Ticker

6/recent/ticker-posts

Ina Da Ulcer, Zan Rama Azumi Ne Ko Ciyarwa Zan Yi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam. Ina da ulcer kuma bana iya awa huɗu banci abinci ba kuma ina shayarwa zan iya ciyarwa ko inna warke zan rama kuma ana bina huɗu nabara ban rama ba ina laulayi anabina uku danace zan in ALLAH yabiyamin wata bukatata.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatallahi Wabarkatahu.

Toh anan abunda yake akanki shine idan ulcer dince tasa bazaki iya azumi ba toh bazaki ciyar ba jira zakiyi idan kin warke seki rama. Inkuma likitanki yace miki wannan irin ciwon naki bincike yanuna cewa ba'a cika warkewaba da ciwon ake mutuwa toh anan shine kawai seki ciyar kuma koda daga baya Allah yasa kin warke to bazaki ramaba. Amma idan ba don ulcer ɗin bane kika kasa azumin A'a ciki ne dake kokuma kina shayarwa shine yasa bazakiyi azumiba toh wannan kawai ciyarwane akanki bazaki ramaba.

Amma akwai saɓani domin wasu malamai suna ganin akasin abunda na faɗa, sedai kuma ni wannan shine na gamsu dashi kuma shine fahimtar me littafin Alwajiz fi fiqhis sunnah. Amma wadancan guda ukun wadanda ake binki na bakance toh sukuma wadannan bazaki ciyarba jira zakiyi inkin warke seki yisu. Inkuma har kika mutu bakiyiba toh magadanki zasuyi miki azumin ba ciyarwaba azumi zasuyi.

WALLAHU TA'AALA A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.