Hani Da Horo A
Matsayin Tubalan Ginin Waƙar ‘Baje Kolin Hajar Tunani’
Ibrahim
Abdullahi Sarkin Sudan Ph. D
Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
e-mail: ibrasskg@gmail.com
GSM:
08096266581/08036153050
1.0
Gabatarwa
Zamantakewar mutane da muhallinsu da ma abin da
suka dogara imaninsu a kansa yakan yi musu jagoranci wajen samar da dokoki ko Ƙa’idoji a al’umar. Wannan tunani bisa al’ada, yakan Ƙunshi abin da ake so mutum ya aikata bisa la’akari
da fa’idodinsa. Haka kuma a ɗaya haujin akwai abubuwan da ba
a so a aikata saboda hasashen illolin da za su iya haifarwa ba ga mutum kaɗai ba har da al’uma baki ɗaya. Isar da irin wannan saƘo ko faɗakarwa a al’uma yakan yi sauƘi ne idan Allah ya huwace mata fasahohi
da mutane masu kaifin basira da kyakkyawar tarbiya da sanin ko laƘantar waɗannan ladubba. A wannan nazari
za a kalli yadda aka yi amfani da fasahar saƘa kalmomi cikin zantuttukan
hikima wajen gaya wa Hausawa (musamman Musulmi) abin da ya kamata su sani
dangane da hani da horo a rayuwarsu ta duniya. A taƘaice, dubi ne za a yi a kan
yadda aka yi amfani da hani da horo a matsayin tubalan ginin waƘar ‘Baje Kolin Hajar Tunani.’
2.0
Matashiya
A wannan fasali za a bayar da haske ne ga mai
karatu ko yi masa sharhin muhimman kalmomin da taken wannan nazari ya Ƙunsa. Haka kuma a wannan fasalin ne za a yi sharhin
waƘar da tarihin mawallafin a taƘaice.
2.1 Hani da Horo
Kalmar hani tana iya ɗaukar fassarori biyu masu alaƘa da juna. Kalmar hani wadda ta tuzgo daga hana na iya ɗaukar ma’anar Ƙin aikata wani abu. Misali ana
iya cewa:
-Ya hana su dawowa.
- Ya hana ni shiga gidan.
- Ya hana a yi masa allura.
A wata
ma’anar kuma, ana iya kallon kalmar da ma’anar doka ko umurni na haramcin
aikata wani abu ga mutum ɗaya ko mutane da yawa. Wannan
shi ma kai tsaye Ƙin amincewa ne a aikata wani abu. A
tanade-tanaden tarbiyantar da al’uma, duk abin da aka kira hani to kai tsaye ba
a ɗammahar mutum ya aikata shi saboda muninsa ko
illar da yake haifarwa. Akwai hane-hane a al’umomi da yawa waɗanda ga dukkan alamu sun game ko’ina. Wato babu
wata nagartattar al’uma da ba ta yi hani da su ba. Misali, sata da Ƙarya, da zalunci, da dai sauransu. Haka kuma ba a
rasa sauran hane-hane a kowace al’uma waɗanda suka taso a sakamakon
tunanin mutane ko yanayin wurin zamansu ko kuma abin da suka dogara imaninsu a
kansa.
Ita ma kalmar horo a Hausa tana iya ɗaukar ma’anoni daban-daban.
akan yi amfani da kalmar wajen nuna ladabtarwar da ake yi wa wanda ya aikata
abin da ya saɓa. Misali, ana cewa:
-
Kotu ta yi masa horo mai
tsanani da ta tabbatar da laifin da ya aikata.
-
Horon da aka yi masa ya fi na laifin da ya aikata.
Hausawa suna amfani da kalma horo don bayanin koyar
da wani abu ko kuma gyara wani abin amfani ta yadda ake so ya kasance. Misali:
-
Sai an hora tanda kafin a fara toya masa da ita.
-
Akwai horo na musamman da ake ba ’yansandan dawaki.
Wata ma’anar kuma da ake ba wannan kalmar wadda
kuma ta fi dacewa da muhallin wannan nazari ita ce umurni. Wato a jawo hankalin
mutum da ya aikata wasu ayyuka waɗanda ake tunanin su samar masa
da kyakkyawan sakamako. A nan ma ana samun horo na gama-gari da kuma waɗanda suka keɓanta ga bukatun kowace al’umma. Misali, al’amurran
da suka shafi kishin Ƙasa, taimakon gajiyayyu, tausaya wa mata da yara,
ladabi da biyayya, furucin lafuzza masu kyau duk tarbiyoyi ne masu kyau da
al’uma take horon a aikata su. Baya ga waɗannan kuma, akwai waɗansu da al’umomi daban-daban sukan hori a aikata
bisa ga tanade-tanaden addini ko yanayin wurin zama ko al’adun da aka gada da
dai sauransu.
2.2
Baje
Kolin Hajar Tunani
Wannan waƘa tana ɗaya daga cikin ɗimbin waƘoƘin da AƘali Bello Giɗaɗawa ya rubuta. Ya nuna ta samu
ne a shekarar 1990.[1]
WaƘa ce ’yar Ƙwar biyu mai ɗauke da baitoci ɗari da shida (106) Kamar galibin waƘoƘinsa, wannan waƘar ba ta tsayu a kan amsa-amon
ciki na bai ɗaya ba. Sai dai amsa-amon waje
na duk ilahirin baitocin waƘar sun Ƙare ne da harafin wa. Ta fuskar jigo kuma, waƘa ce da ke jan hankalin mutane ga aikata abin da ya
dace da kuma kyautata hanyoyin mu’amala tsakanin mutane. A taƘaice, wa’azi waƘar ta Ƙunsa. shi kuma wa’azi, ba wani
abu na ne illa jan hankalin mutane ga barin aikata saɓo da kuma horon su ga aikata ayyukan Ƙwarai.
2.3
AlƘali (Dr) Muhammadu Bello Giɗaɗawa
(OFR)
A fagen rubutacciyar waƘar Hausa, AlƘali Bello Giɗaɗawa (Ɗangaladiman Wazirin Sakkwato) ba ya bukatar
gabatarwa. An yi tunanin cewa wani abu ne a kansa domin tabbatar da tsayuwar
dugadugan wannan nazari da kuma fayyace shi musamman ga waɗanda ba su ratsi tarihin sha’iran Ƙasar Hausa na Ƙarni na 20 ba.
An haifi AlƘali Bello Giɗaɗawa a shekarar 1909. Ya sami
nasarar yin karatun addinin Musulunci da kuma karatun boko. Ya yi aikin jirgin Ƙasa a wurare da dama a arewacin Ƙasar nan. Daga baya kuma ya yi aikin alƘalanci. Ya taɓa zama mai kula da masallatan
Shehu da na Bello a cikin birnin Sakkwato. Daga baya kuma ya zama sakataren Jama’atu Nasril Islam reshen Sakkwato.
Ta fuskar rubutattun waƘoƘin Hausa kuma, a halin da ake cikin ana da fiye
da waƘoƘinsa guda 50. Daga cikinsu akwai waƘoƘin masu jihadi na Larabci da ya fassara da Hausa.
Haka kuma akwai na wasu Sha’iran da yayi wa tahamisi. Shaharar AlƘali Bello a rubutacciyar waƘar Hausa ta sa ya jagoranci Ƙungiyar marubuta da manazarta waƘoƘin Hausa na wannan Ƙasar na fiye da shekara 20. Ya
sami lambobin yabo da girmamawa da dama. Daga cikinsu akwai digirin Dakta da
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo ta ba shi a shekarar 2000. A shekarar
2002 kuma gwaunatin tarayya ta ba shi lambar yabo ta Ƙasa mai laƘabin OFR.[2]
3.0
Tubalan
Hani a WaƘar Baje Kolin Hajar Tunani
Jan hankalin mutane a wannan waƘar domin su guje wa aikata wasu munanan ayyuka sun
zo ta hanyar amfanisu kalmomi ko lafuzza guda huɗu:
-
Bar/bari
-
Kar ka/kak ka
-
Guji
-
Daina
A cikin waƘar, da wannan Sha’irin ya yi
amfani wajen tabbatar da saƘonsa na hani kuma suka fito a matsayin tubalan da
suka gina waƘar baki ɗaya. A duk inda ya yi amfani da
ɗaya daga cikin waɗannan kalmomi ko lafazi, wani aibi ne yake ƘoƘarin jan hankalin mutane daga illarsa. Ga yadda
ya yi amfani da wasu tubalan nasa.
