam).
5.
Salafiyyah tana girmama malaman Sunnah masu karantar da Sunnah a bisa gaskiya
da tsoron Allaah, ko da kuwa suna da alaƙa da wata ƙungiya ko mazhaba ta Ahlus
Sunnah.
6.
Salafiyyah suna zafi ne kawai a kan malaman da suke ƙoƙarin shure Sunnar Annabi
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) domin bin wani ra’ayi ko wata fahimta
ta ƙungiya ko mazhaba.
7.
Salafiyyah ba ra’ayi ba ne na ganin dama, shiyasa wani ba zai ce yana da zaɓin
ransa a kan abin Sunnah Sahihiya ta tabbatar ba. Domin Salafiyyah tsantsar
addinin Musulunci ta ke bi.
8.
Salafiyyah hanya ce ko kuma tafarki ne na fahimtar sahihin addinin Musulunci,
kamar yadda ya zo daga Manzon Allaah Annabi Muhammad (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam).
9.
Salafiyyah suna bin Alqur’ani da Sahihiyar Sunnah ne a bisa fahimtar Sahabbai
da Tabi’ai, ba tare da maƙalewa a kan ra’ayin wani ɗaya daga cikinsu ba.
10.
Salafiyyah tana bin dukkan limaman mazhabobin Ahlus Sunnah. Kuma a lokacin saɓaninsu
da juna tana kallon hujjojin kowannensu, ta zaɓi wanda a fahimtarta shi ya fi
kusa da daidai.
11.
Salafiyyah tana bin ƙa’idojin Usuulul Fiqhi da Al-Qawaa’idul Fiqhiyyah da
malaman Ahlus-Sunnah Magabata suka shimfiɗa ne wurin fahimtar nassoshin
Al-Kitaab Was Sunnah.
12.
Salafiyyah ba ta kallon girma ko shaharar limamin mazhaba ko yawan mabiyansa.
Duk wanda maganarsa ta dace da daidai shi ne kawai take yarda ta bi shi, ko da
kuwa shi kaɗai ne.
13.
Salafiyyah suna matuƙar neman haɗin kan al’ummar musulmi a kan gaskiyar da ta
tabbata daga Alqur’ani da Sunnah a bisa dacewa da fahimtar Sahabbai da Tabi’ai.
14.
Salafiyyah ba su ƙin yin sallah a bayan wani limamin Ahlus-Sunnah domin kawai
suna da bambancin fahimta da shi a kan waɗannan mas’alolin na fiqhu.
15.
Salafiyyah suna ƙyamar rabuwa don bambancin fahimta a kan: Ɗaga hannu a sallah,
ko ɗora hannuwa ko saukewa, ko qunuti a sallar Asubah, ko zaman istiraahah, ko
sallama da sauransu.
16.
Salafiyyah suna ganin bai dace a tsaya jayayya a irin waɗannan mas’alolin ba,
musamman a lokacin da ake fama da manyan mas’alolin da suka fi su girma da
muhimmanci ga al’umma.
[4]
Sannan kuma
1.
Bambancin fahimtar malaman mazhabobi a kan inda za a ɗora hannuwa a lokacin
tsayuwa a cikin sallah ba ɓoyayyen abu ne a wurin Salafiyyah ba.
2.
Tun tuni malaman Salafiyyah irinsu: Al-Allaamah Al-Albaaniy (Rahimahul Laah) ya
kawo wannan bambancin fahimtar a cikin littafinsa Sifatus Salaah da asalinsa:
Aslu Sifatis Salaah.
3.
A ciki har sai da ya ambaci waɗannan hujjojin da wannan marubucin ya kawo daga
asalinsu, kuma ya bayar da kyakkyawa kuma ƙaƙƙarfar martani gare su.
4.
Saboda ƙaunar Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a wurin
Salafiyyah, shiyasa ba su barin maganarsa domin ra’ayi ko fahimtar wani malami
mai girma a wurinsu.
5.
Hadisin Waa’il Bn Hujr; da na Qabeesah Bn Hulb daga babansa; da riwayar Taawus;
da kuma riwayoyi biyu daga Aliyu Bn Abi-Taalib sun bayyana a fili cewa, a kan
ƙirji ake ɗora hannuwan.
6.
A wurin Salafiyyah ba zai yiwu su bar waɗannan riwayoyin guda biyar da suka zo
ta hanyoyi mabambanta kuma masu ƙarfafar juna ba, su koma ga riwayar da ko
isnadinta ma ba a gani ba!
7.
Ina nufin riwayar da su kansu ba su tabbatar da ingancinta ba, domin kalmar
‘ruwiya’ da aka yi amfani da ita, abin da take nunawa kenan a wurin malaman
hadisi muhaqqiqai
فِي رِوَايَةِ الْمُزَنِي:
وَيَكْرَهُ - أَيْ:الْإِمَامُ أَحْمَدُ - أَنْ يَجْعَلَهُمَا عَلَى الصَّدْرِ. وَذَلِكَ
لِمَا رُوِيَ عَنِ النَّبِيِّ - صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - أَنَّهُ: نَهَى
عَنِ التَّكْفِيرِ. وَهُوَ
وَضْعُ الْيَدِ عَلَى الصَّدْرِ . اهـ.
Al-Imaam
Ahmad yana ƙyamar a ɗora su (hannuwan) a kan ƙirji. Wannan kuwa saboda abin da
aka riwaito daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa, shi ya
hana yin at-takfeer, wato: Ɗora hannu a kan ƙirji! (Badaa’i’ul Fawaa’idi:
3/91).
Wannan
a riwayar Al-Muzaniy daga Al-Imaam ɗin kenan. Amma a riwayar da ɗansa Abdullaah
ya yiwo daga gare shi akwai bambanci. Ya ce
"
رَأَيْتُ أَبِي إِذَا صَلَّى؛
وَضَعَ يَدَيْهِ إِحْدَاهُمَا عَلَى الْأُخْرَى فَوْقَ السُّرَّةِ
".
Na
ga babana idan yana sallah, sai ya ɗora hannuwansa ɗaya a kan ɗayan a saman
cibiya. (Masaa’ilu Ahmad, shafi: 62).
Wannan
riwayar ita ta fi kusa da waɗancan guda biyar ɗin, domin ‘sama da cibiya’ - ba
a ‘kan cibiya’ ko ‘ƙasa da cibiya’ ba -, shi ya kusa kai wa ga ƙirji kenan!
8.
Akwai malaman da suka yi aiki da wanan Sunnar ta ɗora wa a kan ƙirji.
Al-Marwaziy ya ce
"
كَانَ إِسْحَاقُ يُوتِرُ
بِنَا ... وَيَرْفَعُ يَدَيْهِ فِي الْقُنُوتِ، وَيَقْنُتُ قَبْلَ الرُّكُوعِ، وَيَضَعُ
يَدَيْهِ عَلَى ثَدْيَيْهِ أَوْ تَحْتَ الثَّدْيَيْنِ ".
Is’haaq
(Ibn Rahwuyah) ya kasance yana yin Wutri da mu… kuma yana ɗaga hannuwansa a
cikin Al-Qunut, kuma yana yin al-Qunut ɗin kafin ruku’u. Kuma yana ɗora
hannuwansa a kan nonuwansa ko kuma a ƙasa da nonuwansa. (Al-Masaa’il, shafi:
222).
9.
Haka kuma a cikin littafin Al-I’laam na Al-Qaadiy Iyaad Al-Maalikiy a lokacin
da yake lissafa Mustahabban Sallah ya ambaci cewa
"
وَوَضْعُ الْيُمْنَى عَلَى
ظَاهِرِ الْيُسْرَى عِنْدَ النَّحْرِ " .
Da ɗora tafin hannun dama a kan
bayan hannun hagu a wurin kwarin ƙirji. (Al-I’laam, shafi: 15).
[5]
Daga ƙarshe dai
1.
Zargin Salafiyyah da rayar da Sunnar Yahudawa da Kirista, don wannan mas’alar
ta ɗora hannuwa a kan ƙirji, kamar yadda marubucin ya yi, ya rage ga mai karatu
ya san matsayinta.
2.
Tun da dai hadisai sahihai ne Salafiyyah suka bi waɗanda suka nuna hakan,
wannan shaguɓen ko gugar zanar da aka yi, ba su ne abin zai shafa ba. Har mai
hadisan ma abin zai shafe shi.
3.
Don haka ban sani ba ko marubucin zai iya ƙarfin halin maimaita rubuta cewa,
hadisan Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) sun rayar da Sunnar
Yahudawa da Kiristoci?!!
Allaah
ya kare mu. Ya kiyashe mu da son zuciya.
Wal
Laahu A’lam.
Sheikh
Muhammad Abdullaah Assalafiy
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.