Ticker

6/recent/ticker-posts

Wanne Istighfari Ne Ya Fi Falala

TAMBAYA (134)

Uncle Dan Allah men ene banbamcin ISTIGFARI da lafazin "astagfirullah wa'atubu ilaik" dakuma "astagfirullah" kadai

Wanne ya fi falala

AMSA

أستغفر الله وأتوب اليه

"Astaghfirullah Wa Atubu Ilaih"

Ma'anarsa

"Ina neman ya fiyar Allah kuma gareShi nake tuba"

Shi kuma

أستغفر الله

"Astaghfirullah" na nufin "Ina neman ya fiyar Allah"

Dukkansu suna da falala saidai na farkon shine ya fi saboda karin "kuma gareShi nake tuba"

Kamar mutum ne ya ce maka zan baka kyautar gida amman idan ka gyara halinka zan qara maka da kyautar mota

Haka kuma fadar

"Astaghfirullahallazi mallazi la'ilaha illa huwa alaihi tawakkaltu wahuwa rabbul arshil azim"

Wannan ya fi biyun farko dincan falala

Muhallish shahid din dai shine Allah ya karbi tuban bawanSa. Idan zai karba bayan ka firta na farko to zai fi saurin karba idan na biyu dincan ka dage da fada haka kuma zai fi saurin karbar tubanka idan ka fadi na uku a maimakon na biyun

Allah (Subhanahu wata'ala) yace

( فَمَن تَابَ مِن بَعْدِ ظُلْمِهِ وَأَصْلَحَ فَإِنَّ اللَّهَ يَتُوبُ عَلَيْهِ ۗ إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ )

المائدة (39) Al-Maaida

"To, wanda ya tuba a bãyan zãluncinsa, kuma ya gyãra (halinsa), to, lalle ne Allah Yanã karɓar tubarsa. Lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai"

Ya Allah ka yafe mana zunubbanmu na fili da na boye

Wallahu ta'ala a'alam

 Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments