Ticker

6/recent/ticker-posts

Li’irabin Sunayen Taurarin Littafin Ruwan Bagaja

Cite this article as: Abdullahi, I. S. S. (2013) “Li’irabin Sunayen Taurarin Littafin Ruwan Bagaja” in Humanities in Sub-Saharan World Ruwan Bagaja in Perspectives: Eight Decades of a Hausa Masterpiece in Prose (1933-2013) UNICAIRO/UMYU. ISBN: 978-125-481-5

Li’irabin Sunayen Taurarin Littafin Ruwan Bagaja

Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
E-main: ibrasskg@gmail.com
Lambar Waya: 0803 6153 050

Tsakure

A wannan nazari, an yi ƘoƘarin ɗora Littafin Ruwa Bagaja a mizanin awon sunayen na Hausawa. Yin haka shi zai sa a yi bitar sunayen domin tantance dacewa ko rashin dacewarsu musamman a yanayi ko lokacin da aka rubuta littafi. Haka kuma ya sa aka fahimci alaƘar sunan tauraro da rawar da ya taka a labarin. Abin fahimta a nan shi ne, baya ga zaɓen taurari da cusa musu ayyukan da za su yi don fitar da saƘon marubuci, Su ma sunayen da aka yi amfani da su suna da rawar da sukan taka wajen alƘacin labari. Wannan wata hanya ce ta gano yadda adabi yake amsa sunansa na “hoton rayuwar al’uma.”

1.0          Gabatarwa

Suna shi ne muhimmin abin da ke yi wa zance jagoranci. Fahimtar zance da gane wanda ya yi, ko wanda ake yi da shi, ya dogara ne ga sunayen mutanen da zancen ya Ƙunsa. Suna shi ke fitar da alƘiblar zance da kuma tunanin masu yin sa. A rubutu irin na adabi, musamman zube ko wasan kwaikwayo, haƘiƘa sunaye su ne ainihin zuciyar kowane saƘon da suke son isarwa. Idan da za a cire su, to saƘon ba zai fito ba, kuma bukatun ba za su biya ba. Kowane aikin adabi makamancin waɗannan yakan ɗauko sunayen taurarin da aka yi amfani da su wajen gina labarin. Burgewa a kowane irin rubutaccen zube ga misali, bai fi amfani da sunayen da suka dace a matsayin taurari ba. ƘoƘarin da wannan nazari zai yi shi ne, tsamo sunayen mutane da aka yi amfani da su ko aka ambata a littafi Ruwan Bagaja domin bayyana matsayinsa ko ma’anar kowane a tunanin Bahaushe. Haka kuma, nazarin zai nemi dacewar kowane suna wajen ƘoƘarin fito da saƘon marubucin. An yi tunanin ɗaukar wannan littafi ne domin kasancewarsa limami a rukunin littattafan farko na Ƙagaggun labarai da marubutan farko na Hausawa suka samar. Da yake an samar da wannan littafi ne a ƘoƘarin lashe gasa, tunani a nan shi ne, za a mayar da hankali wajen burgewa ba zaɓen sunaye ba. Babu Shakka, wannan nazari shi zai ba da damar auna wannan littafi ta fuskar sunayen da suka sa ya yi fice musammam a zamaninsa.

2.0          Littafin Ruwan Bagaja da Marubucinsa

Waiwaye, Hausawa suka ce shi ne adon tafiya. Duk da yake an yi ayyuka da dama waɗanda suka bayar da tarihin samuwar wannan littafin da marubucinsa. Wannan ba zai hana a ce wani abu a nan ba domin tabbatar da dugadugan nazarin. A taƘaice, littafin Ruwan Bagaja yana ɗaya daga cikin rukunin littattafan farko na Ƙagaggun labaran Hausa da Hausawa suka rubuta. Shi ne littafin da ya lashe gasar rubutattun Ƙagaggun labaran Hausa a shekarar 1933 (Yahaya 1988, Malumfashi 2009) Wannan gasa da Hukumar Talifi ta wancan lokaci ta shirya ya tuzgo ne bisa dalilin ƘoƘarin samar da littattafan da za a koyar da yara ’yan makaranta. Ƙumshiyar littafin ya ja hankalin mutane da yawa na tsawon shekaru tamanin (80) da ya yi. Wasu sun ɗauke shi littafin nishaɗantarwa mai ɗauke da tatsuniyoyi daban-daban. Su kuwa manazarta da ɗalibai suka ta daddagar littafin wajen ƘoƘarin fito da jigonsa, ko salailan da aka yi amfani wajen rubuta shi, ko rawar da taurari daban-daban suka taka da dai sauran su. A taƘaice, ayyukan ilimi da aka fitar a cikin littafi ba su da iyaka.

