TAMBAYA (143)❓
Wai naji ance ba kyau mutum ya kashe cinnaka,
kenan ko cizo nawa zai dalla min saidai na kalle shi yayi tafiyarsa ?
✍️ AMSA A TAQAICE❗
Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya hana a
kashe dabbobi kala 4: qwari, zuma, hudhud (tsuntsu) da Suradi (shaho)"
(Musnad Imam Ahmad: 3066, Abu Dawud 5267 Shaikh
Shu'aib al-Arna'ut malamin hadisi ya sahihantashi)
A likitance kuma an gano cewar yana maganin cutar
obesity wato cutar matsananciyar qiba da dai sauransu
Alhamdulillah
A yanda cizon macen cinnaka yake sa wasu kuka su
kuma wasu kidimewa suke suyi ta sosa wajen. To ammanfa abin al'ajabin shine:
wannan cizon da take magani yake sakawa mutum bawai cuta ba, kamar dai yanda
likita zai tsikara maka allura mai dauke da Chloroquine don magance cutar
Malaria to haka shima sinadarin da macen cinnaka take zuba maka wanda ake
kiransa da "ionic saliva" yake aiki a matsayin sedative a cikin jikin
Dan Adam
Yayin da sahabbai (Radiyallahu anhum) suka zamo
sami'ina wa'ada'ana ma'ana sun ji hanin kuma sunyi biyayya bazasu kashe wadannan
halittu ba - bari mu ji abinda Annabin Rahama (Sallallahu alaihi wasallam) ya
hango wanda sai kwanannan likitoci suka gano
1) Cizon macen cinnaka yana maganin qiba wadda ake
samu silar taruwar fats wato kitse. Yayin da ta cije ka tana saka maka
sinadarin ionic saliva ne shi kuma wannan sinadarin yana kashe halittun da suke
a cikin fats ne wadanda suke zama silar da mutum yake yin qiba
Misali: idan ta cije ka a hannu to nan take
sinadarin zai qona halittun da suke a cikin fats na wannan hannun 99%, hakama
idan a kafa ne ko a wani sashe na jiki. Kuma ko kasan cewar ba hakanan take
cizon mutum ba - saboda nasha dora cinnaka a hannuna bazaka ji cizon ba har sai
ka yi yunqurin kashe sa, shi kuma domin neman tsira sai ya maida martani wato
cizo. Allahu Akbar
2) Cizon cinnaka yana qarawa mutum adadin yawan
red blood cells wato jajayen qananan halittun da suke a cikin jini wanda hakan
ke qarawa mutum energy wato kuzari - misali: idan aka ce tashi ka rakani kanti
zaka iya cewa gaskiya na gaji amman yayin da cinnaka ya manna maka bazaka san
lokacin da zaka miqe zumbur ba. Meyasa ? Saboda ka samu energy silar halittar
red blood cells da al-Khaliqu Allah Azzawajallah yayi a lokacin. Subhanallah
3) Cizon cinnaka yana maganin cutar fata da ake da
"cirrhosis of the skin"
4) Haka Kuma yana kunna sinadaran neurons da suke
a qwaqwala daga sensory signals inda cizon ya afku zuwa sensory cells dake
qasan qwaqwala. Subhanallah
Dogaro da wadannan hujjojin da na zayyano a
addinance da kuma a kimiyyance kuskure ne kashe cinnaka. Amman dangane da qwari
irinsu kunama wannan ba laifi bane don an kashe ta saboda dafinta yana iya
kisa. Haka kuma baa son a kashe tururuwa saboda ita musamman ma aka saukar da
Sura mai sunanta: Suratu Nahl inda Allah Azzawajallah yace
( حَتَّىٰ إِذَا أَتَوْا عَلَىٰ وَادِ النَّمْلِ قَالَتْ
نَمْلَةٌ يَا أَيُّهَا النَّمْلُ ادْخُلُوا مَسَاكِنَكُمْ لَا يَحْطِمَنَّكُمْ سُلَيْمَانُ
وَجُنُودُهُ وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ )
النمل (18) An-Naml
Har a lõkacin da suka je a kan rãfin turũruwa wata
turũruwa ta ce, "Yã kũ jama'ar turũruwa! Ku shiga gidãjenku, kada Sulaimãn
da rundunõninsa su kakkarya ku, alhãli kuwa sũ, ba su sani ba."
Haka kuma tsuntsun huda - huda da yazo a hadisin,
shima Allah ya ambace a Qur'ani
( وَتَفَقَّدَ الطَّيْرَ فَقَالَ مَا لِيَ لَا أَرَى الْهُدْهُدَ
أَمْ كَانَ مِنَ الْغَائِبِينَ )
النمل (20) An-Naml
Kuma ya binciki tsuntsãye, sai ya ce: "Me ya
kãre ni bã ni ganin hudhudu, kõ ya kasance daga mãsu fakuwa ne?"
Da kuma zuma wadda itama Surah ce guda da aka
anbace ta da: Suratu Nahl;
( وَأَوْحَىٰ رَبُّكَ إِلَى النَّحْلِ أَنِ اتَّخِذِي مِنَ
الْجِبَالِ بُيُوتًا وَمِنَ الشَّجَرِ وَمِمَّا يَعْرِشُونَ )
النحل (68) An-Nahl
Ubangijinka Yã yi wahayi zuwa ga ƙudan zuma cẽwa: "Ki riƙi gidãje daga duwãtsu, kuma daga itãce, kuma daga abin da suke
ginãwa."
Do haka sai mu kiyaye yunqurin kashe wadannan
halittun indai ba da wani dalili qwaqqwara na shari'a ba
Kuma idan mutum yayi haquri da cizon cinnakan to
zai samu riba biyu
Na farko zaka samu waraka daga cutar obesity wato
qiba idan kana da ita
Na biyu kuma idan kayi haquri to zaka samu lada da
kankarar zunubi kamar yanda hadisi ya tabbata a cikin Sahihul Bukhari cewar
Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya ce: ina mamakin al'amarin mumini, idan
sharri ya same shi sai ya gode Allah haka idan alkhairi ya riske shi
Wallahu taala aalam
Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu
anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.