𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam, idan matar mutum ta biya masa bukatar sha'awarsa ta hanyar amfani da hannunta ko bakinta, shima istimina'i ne? Kuma shima akwai laifi agun Allah?? (DAGA L. M HASHIM).
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa
alaikumus salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.
Addinin
Musulunci ya yarda mutum yayi duk wani wasa da matarsa ko lokacin da take cikin
tsarki, ko alokacin da bazai yiwu ya sadu da ita ba, sanadiyyar jinin haila ko
biqi ko wata larurar.
Kuma
don mutum yayi inzali a irin wannan yanayin babu wani laifi akansa. Mutum dai
bai sadu da ita ta dubura ba, ko acikin jinin haila.
Game
da sanya al'aura a baki kuwa, akwai saɓani atsakanin Malamai. Yayin da wasu
maluman suke ganin haramcin hakan, wasu kuma sun ce ya halatta.
Waɗanda
suka ce bai halatta ba, sun kafa hujjah ne da cewar shi bakin ɗan Adam an
halicceshi ne domin cin abinci ko shan abin sha, ko ambaton Allah. Amma ba'a
yishi domin ya zama kafar saduwa atsakanin Ma'aurata ba.
Kuma
sun ce alokacin da ma'aurata ke tsotsar al'aurar junansu, lallai ne sai an samu
fitar maziyyi wanda shi babu saɓani atsakanin maluma bisa cewar najasa ne,
hukuncinsa ɗaya da fitsari. Kuma haramun ne musulmi ya haɗiye najasa..
Hujjarsu
ta uku kuma sun ce shi dai matse-matsin ɗan Adam ko kuma al'aurarsa waje ne da
ya zamto matattarar kwayoyin cututtuka. Shi kuma bakin ɗan Adam yakan zamto
kamar mashigar cutuka ayawancin lokuta idan aka aiwatar dashi ba bisa Qa'idah
ba. Kuma sau da yawa ana samun fitar kuraje da sauran cutuka acikin bakuna ko
harasan ma'auratan dake aikata wannan. Kuma yazo acikin mashahurin hadisi cewa
"BABU CUTA KUMA BABU CUTARWA". Wato kada ka cuci wani, kuma kada ka
jefa kanka cikin abinda zaka cutu.
Maluman
dake ganin halascin tsotsar al'aura atsakanin Ma'aurata, sun kafa hujjah da
cewa ai Allah da Annabinsa bai haramta yin haka acikin Alqur'ani ko hadisi ba,
Kuma duk abinda ya zamto haramun ne an riga anyi bayaninsa acikin Alqur'ani da
Sunnah kamar yadda muka bayyana abaya...
Kuma
sun kafa hujjar cewa ya halatta Ma'aurata su aikata duk wani abinda zai Qara
musu nishaɗi yayin saduwarsu mutukar dai Allah bai haramtashi ba.
Don
haka idan ma'aurata suka yi wasa da juna har yakai ga an samu inzali, wato
fitar maniyyi, ba haramun bane. Abinda aka haramta shine mutum ya aikata hakan
da kansa.
WALLAHU
A'ALAM.
DAGA
ZAUREN FIQHU 07064213990
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.