3.1 Son rai
Son rai shi ne mutum ya aikata abin da ransa ya
yi masa daɗi ba tare da tunanin matsayinsa
ko sakamako ba. A duk lokacin da mutum ya bi son ransa musamman a kan jin daɗin duniya, to sai ya yi da-na-sani, ya shiga
cikin wani hali na damuwa. A cikin waƘar, an ja hankalin mutane da
barin bin son ransu tare da mummunar sakamakon yin hakan.
4. Kai
Bello ranka shina ta yo ma alƘawal,
Bari
son ka bi shi, shi sa ka hanyar damuwa.
3.2
Ƙwaɗayi
Hausawa na yi masa kirari da ‘mabuɗin wahala.’ Wannan wani babban abin hani ne wanda
idan ba ladabtu da Ƙin barinsa ba to sakamakon yakan yi muni. AlƘali Bello ya ja hankalin mutane da su bar sa kwaɗayi a sha’aninsu na duniya, tare da bayyana
sakamakon da za a tarar.
6. Bari
sa kwaɗanka ga al’amurran duniya,
Tsananin
kwaɗai shi za shi sa ma ruɗuwa.
3.3
Hassada
Hassada na nufin Ƙyashin abin da wani ya samu na
alheri ko wata baiwa da Allah ya ba wani. HaƘiƘa wannan mummunan abu ne da AlƘali Bello ya jaddada hani da yinsa kamar yadda ya zo
a koyarwar addinin musulunci.
10. Bari
hassada ka san rabo duka an raba,
Tun can
azal in ya tafo bai tauyuwa.
3.4
Alfahari
Alfahari shi ne ji da kai ko cika baki (Bello
2006:11)Wannan wata ɗabi’a ce da Hausawa ke Ƙyamar mai yin ta. Kimar mutum yakan zube idan ya ɗabi’antu da ita. Wannan ne ya sa Ɗangaladima yake jan hankalin a bar aikata ta.
15. Kai
Bello so danginka kak ka yi alfahar,
To
girmama su Ƙwarai ka ba su gudunmuwa.
3.5
Zalunci
Bahaushe ya ɗauki zalunci a matsayin wasu dabaru ko amfani da
wata dama a tauye hakkin wani, a cuce shi ta kowace irin hanya. Sha’irin ya yi
tunanin faɗakarwa a kan hani ga aikata
haka wajibi ne. Duk hakkin da aka ɗora wa mutun to kada ya yi
tunanin Ƙwaruwa a kansa.
22. Ka
tsare amana sadda duk taz zo maka,
Hakkin
mutane kak ka yo musu Ƙwaruwa.
3.6
Bin
Diddigi, Tsegumi da Kwarmato
A cikin ɗango ɗaya Alkali Bello ya fito da hani a kan waɗannan munanan ɗabi’u. ƘoƘarin bin diddin duk abin da aka yi wani hali ne
na rashin yarda wanda ba a san mutumun kirki da yinsa ba. Tsegumi shi ne ɗabi’ar jin abin da bai shafi mutum ba, da kuma
bayar da labarin mutum musamman maras kyau a bayan idonsa. Wannan mummunar ɗabi’a ce, abin Ƙyama. Al’ummu da yawa sukan
la’anci mai yin shi. Haka kuma kwarmato, wato jinini musamman a kan wani abu da
aka aikata wanda ba daidai ba, ba ya da wata fa’ida sai zubar da girma.
Gyaruwar mutum in ji AlƘali Bello shi ne ya guji waɗannan halaye uku.
43. Bari
diddigi bari tsegumi bari kwarmato,
Halinga
ukku barinsu shi a gyaruwa.
3.7
Haɗa Kai da
Miyagu
A al’adance, ana bukatar idan mutum zai yi
shawara, to ya nemi mutanen Ƙwarai su sa shi a hanya. ƘoƘarin bin miyagun mutane wajen Ƙulle-Ƙulle ko shawara wata mummunar ɗabi’a ce da Ɗangaladima ya tunatar ga yin
hani da aikata shi.
55. Guji
Ƙulle Ƙulle da masu mugun tunani,
Ka biɗo tsari gun Rabbu zai ma garkuwa.
3.8
Ƙulla Shairi
Hausawa suka ce, ‘shairi kare ne, mai shi yake bi.’
A ckin wannan waƘar an tabbatar da haka ta hanyar jan hankalin
mutane su bar yinsa domin komai daɗewa a kan mutum zai koma.
56. Bari
Ƙulla shairi wanda yak Ƙulla shi kau,
Ɗaki guda suka kwanciya su yi kokawa.
3.9
Gardamar
Banza
AlƘali Bello Giɗaɗawa ya yo hani da gardamar
banza a tsakanin mutane. HaƘiƘa wannan lamari abu ne da ya daɗe yana ta da husuma da ɓata zumunci da kuma ɓata sunan waɗanda suka ɗabi’antu da shi. Idan ma gardamar mutum zai yi, to
AlƘali Bello ya nuna a yi wadda take kare addini.
42. Bari gardamar banza ka zan yin haƘuri.
Ka yi fi sabilillahi daina biyar hawa.
Waɗannan kaɗan ke nan daga cikin hane-hanen da AlƘali Bello Giɗaɗawa ya ja hankalin muta ne daga barin aikata su.
Tubalai ne Ƙanana da ya yi amfani da su wajen gina waƘar, amma hanya ne idan an auna su da mizanin awon
tunani.
4.0
Tubalan
Haro a WaƘar Baje Kolin Hajar Tunani
Yanayin horo a matsayin tubalan gina waƘar Baje Kolin Hajar Tunani ba su zo da wata sifa ko
keɓaɓɓun kalmomi da za a iya fitar da
su kamar na hani ba. Ƙumshiyar baiti ne kawai zai iya nuna horo ake yi ga
aikata wani abu mai fa’ida da ake tunanin yin sa zai taimaka wa rayuwa duniya
da lahira. A wannan fasalin za mu dubi kaɗan daga cikin tunatarwar da AlƘali Bello ya yi ta hanyar yin horo ya kuma yi amfani
da shi a matsayin tubalai wejen gina waƘar tasa.
4.1 Tuba
Tuba a taƘaice yana nufin barin aikata saɓo tare da alƘawarin ba za a sake aikatawa
ba. Duk mutumim da ke yawaita aikata saɓo musamman waɗanda mutane suke shaidawa to ya kyautu a hore shi
da ya koma ga hanyar gaskiya. Ya nemi Allah ya yafe masa ko kuma mahalukin da
ya saɓa wa. Ganin muihimmancin hakan
ne ya sa AlƘali Bello Giɗaɗawa yake cewa:
5. Kai
dai ka tuba da hanzari shi yaf fi kyau,
Tuba
nasufi shi ka yo ma garkuwa.
……………………………………………
7. In
ka yi swaɓo yo nadama ka jiya,
Sannan
ka tuba ka bar biyar mai bauɗuwa.
4.2
Tuna
Ranar Hisabi
Tunatar da mutane da horon su riƘa tuna akwai wata rana tafe da za a yi hisabi yana
da fa’ida Ƙwarai. Wannan yakan sa mutum ya guji yin zalunci, ya
kuma kimanta gudanar da kyakkyawar hulɗa da mutane saboda tsoron abin
da zai faru a wannan ranar. AlƘali Bello Giɗaɗawa ya yi horo ga yin haka a
cikin wannan waƘar:
8.
Ajalinka nisa a garai ko nan kusa,
Shiga tunani ka tuna da ranar taruwa.
4.3
Aikin Ƙwarai
Idan mutum ya aikata ayyukan Ƙwarai haƘiƘa zai sami natsuwa a nan
duniya, ga kuma sakamakon alheri da zai samu a kiyama. Wannan yana ɗaya daga cikin tubalan da AlƘali Bello Giɗaɗawa ya yi amfani da su wajen
gina wannan waƘar.
9.
Aikin Ƙwarai shi dai ka anfaninka can,
Daure
ka yo shi ka bar kwaɗai gun futsuwa.
4.4
Taimako
Kowane mahaluki na duniya yana son a taimaka masa
a duk lokacin da yake cikin tsananin wata bukata. Auna irin kimar jin daɗin da mutum kan yi idan an taimaka masa a lokacin
da yake bukata shi ya sa AlƘali Bello Giɗaɗawa ya yi horo da cewa,
12. Ka
yi jinƘayi gun ’yan uwanka ka taimaka,
Bari
homa ka san ba ta jawo Ƙaruwa.
4.5
Ladabi
da Biyayya
Muruwar mutum takan Ƙaru ainun jama’a suka fahimci
yana da ladabi da biyayya. Duk babba yana sha’awar ya ga an girmama shi an yi
masa ladabi. Idan yana da tunani shi kuma sai ya tausaya ga na Ƙasa. Muhimmancin wannan kyakkyawar ɗabi’a ya sa aka yi horo da hakan a cikin wannan
waƘar.
13.
Manyanku yo ladabi garesu ka girmama,
Girmansu
shi ne naka bar yin ɗemuwa.
4.6
Zumunta
Zumunta abu ne da ke Ƙara kyautata al’umma. Duk
mutumin da ya ɗabi’antu da ita zai zama abin
sha’awa kuma rayuwarsa ta inganta. A wannan waƘar, an tunatar da horon da
ubangiji ya yi a kai.
16. Ka
san zumunta an yi horo mai yawa,
Ka riƘa ta zak kyawo ka yo mata garkuwa.
4.7
Kyautata
Niyya
A wannan waƘar an yi horo da a kyautata
niyya a duk abin da mutum zai aikata. Idan mutum zai yi abu, ya yi shi don
Allah. Ya kuma kasance, tunanin ayyukan alheri su ke jagorancin rayuwar mutane.
Yin haka zai taimaka wa mutane daga yin aikin riya, wanda sakamakonsa ba lada.
Haka kuma an nuna baƘar aniya ba ta da sakamako illa wutar jahannama.
21. To
kyauta niyya har ta zan ta zan fara,
Ture
baƘa don kat ta kai ka ga Ƙonuwa.
4.8
RiƘe Amana
A Hausance, Amana na nufin mutum ya kula da wani
abu da aka damƘa masa. kada ya bari ya lalace ko ya salwanta.
Idan ya kasance mutum mai amana ne to al’amurransa sukan yi kyau. Idan aka ci
amana kuma a sami akasi.
24. Ka
tsare amana ko da yaushe ka bar sake,
Mai
cin amana ba shi kyawaon rayuwa.
4.9
Gaskiya
Yin gakiya da riƘe ta da aiki da ita da taimaka
mata abubuwa ne da bayyanar da nagartar mutum da ma al’uma baki ɗaya. Horon mutane ga kusantar gakiya da taimaka
mata ta kowace hanya abu ne mai kyau ga mai zurfin tunani. Idan aka nazarci
sakamakon rashin riƘe gaskiya a matsayin tafarki, dole ne a yi watsi
da Ƙarya kuma a bukaci mutane su nesanta kansu daga
gareta domin rashin amfaninta.
23. Kai
Bello yo niyya ka taimaki gaskiya,
Ƙarya ka watsash she ta don ba Ƙaruwa.
4.10
Rowa
A can baya sha’irin ya yi horo da a ɗabi’antu da yawaita taimako ga mutane. Bai tsaya
nan ba sai da ya yi dubi ga bukatar a guje wa rowa wadda ita ce akasin taimakon.
38.
Hali na rowa kun sani ai bai da kyau,
Mu yi
taimakon Alher fa ya ku ‘yan Uwa.
