Ticker

6/recent/ticker-posts

Muhallin Magani A Adabin Bakan Bahaushe

Cite this article as: Abdullahi, I. S. S. (2012) “Muhallin Magani a Adabin Bakan Bahaushe” Ɗundaye Journal of Hausa Studies Vol. 1, No 4. Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto. December, Pages 187-198

Muhallin Magani A Adabin Bakan Bahaushe

Daga:

Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
E-mail: kontago2003@yahoo.co.uk
Lambar Waya: 0803 6153 050

Tsakure

Ƙokarin da aka yi na samar da wannan nazari yana da dangantaka da tunanin cewa a duk inda adabin Bahaushe yake akwai tasirin magani a ciki. Wannan fahimta ta tuzgo ne bisa la’akari da cewa, rayuwa ba ta gudana ba tare da magani ba. Don haka dole ne adabin ya ɗauko hoton magani muddin yana son ya amsa sunansa. Wannan nazari ya yi ƘoƘarin tabbatar da hakan ta hanyar duban ɓangarorin adabin baka daban-daban.

1.0 GARATARWA

Masana Hausa sun yi ittifaƘi da cewa, kalmar Adabi wadda ta samu ga Hausawa bayan haɗuwar su da Larabawa tana wakiltar hoton rayuwar al’uma ne. Wato duk wani abu da za a yi bayaninsa wanda kai tsaye ya shafi rayuwar wannan al’umar to shi ne masanan suka kira adabi. Duk rayuwar da za a ɗauki hoton ta, dole ne ginshiƘan da ke ɗauke da al’umar su fito fili a gan su. Hasashen da ake ƘoƘarin tabbatarwa a wannan nazari shi ne, magani yana ɗaya daga cikin ginshiƘan da ke ɗauke da nauyin kowace al’uma ba ma ta Hausawa kaɗai ba. Wato idan har za a dubi rayuwar kowace al’umma to dole ne sai magani ya fito. Mutanen da a al’adance suke da fasahar fito da wannan adabin ba za su iya kawo dalilin da lamarin magani yake taka rawa a fasahohin nasu ba. Wannan ba abin mamaki ba ne domin abu ne mawuyaci mahauci ya gaya maka dalilin da ya sa ake samun tsoka da jini. A wannan nazarin, za a yi ƘoƘarin tabbatar da hasashen na dangantakar da ke tsakanin tsoka da jini ta duban alaƘar adabin bakan Bahaushe da magani. Ana ɗammahar wannan nazarin ya tabbatar muna da tunanin rayuwar Hausawa ba ta kammaluwa ba tare da magani ba. Hanya mafi sauƘi da za a yi amfani da ita ita ce ɗora adabin baka a matsayin mizanin awo domin shi ake tunanin ya ɗauko hoton rayuwar al’uma tul fil-azal.

2.0 ADABI A TUNANIN MASANA HAUSA

Kawowa yanzu, babu wasu saɓanin ra’ayoyi a tsakanin masana adabin Hausa a kan rabuwarsa zuwa kashi biyu, wato na gargajiya ko na baka da adabin zamani ko rubutacce.[1] Haka kuma Ƙumshiyar adabin zamani ko rubutacce (waƘa, zube da wasan kwaikwayo) bai sami bambancin ra’ayi daga malaman ba. To amma tunanin masanan ya faɗaɗa Ƙwarai dangane da kayan cikin adabin bakan Bahaushe. Wannan bai zama abin mamaki ba da yake adabi ne da tun farko aka samo da baki, kuma ake bayar da shi a baka. Misali, Ɗangambo (1984) ya nuna cewa adabin bakan Bahaushe ya Ƙunshi manyan rassa kamar tatsuniya, da waƘoƘi da kayan kiɗa, da tumasanci, da sana’o’in gargajiya, da bukukuwa, da camfe-camfe, da tarbiyya da dai sauransu. Shi kuwa Gusau (1984) a dunƘule ya kasa rukunan adabin zuwa gida uku, wato zube da maganganun azanci, da kuma raha. To haka dai ake samun saɓanin fahimta a kan abubuwan da wannan reshe na adabi ya Ƙunsa.

 

3.0          MAGANI DA RASSANSA A GARGAJIYAR BAHAUSHE

Idan Bahaushe ya ambaci kalmar magani, yana nufin duk wata hanya da ɗan Adam zai bi wajen warkar da cuta ko rauni ko neman kariya daga cutar. Wasu kuma sukan faɗaɗa wannan ma’ana da amfani da wata hanya ta musamman wajen neman kariya daga sharrin abokan hamayya ko kuma neman wata daraja ko ɗaukaka ko buwaya a zamantakewarsu da mutane. Ta la’akari da waɗannan bukatoci da suke sa a nemi magani, za a fahimci cewa, abu ne mawuyaci a ce ga ranar da Hausawa suka fara mu’amala da magani. To sai dai za a aminta da cewa, ba ma Hausawa kaɗai ba, babu al’umar da ba ta da bukatar magani. A al’adance, bukatu ko matsaloli suke tasowa, a yi tunanin kawar da su, sai hanyar da aka bi ta kawar da wannan matsala ko bukata ta zama magani. Sannu a hankali har wannan hanyar ta sami karɓuwa bayan mutane da dama sun jarraba sun sami biyan bukata. Rarrabuwar waɗannan bukatoci na mutane da bambancin abin da ake sarrafawa don yin magani, da kuma dabarun da ake yi wajen sarrafa magani don samun biyan bukata su suka ja hankalin masana maganin gargajiya na Hausawa wajen karkasa shi zuwa rassa daban-daban.

3.1 RASSAN MAGANI TA FUSKAR BUKATUN MUTANE

Manazarta al’adun Hausawa, musamman ma waɗanda suka mayar da hankali ga magungunan gargajiya, sun yi la’akari da bukatocin mutane na magani wajen karkasa magungunan Hausawa.

(i)        Magungunan warkarwa, waɗanda suka Ƙunshi duk wani magani da ake amfani da shi don warkar da cuta ta zahiri ko ta cikin jiki ko rauni da dai makamantan su.

(ii) Magungunan kariya, su kuma sun Ƙunshi magungunan da Hausawa suke sarrafawa ko amfani da su don kare kai daga cuta ko cutarwar mutum ko aljani ko wata dabba ko Ƙwaro.

(iii)   Magungunan cutarwa, akan tanade su ne da tunanin cutar da wasu mutane bisa wasu dalilai na Ƙiyayya ko hukunci ko ramuwar gayya ko gyara wa wani zama.

(iv) Magungunan biyan bukatocin rayuwa, sun Ƙunshi duk wani magani da zai Ƙara wa rayuwa kwarjini da ado da jin daɗi. Magunguna ne da ake amfani da su domin su samar wa zuciya abubuwan da take so waɗanda ba ta iya samar wa kanta su kai tsaye.

3.2          RASSAN MAGANI TA FUSKAR ABIN DA AKE SARRAFAWA

ƘoƘarin gano magugunan da Hausawa suke mu’amala da su a gargajiyance shi ya ba manazarta damar karkasa su ta la’akari da ainihin abin da ake sarrafawa wajen aiwatar da maganin. A al’adance, an fi amfani da abubuwan da al’uma ta samu a muhallin da take zaune a matsayin magani. Tunanin wannan ya sa aka rarrabe magungunan gargajiya na Hausawa zuwa ga dangoginsu. Akwai magungunan da aka samo daga itace ko tsirrai. Wasu kuma daga dabbobi da Ƙwari, ko sassan jikin mutane ko wani abu da ya fito daga jikin nasu kamar Ƙumba da gumi da dai sauran su. Haka kuma akwai magungunan da suka shafi ruwa da Ƙasa. Wasu kuma addu’o’i ne da surkulle ko karance-karance da yanka ko zubar da jini da dai sauran su.

3.3          RASSAN MAGANI TA FUSKAR YADDA AKE SARRAFA SU

Kowane irin magani da nau’insa. Wannan ya kasance haka ne da yake bukatocin mutane ba ɗaya ba, abin da ya sa hanyoyin sarrafa magungunan suka bambanta. Wannan bambancin shi ya ba da damar karkasa magunguna zuwa rukunai daban-daban. Daga cikin waɗannan kashe-kashe akwai magungunan gargajiyar da ake sha, akwai na shafawa a jiki. Wasu a shaƘa a hanci, wasu a sa cikin wuta a turara, wasu kuma a dafa su a yi suraci da turirin. Wasu magungunan binnewa ake yi a cikin Ƙasa, a yayin da ake ɓoye wasu a cikin wani abu a doron Ƙasa da sauran dabaru na sarrafa magani.

4.0          MAGANI A ADABIN BAKAN BAHAUSHE

Wannan fasali zai mayar da hankali ne wajen zaƘulo irin rawar da magani ke takawa wajen ginuwar adabin bakan Bahaushe. A ƘoƘarin yi wa nazarin adalci, za a ɗora magani a rassan bishiyar li’irabin Gusau (1984) na rabe-raben adabin baka.

4.1 ZUBE

Rukunin zube a adabin bakan Bahaushe rukuni ne da ya Ƙunshi duk wani labari da za a bayar da baki. Misalan zube na baka sun haɗa da tatsuniya da hikaya da Ƙissa da labarai da tarihi da barkwanci da almara. Ga misalin yadda lamarin magani yake watayawa a biyu daga cikin su.

4.1.1 Tatsuniya

Tatsuniya a taƘaice, Ƙagaggen labari ne da al’adar Hausawa ta tanada domin ba da nishaɗi da kuma cusa tarbiyya ga yara (Yahya 1994). Da yawa daga cikin tatsuniyoyin Hausawa suna ɗauke da lamarin magani ta hanyar nuna cewa, ba lafiya an nemi magani, ko kuma wata bukata ta taso wadda ba makawa sai an nemi magani sannan a kawar da ita. Irin wannan bukata tana iya kasancewa wani ne ake son cutarwa ko wata kariya ce ake son yi daga cuta. Haka kuma yana iya kasancewa wata bukata ce ta rayuwa kawai ake son biya. Misali:

 A tatsuniyar “Maraya da saniya mai Magana,” kishiyar uwar Janniya ta yi ta zuwa wajen malamai da ‘yan bori tana karɓo maganin da za ta halaka shi ta mallake dukiyar da uwarsa ta bar masa. Duk maganin da aka yi amfani da shi don cuta masa sai saniyarsa mai magana ta gaya masa. Daga Ƙarshe, da magungunan suka Ƙare bai mutu ba, wani bokan ya ba da shawarar ta hura wuta a gaban gado don ya faɗa (a cikin bacci) ya mutu. Ƙarshen ta ‘ya’yanta su suka halaka. Wannan ya sa ta haukace ta bi uwa duniya.[2]

Wannan tatsuniyar ta ɗauko muna hoton yadda Ƙiyayya ke sa a yi ta faɗi-tashi wajen neman maganin cutar da wanda ba a so. To haka irin waɗannan misalai suke da ɗimbin yawa a tatsuniyoyin Hausawa.

4.1.2 Almara

Almara wani gajeren Ƙagaggen labari ne da ake bayarwa sannan a bukaci mutum ya faɗi amsa ko ya yi zaɓi tsakanin abubuwan da aka ambata. Galibi almara kan Ƙare da: “in kai ne yaya za ka yi?” Ko kuma, “cikin su wanne ya fi …...?” A irin wannan nau’i na zuben adabin baka, hoton magani yakan fito Ƙarara kamar dai yadda yake a rayuwa ta zahiri. Misali:

Wani magidanci ne mai mata biyu da ‘ya’ya da yawa ya kwanta rashin lafiya shekara da shekaru ciwo ya Ƙi ci, ya Ƙi cinyewa. An yi maganin duniyar nan amma Allah bai sa an dace ba. Uwargidansa ita aka bari da ɗawainiyar jinya. Ita ke kwashe kashi da fitsarin da yake yi. Ita ke ba shi magani, ta yi abinci da kula da yara, ta tsabtace gida da dai duk sauran aikace-aikacen gida. Ita kuma amaryar ita ke fita tana aikin Ƙarfi, ta sami kuɗi, ta sawo abinci a ci a gidan. A cikin wannan hali aka kasance shekara da shekaru. Ana nan sai wata rana aka sami wani mai maganin da ya ba da tabbacin yana da maganin wannan cutar. Sharaɗin kawai da ya bayar wanda ya nuna sai an yi shi maganin zai ci shi ne, sai majinyacin ya saki mata ɗaya daga cikin matan nan nasa. To idan kai ne wacce za ka saka?

A wannan almarar an kawo matsala, aka nuna magani ya kasa samuwa cikin sauƘi. Wannan da ma al’ada ce ta ciwo. Bahaushe ya yarda da cewa, magani sai dace. Bayan da aka sami maganin kuma, sai almarar ta Ƙara fito da wata al’adar bayar da magani a rayuwar Hausawa, wato kafa sharaɗin amfani da magani. HaƘiƘa wannan misali ya tabbatar muna da nason magani a adabin bakan Bahaushe.

4.2 MAGANGANUN AZANCI

Rukunin maganganun azanci a adabin bakan Bahaushe rukuni ne da yake da rassa da yawa wanda ke nuna irin hikima ko fasahar Hausawa wajen sarrafa harshen su a lokacin da suke magana. Wannan rukuni ya Ƙunshi fasahohi irin su: Salon magana da Karin magana da Habaici da Ba’a da BaƘar magana da Kirari da Take. Ga misalin yadda magani ke rausayawa a ɗaya daga cikin su.

4.2.1 Karin Magana

Karin magana kamar yadda magabata suka nuna, dabara ce ta dunƘule magana mai yawa a cikin zance ko ‘yan kalmomi kaɗan cikin hikima (Ɗangambo 1984:38). Fasaha ce da kan Ƙara wa zance armashi da bayyana halayen rayuwar Bahaushe na haƘiƘani. Hausawa sun yi fice ainun wajen amfani da Karin magana a zantuttukansu na yau da kullum. Kamar yadda sha’anin magani ya yi ta watayawa a tatsuniya da almara, haka ya sami ranar shanya a Karin magana. Fitowar magani a Karin maganar Hausawa yakan ɗauki fuska biyu:

(i)     Magani ya fito muraran a cikin Karin magana. Misali:

-          Da tsohuwar zuma ake magani.

-          Abin majinyaci na mai magani ne.

-          Da kura na da maganin zawo da ta yi wa kanta.

-          Idan magani ya Ƙi ci ba ya Ƙi zubarwa ba.

-          Idan ka ci maganin Ƙarfe, ka ci na Ƙarfi?

-          Magani a sha ka ba don yunwa ba.

-          Da haka ake yi a ce ba a sha? An sa wa majinyaci zuma a magani.

(ii)  Amfani da kalmar magani a Karin magana don nuna mafitar lamari ko samun sauƘin abin da ya yi tsananin ko warware wata matsala ko biyan wata bukata, da dai makamacin haka. Idan aka kwatanta matsayin kalmar ta magani a waɗannan Karin maganganu da ainihin ma’anar magani za a fahimci kai tsaye abu ɗaya ake magana a kai. Misali:

-          Haihuwa da yawa maganin annoba.

-          Maganin biri, Karen Maguzawa.

-          Gobara daga kogi maganinta Ubangiji.

-          Hadarin Ƙasa maganin mai kabido.

-          Idan so cuta ne, haƘuri magani ne.

-          Tuwon salla maganin mai haɗama.

-          Barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa.

-          Haukar ba ni, maganinta ungo.

-          Haske maganin duhu.

-          Hannu da yawa maganin Ƙazamar miya.

-          HaƘuri maganin zaman duniya.

-          Arha maganin mai wayo.

-          Waiwaye maganin mantuwa.

-          Gudu da mari ba ya maganin bauta.

