TAMBAYA (133)❓
Assalamu Alaikum, Allah ya gafarta Malam , Ina Da Tambaya Dan , ya Ake hudubar jariri Idan an haifi Shi Da Radin Suna ??? Nagode sea Naji Daga gare ku 🙏🙏
✍️AMSA A TAQAICE
Waalaikumussalam,
Warahmatullahi, Wabarakatuhu
(Ibn
al-Mundhir ya fada a cikin littafinsa Al-Awsat cewar Annabi (Sallallahu alaihi
wasallam) ya umarci mutane su dinga saka suna a rana ta bakwai da haihuwa,
wanda karshen riwayar hadisin ta kare daga Abdullahi Ibn Amr (Radiyallahu anhu)
(Al-Ishraf
ala Madhahib al-Ulama #3/421)
Sannan
kuma hudubar da akewa jarirai ba sunnar Annabi (Sallallahu alaihi wasallam)
bace ba. Imam al-Bayhaqi yace ruwayoyin wadannan hadisan duk basu inganta ba
duk da'efai ne
(Shu'ab
al-Iman #8620)
Bismillaahir
Rahmaanir Raheem
Dangane
da huduba a kunnen jariri da akwai mabanbanta riwayoyi akan hakan
Na
farko
An
karbo daga Abu Abdullah Al-hakim, daga Abu Ja'far Muhammad Ibn Duhaym, daga
Muhammad Ibn Hazim Ibn Abu Gharzah, daga Ubaidullah Ibn Musa, daga Sufyan Ibn
Sa'id Al-Thawri, daga Asim Ibn Ubaidullah Ibn Rafi' daga mahaifinsu (Allah ya
kara yarda a garesu baki daya) ya ce: Naga Annabi (Sallallahu alaihi wasallam)
yana kiran sallah (adhan) a kunnen Hasan Ibn Ali, a lokacin da Fatima
(Radiyallahu anha) ta haife shi
(Abu
Dawud #5150 da Tirmidhi #1514 ne suka rawaito, sunce hadisi ne Sahih. Imam
Ahmad yace da'ef ne a cikin Musnad dinsa 6/9, 362, 391)
Na
biyu
Imam
al-Bayhaqi ya rawaito Hadisi a cikin littafinsa 'Al-Shu'ab', an karbo daga
Al-Husain Ibn Ali (Radiyallahu anhu) ya ce: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam)
ya ce: "Duk wanda aka yi masa haihuwa sai ya kira sallah (adhan) a
kunnensa na dama ya yi iqamah a kunnensa na hagu, za'a nesanta dan daga qarin
(aljaninsa)"
(Abu
Ya'ala a cikin Musnad dinsa #6780, Ibn Adi' a cikin Kamil dinsa #7/2656,
Bayhaqi a cikin Shu'ab al-Iman #8619. Saidai wannan ba tauqifi bane ma'ana ba
daga bakin Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) aka ji hakan ba)
Na
uku
An
karbo daga Abu Sa'id, daga Ibn Abbas (Radiyallahu anhuma) cewar Annabi
(Sallallahu alaihi wasallam) yayi kiran sallah (adhan) a kunne Hasan Ibn Ali na
dama da kuma iqamah a kunnensa na hagu
Bayhaqi
yace ruwayoyin wadannan hadisan duk basu inganta ba duk da'efai ne
(Shu'ab
al-Iman #8620)
Dalilin
da yasa ake kiran sallar (Allah ne mafi sani) shine saboda ana son yaron ya
fara jin sunan Allah da kuma musulunci da zarar ya shigo duniya kamar dai yanda
ake son ya firta kalmar shahada da zarar mutuwa ta riske shi lokacin da zai bar
wannan duniyar
Dangane
da radin suna kuma koyi da sunnah shine a radawa jariri suna a rana ta bakwai
kamar yanda Muhammad Ibn Ali yaji daga Salih daga mahaifinsa har ma ya kawo
hujja daga hadisin Samura
Haka
kuma saka suna haqqin mahaifi ne ba na mahaifiya ba domin kuwa da sunan mahaifi
za'a kira mutum a ranar lahira. Za'a kira shi da wane-dan-wane, kamar yanda
Allah (Subhanahu wata'ala) ya fada
( ادْعُوهُمْ لِآبَائِهِمْ
هُوَ أَقْسَطُ عِندَ اللَّهِ ۚ
الأحزاب (5) Al-Ahzaab
"Ku
kira su ga ubanninsu, shi ne mafi ãdalci a wurin Allah"
To
kaga wannan ayar qalubale ce ga wadanda suke jingina sunansu da iyayen da ba
nasu ba. Sannan kuma bayan saka suna (ism) akwai laqabi (laqab) da kuma sunan
alkunya (kunyah). To ammanfa duk yanda za'ayi kada ku bari a dinga fada masa
sunan banza (alqab) domin Allah (Subhanahu wata'ala) ya hana hakan
وَلَا تَنَابَزُوا بِالْأَلْقَابِ ۖ
الحجرات (11) Al-Hujuraat
"...kuma
kada ku jẽfi
jũna da miyãgun sunãye na laƙabõbĩ..."
Sannan
kuma sunan da Allah ya fi so shine: Abdullah da Abdurrahman kamar yanda Ibn
Umar (Radiyallahu anhu) ya rawaito daga Annabi (Sallallahu alaihi wasallam)
(Sahih
Muslim #3/1682)
Abu
Wahb Al-Jushami ya ce: Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: "Ku kira
kanku da sunayen Annabawa. Sunan da Allah ya fi so shine: Abdullah da
Abdurrahman. Suna mafi gasgatawa shine Harith da Hammam, sunan da aka fi qyama
shine Harb da Murrah"
(Sahihul
Bukhari #813 da Abu Dawud #13/350. Duba littafin: "Tuhfatu'l Maudud bi
ahkam al-Maulud" na al-Hafiz Ibn al-Qayyim Aljawziyya - Rahimahullah)
Ina
fatan Allah ya albarkaci jaririn da aka samu, Allah ya tabbatar dashi akan
addinin musulunci da bin Sunnar Annabi (Sallallahu alaihi wasallam), Allah ya
rabashi da Bidi'ah da kafirci
Wallahu
ta'ala a'alam
Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu
anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa
Usman
Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.