Alhaji Abubakar Imam shi ne marubucin littafin. Wannan suna ba baƘo ba ne musamman idan ana maganar rubutattun Ƙagaggun labaran Hausa. Ayyukansa na adabi su za a iya cewa, sun samar wa Ƙagaggun rubutattun labaran Hausa tagomashin da yake da shi a yau. Wannan tagomashin, shi ya sa harshen Hausa ya yi wa duk wani harshe maƘwabcinsa fintinkau musamman a fagen karatu da rubutu.   

Bayan da Alhaji Abubakar Imam ya lashe gasar 1933 da littafin Ruwan Bagaja, ya rubuta littattafan Ƙagaggun labaran Hausa da yawa. Waɗannan littattafan sun yi fice ba ma a zamaninsa kawai ba har a wannan lokacin. Daga cikinsu akwai “Magana Jari Ce.” Littafin da Hausawa suka daɗe suna alfahari da shi. Rayuwar Alhaji Abubakar Imam gaba ɗaya a kan rubuce-rubuce ya yi ta. Shi ne editan farko na jaridar “Gaskiya Ta Fi Kwabo.”

3.0              Sunayen Mutane Cikin Littafin Buwan Bagaja

A littafin Ruwan Bagaja an yi amfani da sunayen mutane kimanin arba’in (40). Daga cikin waɗannan sunaye akwai waɗanda taurari ne. Wato su suka yi ta ka-ce-na-ce a cikin littafin har suka fito da saƘon marubucin. Wasu kuma daga cikin sunayen ambaton su kawai aka yi wanda hakan ya taimaka wa taurarin na ainihi da ma marubucin don cimma burinsa. Muhimmin abin la’akari wajen zaɓen waɗannan sunaye shi ne, sun bayyanar da matsayi da sha’awa da kuma kusancin marubucin da abubuwa da yawa. Haka kuma, su suka sanar da jama’a irin yanayin tunaninsa da muhallin da ya fito, da has ashen ɗabi’un rayuwarsa. A wannan nazarin, za a yi ƘoƘarin karkasa waɗannan sunaye zuwa kashi uku. Sunayen asali, ararrun sunaye da kuma ƘirƘirarrun sunaye.

3.1 Sunayen Asali

Rukunin waɗannan sunaye an kira su na asali ne domin sunaye ne da da ma akwai su a rayuwar Hausawa. Hausawa sun saba amfani da su a rayuwarsu ta yau da kullum. Waɗannan sunaye sun wanzu gabanin rayuwar Imam, sun yi tasiri a lokacinsa, kuma bayan ya tafi, ya bar su. Daga cikin wannan rukuni na sunaye, akwai na yanka da kuma na laƘabi.

3.1.1 Sunayen Yanka

Sunayen yanka sunaye ne da Hausawa suka samu daga addinin Musulunci. Sunaye ne da Hausawa Musulmi suke zana wa ’ya’yansu a ranar da ake yanka ragon suna (Abdullahi 1997, Ibrahim 1997). A ranar wannan buki na haihuwa ake raɗa irin wannan sunan. Sunaye ne da Hausawa suka samu ko dai daga AlƘur’ani ko Hadisai ko cikin tarihin Musulunci ko kuma ma’anar ta kasance abu mai kyau a harshen da aka saukar da addinin. Ga sunayen yankan da wannan littafi na Ruwan Bagaja ya zo da su:

Shaihu/Shehu

Wannan sunan yanka ne ga Hausawa. Asali sunan laƘabi ne ga duk Bahaushe mai suna Usman. Daga baya sannu a hankali har aka kama ɗaukansa sunan yanka. Ya samu ne daga sunan Mujaddadi Usmanu Ɗanfodiyo. LaƘabin da ake yi masa na Shaihu ya sa duk mai suna Usman ya zama Shehu. A littafin an yi amfani da wannan suna a shafi na 1 da shafi na 13 da kuma duk inda Malam ZurƘe yake yi wa Alhaji Imam Kirari. Sunan Shaihu/Shehu malami yake nufi, kuma duk inda aka zo da shi a littafin hakan yake nufi ko mai dangantaka da sunan.[1]

Muhamman/Muhammadu

Wannan suna ne na yanka da Hausawa ke amfani da shi. An samo shi ne daga sunan Manzon Allah Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi). Wannan suna ba ya bukatar dogon sharhi. Fitowarsa a cikin littafin ya yi daidai da yanayin tunani na addinin marubucin a matsayinsa na musulmi. Sunan ya fito a duk inda Alhaji Imam ya yi wa Malam ZurƘe kirari da kuma shafi na 24 (sunan mai masaukin Alhaji Imam wan Inusa) da shafi na 39 inda aka ce:

 “Buɗe don Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu”

ZurƘe

Hausawa sun al’adantu da yanke sunayen yanka ko kuma a yi musu gyaran fuska saboda wasu dalilai. Misali sunaye irin su Fati, Fatu, Ima Tima duk sun fito ne daga sunan Fatima (’yar Manzon Allah SAW). Shi ma wannan suna na ZurƘe suna ne da aka gutsure kuma aka yi masa gyaran fuska daga sunan yanka na ZurƘarlaini. Suna ne sananne na Musulunci. Ya fito a cikin littafin a wurare da yawa. Malam ZurƘe kusan a ce shi ne tauraro na biyu mafi fice a cikin littafin wanda rawar da ya taka ya Ƙayatar. Yanayin da sunan ya fito ya tabbatar da lallai marubucin littafin Bahaushe ne da ya ɗabi’antu da gutsure sunaye a yi musu gyaran fuska. To sai dai fitowarsa a haka da kuma rawar da mai sunan ya taka bai rasa nasaba da tarihin wani sanannen motsattsen mutun a birnin Katsina wanda ya yi zamani kimanin shekaru ɗari (100) da suka wuce. Ga dukkan alamu Imam ya san shi suna yana. Wannan ne ya sa sunan da ɗabi’unsa suka yi tasiri a cikin littafin.

Ɗalhatu, Sule, Hashimu da Muhtari

Waɗannan sunaye na yanka na maza da suka fito a shafi na 12 na littafin ba su fito a matsayin waɗansu taurari ba. Sun fito ne a matsayin wata hanya ta zaurance ko ɓoye ma’ana. HaƘiƘa duk sunaye ne na yanka da Hausawa suka saba amfani da su yau da kullum. Haka kuma, sun fito ne da lafuzzan da aka saba furta su a Bahaushen lafazi. Duk da kasancewar marubucin malizincin harshen Larabci, bai yi kauɗin sauya musu lafazin da Bahaushe ya saba furucinsu ba. Sunan Sule ne kawai za a iya cewa, an samu ta hanyar gyaran fuska daga sunan Sulaiman, don neman sauƘi Bahaushe ya kira shi Sule. A asalin sunan Ɗalhatu yana nufin Tsarkakakke, Hashim daga Banu Hashim, Muhtari kuna yana nufin Zaɓaɓɓe.

 Jamilatu

A cikin littafin, sunan Jamilatu ya fito ne a shafi na 14. Ita ce yarinyar da Imam ya shiga nema da aure a gari Ɗandago. Wannan suna ne na yanka da Hausawa suka saba amfani da shi. A Larabce yana nufin “kyau”, ko “mai kyau.” Kowace Ƙabila na son mace mai Ƙyau. WataƘila tunanin Bahaushe na kasancewar mata ake siffantawa da kyau ya sa aka laƘaba musu irin wannan suna a matsayin sunan yanka.

 Armi

 Kamar ZurƘe haka shi ma sunan Armi ya samu ne daga suna Armaya’u. Suna ne na Musulunci da Hausawa ke amfani da shi a matsayin sunan yanka.[2] Wato haruffan Ƙarshe na -ya’u aka gutsure kamar yadda Hausawa suke yi wa sunan Zakariyya/Zakariya’u (Zakari). Wannan suna ya fito a shafi na 15 na littafin. Suna ne na yaron da ke ja wa Imam sanda a lokacin da aka yi masa magani ya makance a gari Ɗandago. A littafin an nuna yaro ne mai haƘuri.

 Inusa da Iro

Waɗannan su ma sunaye ne da Hausawa ke amfani da su a matsayin sunayen yanka duk da yake an yi musu gyaran fuska. Sunan Inusa dai suna ne da ya samu ga Bahaushe daga sunan Annabi Yunus. Haka shi ma Iro Kwaskwarima ce aka yi daga sunan Annabi Ibrahim. Sunayen ba wani tasiri suka yi a cikin littafin ba. An kawo sunan Inusa ne a shafi na 24 inda ake cewa:

“Ai kuwa jiya na ji baƘon nan Alhaji, wanda aka saukar gidan

 Malam Muhammadu wan Inusa, bai yi barci ba, ….

Sunan Iro kuma an yi amfani da shi ne a shafi na 28 cikin littafin, a kirarin da ake yi wa mai masaukin Alhaji Imam a garin Miska.

“Na Malam Iro masu kwana Salla!”

 Nuhu, Sulaimanu da Dawuda

Su ma waɗannan sunaye, sunayen annabawan Allah ne da Hausawa suka ci karo da su a cikin AlƘur’ani a wurare da yawa. Wannan ya sa ake amfani da su a matsayin sunayen yanka kai tsaye kamar yadda suka fito a cikin littafin. A littafin, ba a sauya musu kamanni ko furuci ba. Wato yadda ake furucinsu haka suka fito. Duk sunayen dai an kawo su ne ba a matsayin wasu taurari ba. Sunan Nuhu ya fito a shafi na 37 ta bakin wani aljani, inda ya nuna shi ne bawan takobin Yafisu ɗan Nuhu. Sunayen Sulaimanu da Dawuda kuma sun fito ne a shafi na 39:

“Buɗe don Alfarmar Annabi Sulaimanu ɗan Dawuda.”

 Rakiya

Wannan suna ne na mace wadda Hausawa suka yi wa gyaran fuska musammam wajen furucinsa kuma suke amsa shi a matsayin sunan yanka. Asalin wannan suna shi ne RuƘayya (Sallau 2011). Suna ne na ’yar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi). A wuri ɗaya aka nuna fitowar wannan suna a littafin, (shafi na 44) inda Imam ya nuna ya umurci aljani da ya kai shi garin da ya baro matarsa Rakiya ya ɗauko ta.

3.1.2      Sunayen LaƘabi

Sunayen LaƘabi ga Bahaushe su ne sunayen da ba na yanka ba. Sunaye ne da ake laƘaba wa mutum saboda wani dalili. Galibi, duk mai sunan laƘabi yana da sunan yanka. Sunan laƘabi yakan fi karɓuwa ga jama’a. A littafin an ci karo da wani rukuni na wasu sunaye da suka kasance na laƘabi ne. A wannan fasali, za a iya karkasa waɗannan sunaye zuwa rukuni-rukuni.

3.1.2.1  LaƘabin Addini

Waɗannan sunaye ne na laƘabi masu alaƘa da wani lamari na addinin musulunci. Hausawa suna amfani da waɗannan sunaye kamar yadda a wannan littafin ma aka fito da su. Misalin waɗannan sunaye su ne:

Alhaji

Wanda ya yi aikin hajji ko wanda aka haifa a ranar hawan Arfa. Haka kuma Hausawa suna amfani da wannan suna kai tsaye ga mai hali, ko wajen sakaya sunan yanka ga wanda ake jin nauyi, ko kuma wajen yi wa mutum kirari. Wannan suna ya fito a shafi na 5 da na 8.

 

Liman & Imam

Wannan laƘabi ne da ake yi wa mai jagorancin salla. Duk da yake asalin kalmar Larabci ce, Hausawa sun same ta ne daga Azbinawa (Buzaye) waɗanda suka kira shi Le’imame. Wannan suna ya fito shafi na 5 da 8 da kuma wurare da yawa. Hasalima shi ne sunan babbab tauraron littafin.

 

Malam

LaƘabi ne da ake yi wa duk wani mai koyarwa (musamman ilimin addini). Haka kuma ana iya kiran duk wani Bahaushe da wannan laƘabi muddin dai ba yaro ba ne. Daga cikin waɗanda aka kira da wannan laƘabin a cikin littafin akwai: Malam Na-Bakin-Kogi (shafi na 1), Malam ZurƘe (shafi na 8), Malam Ɗalhatu (shafi na 12), Malam Muhammadu (shafi na 24) da sauransu.

 

3.1.2.2.                        LaƘabin Sarauta

Irin waɗannan laƘubba suna zuwa ne tare da sarauta ko mulki a al’umar Hausawa. Mutane suna amsa irin waɗannan sunaye idan suna riƘe da irin waɗannan sarautu ko idan suka jiɓince shi. A littafin an sami irin sunayen kamar yadda suke a yawancin Ƙasashen Hausawa. Wannan ya tabbatar muna da cewa, hoto ne ake nunawa na rayuwar Hausawa. Ga misalan waɗannan sunaye. Sarkin Sudan (Shafi na 3), Wawan Sarki (Shafi na 21), Sarkin Zagi (Shafi na 22), Sarkin Gardi (Shafi na 28), Waziri (Shafi na 19 & 31), Magaji (Shafi na 24)

3.2          Ararrun Sunaye

Wannan rukuni na sunaye, ya Ƙunshi sunayen da a zahiri akwai su a duniyar ’yan Adam, ko an taɓa yin su a tarihi amma babu su a duniyar Hausawa. Marubucin ga dukkan alamu ya kawo su ne domin ya tabbatar wa Hausawa abin da suka ji ko suka karanta na tarihi. Daga cikin irin waɗannan sunaye akwai Ziyazzinu wanda ya fito a shafi na 1 na wannan littafin. Ziyazzinu sunan wani sarki ne da aka taɓa yi a daular Yemen. Wani misalin kuma na irin waɗannan sunaye shi ne Iwaja ɗan UnƘa wanda ya fito a shafi na 16. Wannan suna an tabbatar da samuwarsa a cikin Ƙissa Isra’ilawa, a kan tarihin Annabi Nuhu. Wannan Ƙissa ta shahara cikin tafsirai na AlƘur’ani musamman Saawii da Jalaalaini.[3]

3.3          ƘirƘirarrun Sunaye

 A wannan littafin an sami rukunin wasu sunaye waɗanda ga dukkan alamu ƘirƘirarru ne ga Hausawa. Wato ko dai Hausawa ne suka ƘirƘiro su bisa wani dalili, ko kuma hikima dai ce ta marubucin. Abin sha’awa da waɗannan sunaye shi ne kowanensu ya dace da muhallin da aka samar da shi.   

Koje

A wannan littafin an yi masa laƘabi da sarkin labari. Wannan sunan wani tsuntsu ne mai yawan Ƙara kuma ba ya gajiya. Duk mutumin da Bahaushe ya fahimci ya cika yawan surutu ko ba da labari sai a sa masa wannan sunan kamar dai yadda ya zo a shafi na 1 na wannan littafin.

 

SaƘimu

Wannan kalma ce ta Larabci da ke nufin mara lafiya ko cuta. Idan aka yi la’akari da ta’asar da mai wannan sunan ya aikata a cikin labarin/littafin (Shafi na 3-5) to za a ga ya dace da sunan da marubucin ya ƘirƘiro masa. Mara lafiyar ƘwaƘwalwa kaɗai ke iya yin abin da ya aikata.

 

YaƘutatu

Shi ma wannan suna ƘirƘirarre ne da ba a saba jin shi ba a al’umar Hausawa. A Larabce Kalmar YaƘutu yana mufin dutse na Ƙawa. Sai aka faɗaɗa ma’anar ko aka mutuntar da kalmar, aka bayar da shi a matsayin suna ga mahaifiyar Imam a shafi na 5 na littafin.

 

Zandoro ɗan

Zotori

Waɗannan sunaye biyu ba Hausa ba ne. Ko a wasu harsunan da furucinsu ke da kusanci da shi kamar Nufanci, bai bayar da ma’ana ba. A nan ma hikimar marubucin ce kawai na harhaɗa lafuzzan da za su nuna a wurin furuci a ga alamar mutumin mai tsawo ne. Idan za a lura, a Hausa harafin “Z” da wasalin a sun fi yawa. misali akan ce ZanƘaleliya, ZanƘal-zanƘal, Zandameme da dai sauransu. Wannan suna ya fito a shafi na 16.

 

Yafisu

Wannan suna ne ba na Hausawa ba, kuma ba na wata Ƙabila nan kusa ba. Lafuzzan sunan ya yi kama da sunayen aljanu. Wannan ba zai zama abin mamaki ba da da yake marubucin sai da ya shiga duniyar aljanu kafin ya Ƙarasa fito da saƘon nasa.

 

4.0          Kammalawa

Nazarinmu an mayar da hankali ne a kan ƘoƘarin samar da madogara ko muhalli ga sunayen da Alhaji Abubakar Imam ya yi amfani da su wajen gina shahararren littafinsa na Ruwan Bagaja. Wannan cike giɓi ne aka yi na abin da aka ga alamar an bari a nazarin wannan shahararren littafi mai tarihi. Kasancewar suna linzami ne mai jan ragamar saƘon da ke cikin littafin, an ɗora kowane suna da aka tsamo a rukunin da ake ganin ya dace da shi. Haka kuma, nazarin ya samar da ma’ana ko muhallin wasu sunaye a rayuwar mutanen da aka rubuta littafin domin su. HaƘiƘa, wannan littafi ya karɓi sunansa na adabi, inda ya ɗauko hoton akasarin sunayen da Hausawa suka saba da su a matasayin taurarinsa. Nazarin, ya Ƙara fito da hikimar marubucin na la’akari da al’adun mutane da muhallinsu da addininsu da yanayin tunaninsu wajen gina musu labari da sunayen da suke da tasiri a rayuwarsu. Tabbas, bai yi wa sunayen littafin kwasan karan mahaukaciya ba, domin kowane suna da rukuninsa. Haka kuma, bai yi musun shigen kutse ba, domin ma’anoninsu sun dace da su. Bugu da Ƙari bai yi musu shan ruwan tsuntsaye ba domin kowane suna an sa masa zancen da ya dace a bakinsa.

5.0 Manazarta

Abdullahi, I. S. S. (1997) “Tasirin Zamani da Illolinsa Kan Sunayen Hausawa.” MaƘalar da aka gabatar a taron Ƙara wa juna sani a Tsangayar Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.

Al-Masumi, B. M. A. (1999) A Guide to Islamic Names Ad-Dar As-Salafiah, Makkah Al-Mukarramah Saudi Arabia

Aminu, M. (1992) Matsayin Sunaye A Al’adun Hausa. Aminu Zinaria Recording & Publishing Co. No 135, Sagagi, Kano City.

Bunza, A. M. (1991) “Sharhin Ciki da Wajen Littafin Ruwan Bagaja.” MaƘalar da aka gabatar a taron Makon Hausa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Bunza, A. M. (2006) Gadon Feɗe Al’ada Tiwal Nig. Ltd Lagos.

Ɗangambo, A. (1984) Rabe-Raben Adabin Hausa Da Muhimmacinsa Ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph Publishing Company.

Gusau, S. M. (2008) Dabarun Nazarin Adabin Hausa, Kano, Benchmark Publishers

Limited.

Ibrahim, M. A. (1997) “ Suna da Sunaye A Al’adar Bahaushe.” Kundin Neman Digirin

Farko (B. A. Hausa) Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.

Imam, A. A. (1999) Ruwan Bagaja, Zaria: Nothern Nigeria Publishing Company.

Ingawa, A. (1969) Ruwan Bagaja. The Water of Cure. Fassarar Hausa zuwa Ingilishi,

Zaria: Nothern Nigeria Publishing Company.

Kudan, M. B. T. (1987) “Kwatanta Jigon Ƙagaggun Labaran Gasa.” Kundin Digiri na

Ɗaya, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya

Malumfashi, I. (1996) “The Making of Abubakar Imam’s Ruwan Bagaja: A preliminary Investigation.” MaƘalar da aka gabatar a taron ANA Arewa House, Kaduna.

Malumfashi, I. (2009) Adabin Abubakar Imam, Sokoto: Garkuwa Media Services LTD.

Mora, A. A. (1989) Abubaka Imam Memoirs, Northern Nigerian Publishing Company, Zaria.

Mukhtar, I. (2004) Jagoran Nazarin Ƙagaggun Labarai, Kano, Benchmark Publishers

Limited.

Sallau, B. A. (2011) “Raɗa Suna jiya da Yau” a cikin mujallar Himma Journal of

Contemporary Hausa Studies Vol. 3 Department of Nigerian Languages, Umaru Musa Yar’adua Unuversity, Katsina.

Yahaya, I. Y. (1988) Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa, Zaria:

Nothern Nigeria Publishing Company.

Yunusa, M. M. (1985) “Kasancewar Tatsuniyar Ruwan Bagaja tushen littafin Ruwan

Bagaja na Abubakar Imam ” Kundin Digiri na Ɗaya, Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Sakkwato.



[1] Asalin wannan sunan a Larabci “Sheikh” shi ne “tsoho.” A can da suna amfani da “ajuz” mai nufin gajiyayye. Da suka gano ba dukkan tsoho ne gajiyayye ba, suka ci gaba da “sheikh” wato wanda ya tsufa cikin abu.

[2] Armaya’u Annabi ne daga Bani Isra’il da aka ambata a Ƙissar Annabawa kamar yadda tafsirin Jalalaini ya kawo

[3] Wai Iwaja ɗan UnƘa ruwan Ɗufana bai nutse shi ba, a cibi ya tsaya masa saboda tsawonsa.Haka kumma an nuna a lokacinsa yakan kama kifi ya nuna ga rana su gasu ya ba matarsa.


Post a Comment

0 Comments