Ticker

6/recent/ticker-posts

Yar Izala Za Ta Iya Auren Dan Darika

TAMBAYA (108)

Assalamualaikum. MLM fatan alkhairi agareku

Dan Allah tambaya gareni akan shin mace yar izala zata iya auren namiji dan dariqa pls

AMSA

Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuh

Alhamdulillah

Anan kamata yayi ayi masa abinda malamai suke cewa: "Izalatush shubha, wa'iqamatul hujja" ma'ana "a kauda masa shubuha, a tsayar masa da hujja"

Ya zamana a kawar masa da shubuhohin da suke a cikin dariqa sannan a kafa masa hujja da aqidar sunnah, idan yace shi ba ruwan sa da sunnah, shi dai a barshi da dariqar sa to kinga kenan zata auri mara addini, domin kuwa dariqa ba addini bace ba

Idan har tana tsoron zai iya maida ita yar dariqa ya koya mata bidi'o'i to bai halatta ta auri dan bidi'ah ba kam. Ta haqura ta auro wanda ya ke koyi da sunnah bisa minhajin Salaf (magabatana farko wato sahabbai, tabi'ai da tabi'ut tabi'un)

Muna roqon Allah ya rabamu da bidi'a ya tabbatar damu akan musulunci bisa sunnar Annabi SAW kan fahimtar Salaf (Magabatan farko)

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments