𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin
Mallam Yaya Mai Yawan Saɓon Allah Zai Kyautata Halinsa? kuma menene sharuddan
tuba?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Babu
shakka saɓon Allah abune dake haifarwa da bawa matsaloli masu yawa, amma kuma
Allah mai yalwar falalane matukar mutum yayi nadama yagane kuskurensa ya tuba
to lallai Allah mai yawan gafarta zunubaine, Allah maɗaukakin sarki yace
...وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ الْمُؤْمِنُونَ
لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
Kuma
ku tũba zuwa ga Allah gabã ɗaya, yã ku mũminai! Tsammãninku, ku sãmi babban
rabo. (Suratul Nur Aya ta 31)
Allah
yasake cewa
قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ
أَسْرَفُوا عَلَىٰ أَنْفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِنْ رَحْمَةِ اللَّهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ
يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ
Ka
ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi ɓarna a kan rãyukansu! Kada
ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya.
Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai." (Suratul zumar:l Aya ta 53)
Kalmar
tuba tana da girma da dalililai masu zurfi, ba kamar yanda wasu dayawa suke ɗauka
ba, kawai ka furta da harshe kuma kaci gaba da aikata laifuka, ka lura ka kula
da fadar Allah maɗaukakin sarki
وَأَنِ اسْتَغْفِرُوا رَبَّكُمْ
ثُمَّ تُوبُوا إِلَيْهِ...
Kuma
ku nẽmi gãfara gun Ubangijinku. Sa'annan ku tũba zuwa gare Shi...(suratul Hud
Aya ta 3)
zakasamu
a wannan aya cewa shi tuba wani al'amarine dayake karuwa ta hanyar neman
gafarar ubangiji. Kuma saboda duk wani babban al'amari zaka sameshi yana da
sharudda saboda haka malamai suka ambaci sharuddan tuba, waɗanda suka dakko
daka Alqur'ani da hadisai
1.
Barin zunubi da gaggawa.
2.
Yin dana sani akan abunda ka riga ka aikata na laifuka.
3.
Qudurta niyyar bazaka sake komawa wannan laifi ba.
4.
Maida hakkin wanda ka zalunta, ko barranta daka azzallumai idan da kaine kake
taimaka musu.
Bayan
waɗannan kada mutum ya manta dawasu al'amuran nadaban waɗanda sunada mahimmanci
kwarai wajen tabbatuwar tuba nagartacce,
1.
Yazamto dan Allah mutum yatuba daka zunubi, badan wani abu yabar laifin ba
kodan bashi da ikon aikata laifin, ko kuma kabar zunubi dan tsoran maganar
mutane, ba tuba bane wanda yabar zunubi dan kare mutuncinsa wajan mutane, ko
dan bashi da iko, ko dan kare lafiyarsa daka wata cuta da'ake samu daka
zunubin, ba'a kiran wanda yabar cin hanci ko karɓar rashawa dan yana tsoran
kada akamashi yasha tozarci, haka wanda yabar zina dan kada yaɗau cutukan
datake haifarwa, komai shangiyar dayabar shanta dan illolin datake haifarwa, ko
barawon dabashi da ikon yinsata ko danfashin darashin samun dama ce tasa ya
tuba, duk wani laifi indai badan tsoran ukubar da Allah yatanadar akai ba ka
tuba daka gareshi, to bakayi tuba wanda Allah yakeso ba.
2.
Wajibine ka dunga jin bakin ciki duk lokacin da katuno aikin zunubin daka
aikata abaya da kuma illarsa. Ana nufin tuba ingantacce baya yiwuwa tare dakana
jin daɗin abunda ka aikata abaya inkatuna, koma kadunga burin inama kasake
komawa nan gaba.
Ibnul
qayyeem acikin littafinsa Adda'u waddawa'a yakoro bayani akan illar zunubi da
kuma cutukan dayake haifarwa, daka ciki yace
Haramtawa
mutum ilmi, zunubi nasa kakasa samun nagartaccen ilmi ko kasamu ilmin amma mara
amfani, rashin kwanciyar hankali, Kuncin al'amura, cutar jiki, zunubai nasanya
Allah yahanawa ɗan adam ikon aikata abunda yake biyayyah ne ga Allah, dakuma
rashin albarka arayuwa, da karancin dacewa cikin duk abunda mutum zaiyi, da
kuncin rai, da zakkewa zunubai, dakuma aikata kananun laifuka, Bakin cikin mai
zunubi game da Allah da bakin cikinsa da mutane, da tsinuwar da dabbobi zasu
dunga yi masa, da rigar kaskanci dazai shiga, da bushewar zuciya dashiga
karkashin la'anta, dakin amsa addu'arsa, da aikata ɓarna afili da ɓoye, da
rashin kishi, da gushewar kunya atare da mutum, da gushewar ni'imomi, dasaukar
bala'i da saukar datsoro da firgici azuciyar mai saɓo, dafadawa cikin tawagar
Shaiɗan da mummunan karshe da kuma azaba alahira.
Inkasan
waɗannan illoli na zunubi zaisa kabar aikata laifi gaba ɗaya, domin wasu mutane
idan suka bar laifi saisu koma wani wanda aganinsu ma'aunin su ba ɗaya bane da
wanda suka bari, suna ɗaukar yafi sauki sauki akan wanda suka daina sauki.
Bayan
duk kabi matakan tuba idan kanada wasu abokai da kuke aikata wannan zunubi
wajibine ka canjasu da wasu, domin dayawa mutum kan tuba daka zunubi amma
sanadiyyar rashin rabuwa dawanda suke aikata laifin tare sai mutum yakoma
yasake fadawa cikin ɓata sama dawanda yake abaya, ko gurine ko majalisa dakake
tasirantuwa da ita wajibine ka kaurace mata kacanza dawata wacce zaka samu
ingantuwar tubanka da imaninka, kasamu abokai nagari masu addini waɗanda koda
basu umarceka da kyakkyawa ba zaka tasirantu dasu wajan aikata mai kyau kaima.
Ka
yaiwata aikata kyawawan ayyuka domin kyawawan ayyuka suna share munana. Allah
maɗaukakin sarki acikin suratul Furqaan bayan jero dangin manyan zunubai wanda
muminai nagari basa aikatawa kuma duk wanda ya aikata su za'a rufanya masa
azaba saiyace
إِلَّا مَن تَابَ وَآمَنَ
وَعَمِلَ عَمَلًا صَالِحًا فَأُولَٰئِكَ يُبَدِّلُ اللَّهُ سَيِّئَاتِهِمْ حَسَنَاتٍ
وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا
Sai
wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan
Allah Yanã musanya miyãgun ayyukansu da mãsu kyau. Allah Ya kasance Mai gãfara
Mai jin ƙai. (Suratul Furqan Aya ta 70)
Muna
rokon Allah ya shiryar damu zuwa ga abunda yakeso kuma ya yarda dashi, yakarbi
tuban mu gaba ɗaya domin shi mai yawan karbar tuba ne mai jinkai.
WALLAHU
A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.