Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan Maniyyi Ya Zuba A Tufa Najasa Ne?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam ya karatu ya dalibai, Malam tambaya ce idan Maniyyi ko maziyyi ya zuba atufa ko jiki najasa ne ko ba najasa bane? Allah Kara ilimi.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Farko dai akwai saɓanin malamai game da hukuncin shin maniyyi najasa ne, ko ba najasa bane?

Kuma saɓanin ya samo asali ne daga fahimtar da malamai suka yiwa wasu hadisai guda biyu waɗanda aka riwaitosu duk daga Nana A'ishah (rta).

Tace : "Na kasance ina wanke janabah (wato maniyyi) daga tufafin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam sai ya fita zuwa sallah alhali gurbin ruwan yana jikin tufafinsa".

Da kuma hadisin da tace "Na kasance ina kankareshi (da farcena) daga tufafin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam kuma yayi sallah acikinsa".

Duk wadannan hadisan akwaisu cikin Bukhariy da Muslim da wasu litattafan.

Maluman Mazhabin Shafi'iyyah da Hanbaliyyah da kuma Sufyanuth Thauriy da Abu Thaur sunce maniyyi ba najasa bane. Hujjarsu ita ce Nana A'ishah tace tana kankareshi daga tufafin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Kuma da ace maniyyi ba tsatsarka bane, da kankarewa Kaɗai bazata isar ba. Kuma wannan ita ce fatawar manyan Sahabban Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam irin su Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib, da Abdullahi bn Abbas, da Abdullahi bn Umar, da Sa'adu bn Abi Waqqas da ita kanta Nana A'ishah (Allah ya yarda dasu baki ɗaya).

Imam Malik da Imam Abu Hanifah (Allah ya jikansu) sun ce maniyyi najasa ne. Hujjarsu ita ce hadisin da Nana A'ishah (ra) tace tana wankeshi daga tufafin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Kuma sun ce saboda yana fita ne daga mafitar fitsari. Kuma tunda fitsari najasa ne, don haka shima najasa ne.

Amma gaskiya waccen fatawar ta farko (fatawar Shafi'iyyah da Hanbaliyyah) tafi Qarfin hujjah mai karfi tare da cewa ta samu tushe daga sahabbai (Allah ya yarda dasu).

Amma babu saɓani cikin wajibcin yin wanka saboda fitarsa ta hanyar mafarki ko a farke ta dalilin jima'i ko motsuwar sha'awa ko shafa, ko kallo.

Shi kuwa maziyyi, dukkan maluman fiqhu sunyi ittifaki akan cewa najasa ne shi. Kuma idan ya taɓa tufafi wajibi ne sai an wankeshi.

Don karin bayani aduba littafin Ta'aseesul Ahkam na Shaikh Ahmad bn Yahya Annajmiy (juzu'i na daya shafi na 86 zuwa na 87)da kuma shafi na 62 - 63.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

HUKUNCIN SUTURAN DA MANIYYI YA TAƁA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

malan da fatan kana lafiya tambayace dani tambayata itace ya masayin suturan da manniyi yataba wanne irin wanke akeyi mata ruwa ba sabulu ko ba omo?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To ɗan uwa shi kansa maniyyin Malamai sun samu saɓani dangane da hukuncinsa ma'ana Shin maniyyin Najasane ko ba najasa bane?

Wasu malaman sun tafi akan cewa naniyyi najasa ne, inda kuma Wani ɓangare na malamai sukace maniyyi ba najasa bane, amma dai fahimtar da muke kai ita ce fahimtar malaman da suka tafi akan cewa Maniyyi ba najasa bane.

sabida haka idan miniyyi ya taɓa tufafi ya halatta ayi sallah da tufafin mustahabbi ne a wankeshi Amma dai ba najasa bane, Saidai kuma fitarsa ta hanyar Jima'i, Mafarkin suduwa ko wasa yana wajabta wanka. Sabida haka idan mutum ya wanke maniyyin to shine yafi, sai ba dole ne sai an sanya sabulu ko omo yayin wankewar ba idan an wanke da ruwa ya wadatar

Domin neman karin bayani dangane da hukuncin maniyyin Sai a duba Al'mugni na Ibn qudama (1/736)

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

SHIN MANIYYI YANA FITO WA MACE

TAMBAYA (184)

Mace BUDURWA maniyyi yana fito mata?

AMSA

Tambaya Mai muhimmanci

Kamar yanda Namiji yake fitarda: Maniyyi, Mazy da Wady haka itama mace take fitarda wadannan abubuwan guda 3

Indai Mazy da Wady suka fita daga gabanta to wanke gabannata zatayi kawai

(Fatawa al-Lajnah al-Daa’imah.)

(Fatawa al-‘Ulamaa’ fi ‘Ushrat al-Nisaa’, p. 37)

Shaikh Saleh al-Fawzaan yace: Idan wani abu ya fito daga gaban mace silar kissing da Mijinta zaiyi Mata ko Kuma Wasa da ita to anan bazatayi wanka ba, a inda zatayi wanka shine idan maniyyi ya fito

(Fatawa al-Mar’ah al-Muslimah, 1/222)

Shan maniyyi ba Haramun bane ba saidai abin qyama ne laakarida yanayinsa Kamar majina yake Kuma an qyamaci Shan majina saboda ko yarone kikaga Yana Shan majina zakice Kai kaidai kam ka fiya qazanta

Ballantana Kuma Miji ya Sha na Matarsa dukda dai cewar Shan sa din ba Haramun baneba a Shari'ah saboda ba Najasa baneba

Ibn Qudamah yace: Shan Najasa Haramun ne

(al-Mughnee': vol. 1, p. 378)

Wallahu taala aalam

Muna muku tallar sabuwar makaranta Online mai suna: "MU'AMALAR AURATAYYA A MUSULUNCI". Wanda yake da ra'ayin shiga yayi magana ta Private hukumar makaranta zata turo masa tsare - tsare da dokokin shiga

(WhatsApp: 07035387476)

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments