Hukuncin Yin Kasuwanci Da Kuɗin Da Aka Ba Wa Mutum Ajiya

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Mene ne hukuncin Mutumin da akabashi ajiyar kuɗi sai yake kasuwanci da kuɗin yana samun ribah?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Asalidai a Shari'ance idan akabawa Mutum ajiyar wasu Kuɗaɗe kokuma kadarori to wajibine akansa yakiyaye wannan amanar da akabashi, Sannan kuma ba zai yi amfani da'itaba dole sai in yanemi izinin mai ita, to amma idan har Mutum yayi amfani da Kuɗin ajiya yana Kasuwanci dasu yana samun riba, anan sai Malamai sukayi Saɓani dangane da hukuncin wannan ribar da'aka samu, Mazhabin Malikiyya da Shafi'iyya sunaganin cewa wannan riba da'akasamu ta shi Mutumin da yajuwa Kuɗin ne wato wanda akabawa ajiyar Kuɗin kenan, sukace wanda yabada ajiya za'amayar masa da asalin Kuɗinsane da yabayar a ajjemasa, amma wanda akabawa ajiyar Kuɗin shine zaidauki abinda yakaru aciki, domin shine yayi wahala wajen yin kasuwanci da'ita, duk dacewa yayi amfani da Kuɗaɗenne ta hanyar ta'addanci batare da izinin maisuba.

    Hujjarsu anan itace, tunda haryayi ta'addanci nayin amfani da Kuɗaɗen ajiya wanda kuma inda waɗannan Kuɗaɗen zasu salwanta to wajibine akansa sai yabiya, danhaka kenan tunda ramuwa tana kansa idan akayi asara to hakanan kuma idan akasamu riba shine zairiketa, kamar yadda Ƙa'idarnan ta Fiƙ-hiyya datake cewa

    (الخراج بالضمان)

    Saidai mazhabin Hanabila suntafine akancewa wannan riba da'akasamu ta mai asalin wanda yakawo ajiyar Kuɗinsane domin da Kuɗaɗensa ne akasamu wannan riba danhaka tasace, amma Mazhabin Hanafiyya suntafine akan cewa da wanda yabada ajiyar da wanda akabawa ajiyar dukkaninsu babu wanda zaidauki wannan riba ta Kuɗi da'akasamu, danhaka saidai ayi Sadaƙa da Kuɗin kawai, Saidai wasu daga cikin Malamai sukace a'a, kawai za'araba wannan ribar Kuɗaɗen da akasamune gida biyune sai suraba atsakaninsu, kowa yadauki rabi.

    Danhaka kenan asali Haramunne amma akwai Malaman dasukace Makaruhine Mutum yayi amfani da dukiyar da'akabashi ajiya batareda izinin mai'itaba, to amma idan har ya aikata hakan batareda izinin mai'ita ɗinba meye hukuncinsa? Malamai sukace yayi ƙoƙari yanemi afuwa da ya fiya daga wajen mai asalin dukiyar shikenan magana taƙare.

    шαʟʟαнυ- тα'αʟα α'αʟαмυ

    Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα

    "مغني المحتاج" (3/363)

    "المغني لإبن قدامة" (5/159)

    AMSAWA

               Mυѕтαρнα Uѕмαи

                  08032531505

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.