𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu. Malam don Allah don Annabi inaso ataimakamani da wata sura ko azkar ko wata addu'a dazan rinkayi domin neman gafar Allah dakuma yaddarshi akan wasu abubuwa dana aikata na ba daidaiba dana aikata tsakanina dashi ngd
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa
alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh.
Babu
wata Surah da shari'a ta keɓe ga wanda ya aikata zunubi don neman gafara, sai
dai duk ɓangaren alqur'ani da mutum ya karanta, Allah zai amfani da hakan ya
tafiyar masa da zunubin da ya gabatar, Allah Yace:
...إِنَّ ٱلۡحَسَنَـٰتِ یُذۡهِبۡنَ
ٱلسَّیِّـَٔاتِۚ ذَ ٰلِكَ ذِكۡرَىٰ لِلذَّ ٰكِرِینَ
...Lalle
ne ayyukan ƙwarai sunã kõre mũnãnan ayyuka. wancan ne tunãtarwa ga mãsu tunãwa.
[Surah Hud 114]
Bayan
haka akwai addu'ar da aka shar'anta domin neman gafarar Allah dangane da
zunubin da bawa ya aikata. Annabi Sallallahu alaihi Wasallam Yace: Allah zai
yafe wa duk wanda ya karanta ta, ko da zunubinsa ya kai na wanda ya juyo baya a
fagen jihadi ita ce
أسْتَغْفِرُ اللهَ العَظِيمَ
الَّذِي لاَ إلَهَ إلاَّ هُوَ، الحَيُّ القَيُّومُ، وَأتُوبُ إلَيهِ
Ina
neman gafarar Allah, Allah babu abin bautawa da gaskiya sai shi, rayayye, Mai
tsayuwa da komai, kuma ina tuba zuwa gare shi.
Manzon
Allah Sallallahu alaihi Wasallam Yace: duk wanda ya karanta wannan Istighfarin
da safe, in dai ya mutu acikin wannan winin to shi Ɗan Aljannah ne. Idan kuma
ya karantashi da yamma, to in dai ya mutu acikin wannan daren shi Ɗan Aljannah
ne. Addu'ar itace
اللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي
لَّا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ، خَلَقْتَنِي وَأَنَا عَبْدُكَ، وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ
وَوَعْدِكَ مَا اسْتَطَعْتُ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ، أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ
عَلَيَّ، وَأَبُوءُ بِذَنْبِي فَاغْفِر لِي فَإِنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا
أَنْتَ
"Ya
Allah kai ne Ubangijina, babu wani abin bauta da gaskiya sai dai kai. Kai ne ka
halicceni Ni kuma bawanka ne. Kuma ina nan bisa alwashinka da Alkawarinka
(wanda na ɗauka) mutukar ikona.
Ina
neman tsarinka daga sharrin abinda na aikata, Ina yin furuci gareka da
ni'imarka agareni, kuma ina yin furuci da zunubaina. Ka gafarta min domin babu
mai yin gafarar zunubai sai dai Kai". (Imamul Bukhariy da Nisa'iy da
Tirmidhiy ne zuka ruwaitoshi.)
Akwai
wannan addu'a da aka keɓe a karanta sau ɗari da safe, sannan sau ɗari da yamma,
Allah zai yafe ma bawa zunubansa da ya gabatar, Addu'ar ita ce
أسْتَغْفِرُ اللهَ وَأتُوبُ
إلَيهِ
Manzon
Allah Sallallahu alaihi Wasallam Yace: "Ban Taɓa Wayi Gari ba Ko Da Sau
Ɗaya, Face Na Nemi Gafarar Allah A Wannan Ranar Sau Ɗari."
(Nasa'i
Ya Rawaito,Albany Ya Inganta)
Bayan
haka Annabi Sallallahu alaihi Wasallam Yace: babu wani wanda zai aikata wani
zunubi, sai yayi alwala, kuma ya kyautata ta, ya sallaci sallah raka'a biyu, ya
roƙe shi gafara, face sai Allah ya gafarta masa zunubansa komin yawansu kuma
komin girman su.
Bayan
haka azumi na kankare zunubai haka sadaka da kuma kyautata wa iyaye, iyali da
makusanta.
Manzon
ALLAH Sallallahu alaihi Wasallam Yace: “Duk wanda yake son takardar aikinsa ta
faranta ransa ranar alƙiyama toh ya yawaita neman gafarar ALLAH (Istighfari).” [Sahih
Al-Jàmi': 5955]
Don
haka dai, ƙa'ida ita ce duk wanda yake tsoron Allah ya kama shi da laifinsa,
toh ya yawaita istighfari, salatin Annabi, karanta alqur'ani, nafilfili da
sauran kyawawan aiyuka, saboda faɗin Allah
وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ طَرَفَیِ
ٱلنَّهَارِ وَزُلَفࣰا مِّنَ ٱلَّیۡلِۚ إِنَّ ٱلۡحَسَنَـٰتِ یُذۡهِبۡنَ ٱلسَّیِّـَٔاتِۚ
ذَ ٰلِكَ ذِكۡرَىٰ لِلذَّ ٰكِرِینَ
Kuma
ka tsai da salla a gẽfe guda biyu na yini da wani yanki daga dare. Lalle ne
ayyukan ƙwarai sunã kõre mũnãnan ayyuka. wancan ne tunãtarwa ga mãsu tunãwa.
[Surah Hud 114]
WALLAHU
A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.