Ticker

6/recent/ticker-posts

Abinda Yake Kan Wanda Bazai Iya Azumi Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Meye abun da yake wajibi akan dattijo da bazai iya azumi ba, da mara lafiya da ba'a tsammanin warkewarsa??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Imam Bukhari Allah ya masa rahama yace "Amma tsoho mai girman shekaru da bazai iya azumi ba, Sahabi Anas ya ciyar da abinci bayan ya girma tsawon shekara daya ko biyu, akowace rana yana ciyar da miskini khubz da nama". Sahabi ibnu Abbas Allah ya masa rahama yana cewa gameda mutumin da ya girma bazai iya azumi ba zai ciyar akowane rana miskini guda ɗaya.

البخاري ٦/٣٠

Shaikh Ibnu baaz Allah ya masa rahama yana cewa "Abinda yake kan wanda bazai iya azumi ba saboda girman shekaru ko rashin lafiya da ba'a tsammanin warkewarsa ya ciyar da miskini guda ɗaya akullum idan zai iya, kamar yadda dayawa daga cikin Sahabbai Allah ya ƙara yarda dasu sukayi fatawa akai, daga cikinsu harda ibnu Abbas".

سبعون مسألة مهمة في الصيام

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments