Ticker

6/recent/ticker-posts

Karatun Diploma Kyauta Daga "Zad Academy" Makkah

TAMBAYA (149)

Assalamu alaykum Brk d sfy

Tambaya ta ba akan hukuncin addini bane Ina tambaya akan hanyar neman ilimi

Akwai makaranta wadda kake gudanarwa ko wanin ka a online karatun addini ko nazamani ko duka ?

Don Allah idan akwai aimin bayani sai a sakani

Ina matuƙar ƙaunar ilimin amma yanayin rayuwa yasa banida wadataccen lokacin da zanje makaranta in ɗauki karatu amma Anan ina fatan inshallah asamu mafita ngd

AMSA

Waalaikumus salam warahmatullahi wabarakatuh.

Alhamdulillah

Bazaa rasa ba. Da akwai wata babbar dama ta karatu a makarantar ZAD ACADEMY dake kasar MAKKAH a karon farko sun fara free registration ga duk wanda yake jin turanci Kuma karatun online ne. Ni kaina nayi registration da su.

Diploma program ne tsawon shekaru 2 wato semesters 4. Nan da ranar talata 1 ga watan August 2024 kenan zasu rufe registration din sannan zaa fara lecture ranar 25 ga August 2024. Ana darussan: Qur'ani, Hadith, Aqidah, Tarbiya Islamiyah, Tafsir, Arabic, Fiqh da Kuma Seerah sannan Kuma zaka fita da CERTIFICATE na shaidar kammala DIPLOMA idan kana son ci gaba kofa a bude take

Da akwai shahararrun malaman Ahlus Sunnah da duniya ta san dasu irinsu: Shaikh Muhammad Salah. Wanda a shekarar 2018 mun taba haduwa dashi a wani Islamic conference da aka gayyaceni anan The Afficient, Nassarawa GRA dake jihar Kano. Dasu Shaikh Assim alhakim da har mukai exchanging contact dasu Wanda a wannan makaranta ta ZAD ACADEMY zai dinga koyar da SEERAH

Idan kana da raayi ga link din Kuma kyauta ne domin kuwa Larabawa ne suka dauki nauyin karatun kowanne dalibi sannan duk wanda ya fita da distinction wato kyakkyawan sakamako to zai samu kujerar MAKKAH da kyautar Laptop da babbar waya da dai sauransu. Ka yi registration din a Android dinka idan Kuma baka gane ba sai kaje masu Cafe su cike maka. Ga link din

Registration is now open for Zad Academy - English. To register and to learn more about the program, you can visit the following link: https://register.zad-academy.com/index.php?lang=en&utm_source=engar . Contribute to the reward and spread knowledge, and invite your friends to register.

Allah yabada saa. Please a sanar da wasu wadanda suke da interest akai

SANARWA

Usman Danliti Mato, (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.