4.11
HaƘuri
Hausawa sukan ce maganin zaman duniya. Duk wanda
ya laƘanci yin haƘuri to ya sami kyakkyawar
shaida a rayuwa. Masu haƘuri su ke tabbatar da zaman lafiya a gida da gari
da kuma al’uma baki ɗaya. Lafazin da aka yi amfani
da shi a waƘar ya nuna fa’idojin yin haƘuri wanda horo ne ga mutane su ɗabi’antu da ita.
42. Mai hanƘuri shi ne dafarsa takan dafu,
Ko da ta dutsi ta yana shan romuwa.
4.12
Shawara
da Mutanen Ƙwarai
Neman mutanen Ƙwarai wajen yin shawara abu ne
da ke da muhimmanci ga mutum da al’umarsa. AlƘaali Bello ya jaddada wannan
horon da addinin musulunci ya yi a kan hakan.
49. Kai
Bello zan yin shawara to kajiya,
Ga
mutan Ƙwarai ita za ta gyara abubuwa.
50. Duk
wanda bai yin shawara ya karkace,
Ya
kauce hanya ba shi samun shiryuwa.
51. Aya
ta Ƙur’an ta yi horon shawara,
Sannan
a dorara gun gwani Mai basuwa.
Waɗannan kaɗan kenan daga cikin horon ayyukan alheri da aka yi
amfani da tubalansu wajen gina wannan waƘar.
5.0
Naɗewa
A wannan nazarin an yi ƘoƘarin tabbatar da tubalan da aka
yi amfani da su wajen gina waƘar Baje Kolin Hajar Tunani ta AlƘali Bello Giɗaɗawa. Waɗannan tubalan kamar yadda aka
ambata a farko, su ne na hani
da horo. Wato hani ga aikata
munanan ayyuka da kuma horon a aikata ayyuka
masu kyau. Duk wata kyautatuwa ta mutum ko ta al’uma ta dogara ne ga tsare
waɗannan ladubban. Sanin fa’idojin waɗannan ya sa Ɗangaladima ya yi amfani da
hikimarsa ta waƘa, ya mulmulasu a cikin Ƙananan tubalai na kalmomi ya faɗakar da mutane amma masu hankali. Ba wani tunani Ɗangaladima ya baje kolin hajarsa ba illa fito wa
jama’a da abin da ake ganin ba kyau da kuma horo ga aikata abin alheri.
6.0
Manazarta
Abdulkadir, D.
(1976) “The Role of Hausa Poet” a cikin Harsunan Nijeriya Vol. VIII
CNHN
Jami’ar Bayero,
Birnin Tudu, S. Y.
(2001) “Jigo da Salon
Asirin.”
Digiri na Uku Ph.D Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu
Danfodiyo,
Sakkwato.
Bunza, A. M.
(1986) “Tasirin Musulunci Cikin Rubutattun WaƘoƘin Hausa” Kundin
Digirin
farko, Jami’ar Sakkwato.
Furniss, G. L.
(1995) “Ideology in Practice: Hausa Poetry as Exposition of Values and
Viewpoint,”
Rudiger KÓppe Verlag KÓln
Furniss, G. L.
(1978) “The Application of Ethics in Contemporary Hausa Didactic
Poetry”
Cikin African Languages/Languages Africaine 4:127-139
Ibrahim, F. (1997) “Tarbiyyar Yara A Ƙasar Hausa” Kundi B. A. Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya da Na Afrika,
Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.
Muhammad, D ed (2006) Bargon Hikima Usmanu Danfodiyo University Press, Sokoto
Sa’id, B. ed (2006) Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, Ahmadu Bello University Press
Ltd.
Sokoto, A. B. G (1991) Baje Kolin Hajar Tunani Fadama Printing Works, Sokoto.
William, C. (1979)
How Does A Poem Mean?
Yahya, A. B. (1983) “A Critical Anthology of the
Verse of Alhaji Bello Giɗaɗawa” M.
A. Dissertation Bayero
University, Kano
Yahya, A. B. (1994) Jigon Nazarin WaƘa Fisbas Media Services, Kaduna.
Yahya, A. B. (2001) Salo Asirin WaƘa Fisbas Media Services, Kaduna.
Yahaya, I Y. ed
(1973) MaƘoƘin Hikima Oxford University
Press,
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.