𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Don Allah Malam ina da tambaya, ni ce nake jinin haila, kwana biyar na saba yi, to amma wannan karon kwana tara yayi min, bayan nayi wanka da kwana uku sai kuma wani ruwan ƙasa tare da jini kaɗan yake fito min wadda har yanzu bai daina ba, shine nake tambaya akan hukuncin wannan rikitaccen lamarin nawa. Nagode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikum assalam. To Malama ana iya samun ragi
ko ƙari a jinin haila, don haka ƙarin ba zai cutar ba,
saboda shi ma haila ne, mutuƙar bai wuce iyaka ba,
wanda a lokacin zai zama jinin istihala, amma ruwan ƙasar da kike gani to mutuƙar bayan kin kammala
haila yazo, to ba ya cikinta, ba zai hana Azumi ba da Sallah, domin shi ne ake
kira kudra, ita kuma kudra idan tazo bayan jinin haila, to ba ta cikinsa, kamar
yadda Hadisin Ummu-Addiyya yayi nuni, inda take cewa: "Mun kasance ba ma ƙirga kudra da sufra bayan tsarki a cikin haila", Bukhari 1/426.
Allah ne mafi sani.
𝑨𝒎𝒔𝒂 𝒅𝒂𝒈𝒂 𝑫𝒓. 𝑱𝒂𝒎𝒊𝒍𝒖 𝒀𝒖𝒔𝒖𝒇 𝒁𝒂𝒓𝒆𝒘𝒂
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.