TAMBAYA (138)❓
Assalamu
alaikum. Malam Ina wuni, ina gajiya, ya aiki, ya iyalai
So, malam nidai tambaya nakeyi, Allah yasa an san amsa ta, yau sati na daya da yin aure kenan, nidai muna jima'i da miji na, malam, shi yana gamsuwa, nice dai bansan ya gamsuwar take ba malam, ko dan ina farin shiga. Sannan kuma malam, idan har sperm ya shiga cikin jikin mace, akwai wani sign da za ta ji ne alama na maniyyi ya shigeta ko ko ba wani sign. Allah ya karawa malam lafiya. Nagode sosai
✍️AMSA A TAQAICE
Waalaiki
Salam, Warahmatullahi, Wabarakatuh
(Dadin
saduwa zai iya mantar dake ko maniyyin ya shiga ko bai shiga ba duk da dai yana
wahala ace mace ta manta amman shi namijin yasani cewar ya shiga ko akasin
haka. To kinga kenan ba abin damuwa bane idan kinji alamun sperm din nashi bai
shige gabanki yanda kike tunani ba musamman ma la'akari da ke sabon shiga ce.
Kawaidai kada ku manta da addu'ar saduwa kafin ku fara)
Bismillaahir
Rahmaanir Raheem
Tabbas
ana samun irin haka ga sabbin ma'aurata, musamman ga mace
Amman
yau da gobe za tasa ki ji kin saba, in sha Allahu
Shi
sperm ai yana shiga mahaifa ne kai tsaye, kuma ai zaki ji alamun shigarsa da
zarar mijinnaki ya kawo (releasing)
Idan
kuma ba ki ji shigar sa din ba, kada ki damu da wai dole ne sai kin ji shigar
sperm din ba, domin kuwa kowanne release daya tak da akwai halittu a cikin
maniyyin masu rai at least ko kuma sama da miliyan ashirin (20,000,000) wanda a
cikinsu guda daya ne tak yake karasawa mahaifa a raye duk sauran mutuwa sukeyi
silar attack (feshin) chemicals da suke samu daga white blood cells
Guda
daya dinnan ne yake haduwa da egg cell (maniyyin mace) sai a samu zygote bayan
fertilization ya faru, bayan kuma kwanaki 40 sai ya koma jini, 80 days ya zama
tsoka sannan a 120 days ya zama qashi daganan sai a busa masa rai
To
kinga kenan ba abin damuwa bane idan kinji alamun sperm din nashi bai shige gabanki
yanda kike tunani ba
Sannan
kuma matuqar ba ta baya (dubura) mijinki ya sadu dake ba to ba laifi yazo miki
duk ta yanda yaso saboda fadin Allah (Subhanahu wata'ala)
( نِسَاؤُكُمْ حَرْثٌ
لَّكُمْ فَأْتُوا حَرْثَكُمْ أَنَّىٰ شِئْتُمْ ۖ
البقرة (223) Al-Baqara
Mãtanku
gõnaki ne a gare ku, sabõda haka ku je wa gõnakinku yadda kuka so
Kawaidai
shawarar da zan baki anan itace kada ku manta da addu'ar da Annabi (Sallallahu
alaihi wasallam) ya koyar kafin saduwa aure. Itace
بِسْمِ اللهِ اللّهُمَّ جَنِّبْنَا
الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا.
"Bismil-lah,
allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana"
Ma'ana
"Da
sunan Allah. Ya Allah! Ka nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da
shaidan daga abin da Ka azurta mu da shi"
Wallahu
ta'ala a'alam
Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu
anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa
Usman
Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.