Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Sha Azumi Saboda Shayarwa, Ciyarwa Zan Yi Ko Ramawa?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamou aleikoum, malam ina tambaya, ni ce na kasance na haihu wata daya kafin Ramadan, da Ramadan ya zo ban yi azumi ba, ban ma gwada ba ballantana in ga zan iya ko kuwa, kawai sai na fake da ciyarwa ban yi azumin ba, to malam ramkaci zan yi ko chiyarwa zan yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, Game da hukuncin mace mai ciki da mai shayarwar da suka sha azumi, malaman Musulunci sun yi saɓani game da abin da ke kansu na hukunci, shin ciyarwa za su yi kaɗai, ko ramawa kawai, ko kuma ciyarwa da ramawa?

Waɗannan zantuttuka guda uku, wanda ya fi rinjaye a cikinsu shi ne

Mai ciki da mai shayarwa idan suka sha azumi saboda kasawa ko tsoron kada su jigata, ko saboda tsoron kada abin da ke cikin nasu ya jigata, to abin da ke kansu shi ne za su rama wannan azumin ne da suka sha a lokacin da suka sami dama, ko da an sami jinkirin ramuwar saboda wata lallura. Saboda mai ciki da mai shayarwa ana riskar da su ne a cikin marasa lafiya da matafiyan da suka sha azumi.

Sheikh Abdul'aziz Bn Baaz ya ce: "Mai ciki da mai shayarwa hukuncinsu ɗaya da maras lafiya, idan azumi ya tsananta a gare su an shar'anta masu karyawa, ramuwa ta tabbata a kansu a lokacin da suka sami damar hakan, su kamar marasa lafiya ne, wasu daga cikin malamai sun tafi a kan cewa abin da ke kansu shi ne ciyar da miskini a kowace rana, sai dai wannan magana ce mai rauni wadda aka rinjaya. Abin da yake daidai a kansu shi ne za su rama ne kamar hukuncin matafiyi da maras lafiya , saboda faɗin Allah mai girma da buwaya da ya ce:

فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِیضًا أَوۡ عَلَىٰ سَفَرࣲ فَعِدَّةࣱ مِّنۡ أَیَّامٍ أُخَرَۚ

"Wanda ya kasance maras lafiya a cikinku, ko a halin tafiya, to sai ya rama a wasu ranaku na daban" (Suratul Baqara, aya ta 184.)

Duba Majmú'u Fataawá na Ibn Baaz (15/225).

Wannan ita ce fahimtar Fataawal Lajna a mujallad na 10 shafi na 220, kuma ita ce fahimtar da ta fi rinjaye a wurin mafi yawan malamai.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Post a Comment

0 Comments