Fitar Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau Daga Anka Zuwa Sabon Wurin Da Ya Kafa, Watau " Sabon Birnin Banaga
Akwai magana /maganganu guda biyu game da wannan fitar ta Banaga Ɗan Bature Ɗan Danau daga Anka da suka fi shahara a Tarihin samar da Anka a matsayin hedikwatar ƙarshe ta Zamfarawan da suka zauni Dutci/Dutsi da Birnin Zamfara da Kiyawa da Banga da Ƙuryam Madaro da Sabongarin Damri tsakanin 1300 zuwa 1815/1824.
Ta farko ita ce wacce/wadda Dr. Kurt Krieger ya tafi akai
cewa Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo (1815-1824) ne ya yi wa Banaga Ɗan Bature Ɗan
Danau sammu da aka haɗa
a kab'akin Tuwo aka ɗauka
daga Sabongarin Damri zuwa Anka. Har Bawan Sarkin Zamfara Ɗan Baƙo
wanda ya ɗauki sammun
zuwa Anka ya ambata a cikin aikinsa "Tarihin Zamfara" (wanda akasari
daga rubutun magabata ne da suka mulki Daular Zamfara da aka rubuta a cikin
Ajami da ya karɓe daga
Fadar Sarkin Zamfaran Anka a cikin 1940s/50s) ya tafi dashi Ƙasar
su, Jamus. A shekarar 1959 kuma ya wallafa wannan Littafi nasa mai suna
"Tarihin Zamfara" wanda kusan shi ne madogara ta biyu akan Tarihin
Daular Zamfara bancin Infak'ul Maisur na Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio
tagammadahullah birahamatihi.
A ciki ya bayyana cewa bayan wannan Bawa ya girke wannan
kab'akin tuwo a Ƙofar gidan Banaga Ɗan Bature a Anka( a gidan ne Sarakunan
Zamfara tun daga Sarki Ɗan Baƙo, 1815-1824 ya zuwa yau suke sarauta) da ya fito Sallar Asuba
ya yi kicib'is da shi sai sammun ya shige shi.
Da hantsi ya tara hakimansa da manyan mutanen garin ya sanar
dasu cewa zasu tashi daga Anka ba tare da ɓata
lokaci ba, ya yanke shawara umurni ne ya ke basu. Saboda haka a ranar suka
kimtsa kayansu, su ka fice daga garin, suka tsallaka Kogin Zamfara dake Kudu da
Anka ya sake kafa sabon zama da ya kira "Sabon Birnin Banaga" inda na
ambata a cikin rubutun da ya gabata cewa anan ne Allah ya yi masa wafati. Na je
garin a cikin farko farkon shekarar 2011.
Magana ta biyu kuma akwai bayanin da ke nuna cewa umurnin
Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan
Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ne Sarakunan Zamfara na
wancan lokaci da ke zaune a Sabongarin Damri su ka bi wajen fitar da shi daga
Anka da zummar su zauni wurin a matsayin sabuwar hedikwatarsu duk da yake ba a bayyana
ko ta wace hanya suka bi ba wajen aiwatar da wannan umurni ba, ban kuma ci karo
da wannan bayani a rubuce ba. Allahu Wa'alam!!!
Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara,
Nijeriya
08149388452, 08027484815.
birninbagaji4040@gmail.com
Asabar, 29/06/2024
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.