4.3 RAHA

Raha wani babban reshe ne daga rassan adabin bakan Bahaushe. Shi ne reshen da yake ɗauke da duk nau’o’in rabe-raben waƘoƘin Hausawa kamar waƘoƘin aiki, da na gaɗa da na yara da waƘoƘin fada da na sha’awa da na maza da waƘoƘin jama’a da dai sauran su. A kowane ɗaya daga cikin waɗannan rukunai na waƘa akwai mutanen da suka yi fice, kuma akwai waƘoƘi masu armashi da ke fito da hoton rayuwar Hausawa musamman dangane da al’amurran da ke faruwa yau da kullum. ƘoƘarin da wannan fasali zai yi shi ne, fito da lamarin magani a wasu daga cikin rassa na waɗannan waƘoƘin don tabbatar da dugadugan wannan nazarin.

4.3.1 WaƘoƘin gaɗa

A al’adar Hausawa, yara ’yan mata sukan fita wasan gaɗa a dandali da dare. A irin wannan lokacin sukan yi wasannin da suke Ƙunshe da waƘoƘin waɗanda suke bayyana ra’ayoyi ko abin da suka hango, musamman a rayuwar aure ko ma rayuwar mace gaba ɗaya. Wasu daga cikin waɗannan woƘoƘin sukan fito da hoton magani. Ga misali:

“Ayye yaraye,

Ayye yaraye,

Ayye yaraye iye nanaye.

Ni ba kishiya,

Ni ba kishiya,

Ni ba kishiya nake tsoro ba.

Tai maka magani,

Tai maka magani,

Tai maka magani ka faɗa daji,

Hanyar gidanku ta ɓarɓace maka.”

Wannan misalin ya fito da wata al’ada ta Ƙiyayya da ke dasuwa a zukatan kishiyoyi na neman magungunan sharri a Ƙuntata wa juna. Su kansu ‘yamatan da ba su riga suka yi aure ba sun fahimci irin wannan rayuwa ta yadda har ya fito a waƘoƘin nasu.

4.3.2 WaƘoƘin Jama’a

WaƘoƘin Jama’a su ne waƘoƘin da makaɗan Hausa ke rera wa kowane irin mutum. Wannan ya Ƙunshi waƘoƘin attajirai da na mutanen da suka yi fice a wani sha’ani na duniya da dai duk wanda ya ja hankalinsu. Wasu daga cikin irin waɗannan waƘoƘi kai tsaye a kan magani aka rera su. Wasu kuwa tsarmin maganin kawai za a gani a cikin su. Misali, waƘar Malam Babba na Ƙofar Gabas ta Alhaji Mamman Shata, maganin ne turken ta.

“Malam Babba na Ƙofar Gabas,

Na ga dai yai shirin ya duba mani,

Ya dai haka, sai na ga nai yai haka,

Ya kimtsa sai na ga ya yo haka,

Ya sake shiryawa sai na ga ya yo haka,

Ya fid da uku ya ɗauke shida,

Sannan ya ɗauke huɗu ya ɗauke tara,

Na ga yai gum da ni yana al’ajab,

Ya ce mani, ‘kai makaɗi mai kiɗa,

Sha shagalinka cikin duniya,

Duk ba abin da zai tam maka,

Gidan tara kake, gani kuma nike,

Maganan kau duk haka tat tabbata,

A nan na yarda da Babba na Ƙofar gabas. ”

A wannan misalin, duk da yake Shata bai ambaci cewa, magani aka ba shi ya sha ko ya shafa ba, duban da aka yi masa, Malamai sun lissafa shi a matsayin wani babban rukuni na magani, (Bunza 1995). A waƘar Gagarabadau kuma Shata ya kawo misalin wani magani na kariya inda yake cewa:

Aradu na sha magani Nadadale ne ni

yanzu wuqa ba ta tava ni,

sai ya na faxin, Kushegere,

yanka kushegere, Tsii!

4.3.3 WaƘoƙin Maza

Wannan rukuni ya Ƙunshi waƘoƘin da wasu makaɗan Hausa suke yi don wasa gwarzayen da suka yi fice a wasanni kamar dambe ko kokawa ko tauri da dai sauran su. Jigon magani yana taka muhimmiyar rawa a irin waɗannan waƘoƘi domin duk wata bajinta da namiji zai nuna za a fahimci yana tinƘaho ne da maganin Ƙarfi ko na juriya ko na buwaya. Shi kuma wanda za a kushe, akan nuna duk da maganin da ya mallaka bai kai gwarzon makaɗin ba. Ana iya ganin irin wannan misalin a waƘar Jikan Bagwariya (makaɗin Tauri) ta Mamman Ɗanturwa.

“Gamon da mukai a cikin Zarumawa, xan Turwa

Rannan abun ya ba mu tausai

Na ga abun tausai a dawa

Rannan na ga abun kunya

Uban wani ya sheqa da gudu

Wani na gudu da kayan layu

Ya kwance kambuna ya watsar

Ca! Mamman, xan Turwa.

Layu da kambu wasu hanyoyi ne na sarrafa magani a al’adar Hausawa. Kai tsaye da zarar an gan su to an san magunguna ne da Hausawa ke mu’amala da su. Ba abin mamaki ba ne hoton su ko amfani da su a matsayin magani ya fito a irin waɗannan waƘoƘi.

4.3.4      Fanɗararrun WaƘoƘi

Malaman adabin Hausa musamman masana waƘoƘin baka sun keɓe wani rukunin waƘoƘi da suka kira fanɗararru. An laƘaba musu wannan suna ne bisa la’akari da irin mutanen da ake yi wa waƘa da kuma Ƙyamar da al’uma ke yi na irin abin da ya sa ake yi musu waƘar. Misalin irin waɗannan waƘoƘi sun haɗa da na ɓarayi da ‘yan caca. Gwarzayen da ake yi wa irin waɗannan waƘoƘi ba su kan yi fice ta yadda har za a yi musu waƘa sai sun haɗa da magani. Don haka dole ne yabo ta fuskar maganin ya yi tasiri a waƘoƘin nasu. Misali, Gambu mai waƘar ɓarayi yana yaba wani gwarzonsa Arzika da cewa:

“Wata rana an tashe shi Lolo

Naj ji Zabarmawa na ta Zaino! Zaino!,

Zaino kowa ka cewa,

Ban san da Zabarmanci sannan,

Naj ji Nuhwawa na ebeci!

Ban san da Nuhwanci ko kwabo ba,

Naj ji Hulani na hwaɗin gujjo!

Ba jin Hillanci nikai ba,

Sai ga Hausawa irin mu

Naj ji suna eho! Ɓarawo!

Nac ce ‘an yi ɓarna’

Wancen bawa ba kai shikai ba.

Na dubi dut rutsun kasuwan nan,

Sai shina tahiya tai yanga-yanga!

Hay yas shiga jirgi lahiya lau,

Wane jihwa ko bugawa!

Sai dai nuni ɗan gaton uwa,

Nac ce biya mallanmanka Arzika

Sun cika aiki babu wasa.”

A wannan ɗan waƘa Gambu ya umurci Arzika da ya biya malaman da suka ba shi maganin ɓacin rana domin aikin nasu ya yi kyau, an ga sakamako. Ya yi sata cikin kasuwa, aka tayar da shi amma aka kasa yi masa komai har ya ɓace.

Waɗannan kaɗan kenan daga cikin ɗimbin misalan da za a iya hangowa na tasirin da magani yake da shi a wannan rukuni na adabin bakan Bahaushe.

5.0          KAMMALAWA

HaƘiƘi wannan nazari ya tabbatar muna da cewa, dangantakar da ke tsakanin adabin baka na Bahaushe da magani tamkar ta tsoka da jini ce. A taƘaice, ba a iya raba su. Idan Bahaushe bai tanadi magani don kare kai ko cutarwa ko kuma biyan wasu bukatocin rayuwa ba, to dole ya nema saboda ciwo wanda yake ɗauka a matsayin babban maƘiyi. Haka kuma idan har adabin zai amsa sunansa na hoton rayuwar al’uma, (wanda ya amsa ɗin) to dole ne ya ɗauko maganin Bahaushe domin rayuwar Hausawa ba ta taɓa gudana ba tare da magani ba. An tabbatar da haka ne a wannan nazari, ta ɗaukan adabin baka Bahaushe a matsayin mizanin awo. Nazarin ya leƘa rassan adabin bakan guda uku, wato Zube, da Maganganun azanci da kuma Raha. A kowane ɓangare an sami misalai da suka nuna yadda sha’anin magani yake watayawa. A rukunin zube a an leƘe tasuniya da almara. A maganganun azanci aka zaƘulo magani a Karin magana. Ta ɓangaren raha kuma, an kawo misalai daga waƘoƘin jama’a da na maza da kuma cikin fanɗararrun waƘoƘi. Kenan, idan da za a auna duk wani ginshiƘin rayuwar Bahaushe kamar magani a adabi, ana ɗammahar haka za a ga ya wataya, domin ya ba adabin dama ya amsa sunansa.  

6.0              MANAZARTA    

Ahmad, I. A. (1984) “Cututtukan Ciki da Magungunansu.” Kundin Digiri na Farko,

(B. A. Hausa) Jami’ar Bayero, Kano.

Bunza, A.M. (1990), “HayaƘi Fid Da Na Kogo: (Nazarin Siddabaru Da Sihirin Hausawa)”, Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa), Jami’ar Bayero, Kano.

Bunza, A. M. (1991) “Sharhin Ciki da Wajen Littafin Ruwan Bagaja.” MaƘalar da aka gabatar a taron Makon Hausa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Bunza, A. M. (1995) “Magungunan Hausa a Rubuce: (Nazarin Ayyukan Malaman Tsibbu),” Kundin digiri na uku (Ph.D Hausa) Jami’ar Bayero, Kano.

Bunza, A. M. (2008) “Asirran Sata a Riwayar GambuTakardar da aka gabatar a

taron Ƙara wa juna sani na Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato.

Ɗangambo, A. (1984) Rabe-Raben Adabin Hausa Da Muhimmacinsa Ga Rayuwar Hausawa. Kano, Triumph Publishing Company.

Gusau, S. M. (1984) “Adabin Hausa na Gargajiya: ma’anarsa da Yanaye-yanayensa.” MaƘalar da aka gabatar a taron raya Harshen Hausa wanda Ƙungiyar Hausa ta Makarantar Tarbiyyar Malamai Mata ta Arabiyya ta Gusau ta shirya.

Gusau, S. M. (2008) Dabarun Nazarin Adabin Hausa, Kano, Benchmark Publishers Limited.

Sayaya, A. S. (2009) “Wasan Tauri a Ƙasar Katsina” Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa), Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato

Tremearne, A. J. N. (1913) Hausa Superstitions And Customs, Oxford, John Bale, Sons and Danielsson, LTD.

Tukur, A. (1988) “Nazari a kan Cututtukan da suka shafi Fatar Jiki da Magungunansu

a Bahaushiyar Al’ada.” Kundin Digiri na Farko, (B. A. Hausa) Jami’ar Bayero, Kano.

Umar, M. B. (1987) Dangantakar Adabi da Al’adun Gargajiya. Triumph Publishing

Company, Kano.

 

Yahya, A. B. (1994) “Dangantakar WaƘa da Tarbiyar ‘Ya’yan Hausawa.” MaƘalar da

Aka gabatar a taron Ƙara wa juna sani wanda Ƙungiyar marubuta da manazarta

waƘoƘin Hausa ta gudanar a Sakkwato.

Yahya, A. B. (1997) Jigon Nazarin WaƘa. Fisbas Media Services, Kaduna.

Yahaya, I. Y. (1977) Tatsuniyoyi da Wasanni, (littafi na uku) Oxford University

Press, Ibadan

Yahaya, I. Y. (1988) Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa, Zaria,

Northern Nigeria Publishing Company.[1] Adabin gargajiya shi aka yi bayani da Adabin da Hausawa suka gada kaka da kakanni. Shi kuwa

 adabin zamani, shi ne wanda ya zo a rubuce bayan da Hausawa suka sami hanyar rubutu.

[2] Don ganin cikakkiyar tatsuniyar dubi littafin Tatsuniyoyi da Wasanni, (littafi na uku) na Ibrahim Yaro Yahaya. Oxford University Press, Ibadan.

Post a Comment

0 Comments