Ticker

6/recent/ticker-posts

A Sanadiyar Rashin Samun Kulawa Daga Matarsa, Ta Jefa Shi Cikin Aikata Istimna'i

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Da fatan Malam yana lafiya. Allah Ya taimaka, Ya kara wa Malam lafiya da imani. Tambaya ce ga Malam. Mene ne hukunci matar da bata kula mijinta ta hanyan mu'amalar aure. A sanadiyar rashin samun kulawa daga matar tashi har tayi sanadiyar jefa shi cikin aikata istimna'i? Mene ne hukuncin su biyu a Musulunci? Allah Ya saka wa Malam da mafificin alkhairi.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaykumussalam. Ya tabbata cikin hadisin bukhari da muslim hadisin Abu-huraura cewa duk matar da mijinta ya kirata shimfidar sa sai taki har mijin ya kwana cikin fushi da ita to mala'iku suna la'antar ta...

Shi kuma ta ɓangare sa abinda ya aikata ya wuce iyakar da Allah yayi cikin fadar Allah cikin Suratul-Mu'uminoon

وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ ٥۝ إِلَّا عَلَىٰ أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ ٦۝ فَمَنِ ابْتَغَىٰ وَرَاءَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْعَادُونَ ٧۝

Bayin Allah nagari Sune waɗanda dangane da farjinsu suke kiyayeshi. Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka (kuyanginsu) to lalle sũ bã waɗanda ake zargi ba ne. Sabõda haka wanda ya nemi abin da ke bãyan wancan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetarewar haddi. (Suratul Mũminun 5-7)

Waɗannan nassoshin biyu na nuna dukkan su sun aikata lafi sai a tuba a nemi gafarar Allah, ita matar ta kara da neman gafarar mijin ta kuma kar ta sake, domin hakan na iya jefa shi cikin haɗari kuma yayi sanadiyar halakar sa da ita baki ɗaya bugu da kari aure na iya mutuwa ta sanadiyyar rashin saduwa.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments