Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Haila Za Ta Iya Riƙe Al'qur'ani Izu Goma?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam wai gaskiya ne mace mai haila za ta iya riƙe Al'Qur-ani izu goma?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. Abin da yafi zama daidai shine: Kar mai haila ta taɓa ko da wani ɓangare ne na Al'Qur-ani, saboda Hadisin Amru Bn Hazm wadda wasu Malaman Hadisin suka inganta inda Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) yake cewa: "Kar wanda ya taɓa Al'Qur-ani sai mai tsarki".

Amma ya halatta ta karanta ta hanyar kallo, saboda duk Hadisan da suka hana mai haila karatun Al'Qur-ani ba su inganta ba.

Allah ne mafi sani.

𝑨𝒎𝒔𝒂 𝒅𝒂𝒈𝒂 𝑫𝒓. 𝑱𝒂𝒎𝒊𝒍𝒖 𝒀𝒖𝒔𝒖𝒇 𝒁𝒂𝒓𝒆𝒘𝒂

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments