Tun yana karatun Allo a Makarantar Malam Bello Mai Wurno dake Unguwar Mad'unka a cikin Birnin Sakkwato, Hon. Dakta Usman Balarabe Shehu Kakale Shuni, Tsohon Ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya da ya wakilci Mazab'ar Tureta /Dange, Shuni /Bod'inga ya ke yiwa karatun wani kallo na musamman a zuciyarsa.
Duk da karatun zamani da ya yi har ya kai matsayin ƙwararren
likita a sashen Radiology bai sa ya zubar da wannan tunani nasa akan karatun
Allo ba.
Sai gashi sannu a hankali haƙarsa ta cimma ruwa domin kuwa zamansa a
Majalisar Wakilai ta Tarayya daga shekarar 2019 zuwa 2023 ya bashi damar yin
tsayin gwamin Jaki sai da ya ga ƙudurinsa na ƙirƙiro Hukumar Kula da
Almajirai da bai wa Yaran da basu shiga Makarantu damar samun Ilmi (National
Commission for Almajiri&Out-of-School Children Education, NCAOOSCE) ya
cimma gaci.
Alhamdulillahi! Domin yabawa wannan namijin ƙoƙari da
kuma ƙarawa
masu tunani irin nasa ƙwarin gwiwa, Mai Martaba Sarkin Daura na 60, Alhaji Dr. Umar
Farouk Umar da yan majalisarsa suka damk'a masa wannan sarauta ta Barden
Tsangayun Hausa.
Bahaushe ya na cewa "Ruwa baya tsami banza". Malam
Muhammadu Agali da ya fito daga Ƙabilar Buzaye dake Jamhuriyar Nijar ta
yanzu ne ya shigo yankin Kogin Rima ya na sana'arsa ta Wanzanci har ya zauna a
yankin Rikina daidai lokacin da Sarkin Sullub'awa watau Arɗo Malam Manuri da jama'arsa
ke kai komo wajen taimakawa masu jihadin jaddada addinin musulunci na Daular
Usmaniya ƙarƙashin
jagorancin Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi,
kuma ya bayar da tasa gudummawa.
Malam Muhammadu Agali
ne ya haifi Malam Abubakar Akawal, Malam Abubakar Akawal ne ya haifi Malam
Muhammadu Barmo wanda ya zauna a wani Ƙauye da ake kira Heterete a cikin
gundumar Shuni, Ƙaramar Hukumar Mulkin Dange/Shuni, Jihar Sakkwato inda ya auri
wata mata da ake kira A'isha /Indo da mahaifanta suka fito daga Talata Mafara
ta Jihar Zamfara ta yau. Sune suka haifi Alhaji Usman /Shehu Kakale Shuni a
shekarar 1929 a wannan Ƙauyen (Heterete).
Alhaji Usman /Shehu Kakale Shuni ne ya haifi Hon. Dr. Usman
Balarabe Shehu Kakale Shuni a Ƙofar Taramniya a Birnin Sakkwato, ranar
8/11/1974.
Hajiya Halimatu/Inna Malama 'yar Malam Ubandawaki Umaru ce,
Malam Ubandawaki Umaru ɗan
Sarkin Tambuwal Malam Haruna ne, Sarkin Tambuwal Malam Haruna ɗan Sarkin Tambuwal Malam
Umaru ne, Sarkin Tambuwal Malam Umaru ɗan
Sarkin Tambuwal Malam Muhammadu Buhari ne, Sarkin Tambuwal Malam Muhammadu
Buhari ɗan Mujaddadi
Shehu Usman Ɗanfodio
tagammadahullah birahamatihi ne, wannan baiwar Allah ita ce Mahaifiyar Hon. Dr.
Usman Balarabe Shehu Kakale Shuni, Barden Tsangayun Hausa. Haƙiƙa Ruwa
bai yi tsami a banza ba.
Allah ya sakawa Mai Martaba Magajin Bawo, Sarkin Daura
Alhaji Dr. Umar Farouk Umar da mafificin alherinsa akan aza wannan ƙwarya
daidai gurbinta.
Allah ya ja zamanin Mai girma Barden Tsangayun Hausa,
Honorable Dr. Usman Balarabe Shehu Kakale Shuni, amin.
Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya
08149388452, 08027484815.
birninbagaji4040@gmail.com
Alhamis, 25/07/2024.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.