Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Yi Sallah Da Najasa A Jikinsa Ko Tufafinsa Bai Sani Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam mace ne bayan tayi tsarki daga al'adanta to sai akwai kayan data saka alokacin al'adarta sai tayi sallan asubah da kayan sai tacire su washe gari kuma mah takuma yin asubar dasu sannan tacire to sai wajen azahar ta wannan ranar kawai sai taga wannan kayan datayi sallar asuba dasu sau biyu akwai ɗigo ɗigon wannan jinin al'adar ajiki to Malam ya matsayin wannan sllar asubar guda biyu datayi da wannan kayan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Sallah tayi saboda ai bata sani bane cewa tufafin da jini, saboda hadisin annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) wanda mala'ika jibrin yazo ya same shi da sahabbai suna Sallah kowa da takalminsa a ƙafarsa, sai aka ga Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya cire takalminshi sai sahabbai ma suka cire nasu bayan ya gama sallar sai ya tambayesu mai yasa suka cire takamansu sai suka ce ai sunga ya cire nashi ne, sai yace ni mala'ika jibril ne ya sanar dani cewa ƙarƙashinsu akwai najasa, don haka idan ɗayanku yazo zaiyi Sallah da takalmansa to ya duba ƙasansu idan da najasa ya goge, kuma ba a samu wata riwaya da ta nuna cewa Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya biya wannan sallar da ya sallata da takalaminsa mai najasaba, da wannan malamai ke cewa duk lokacin da mutum yayi Sallah da najasa a jikinsa bai sani ba sai daga baya ya gani sallarshi tayi ba sai ya sake ba.

Wannan bayani na cikin fiqhul ibadat da sheikh uthaimin da fatawarsa, da fatawa ibn baaz, da fiqhussunah na saidussabiq a juz'i na 1.

WALLAHU A'ALAM

Amsawa: Mal Adam Daiyib

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments