Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Ake Fanke, Dibila, Alkaki, Nakiyar Shinkafa, Tsattsafa, Hikima, Cin-Cin, Kyak

Abubuwan Da Ke Ciki

Wannan rubutu yana ɗauke da bayanai game da yadda ake yin fanke da dibila da alkaki da nakiyar shinkafa da tsattsafa da hikima da cin-cin da ƙuli-ƙulin fulawa da kyak da kuma kyak ɗin ayaba. Kuna iya turo mana tsokaci ko tambaya a sashen comment da ke ƙasa.

Fanke

Kayan haɗin da za a tanada su ne:

i. Bakin foda

ii. Bota

iii. Fulawa

iv. Madara

v. Ƙwai

vi. Suga

Za a haɗa fulawa da madara da suga da bakin foda a kwaɓa su da ruwa. Daga nan sai a fasa ƙwai, sannan a narka bota a sanya su a ciki. Daga nan za a ɗ ora kaskon suyar ƙwai a riƙa ɗiba da ludayi ana zubawa yana gasuwa a hankali. Kada a bar shi wuta  ta yi mai yawa; idan gefe ɗ aya ya yi, sai a juya ɗaya gefen shi ma ya soyu.

Di ɓila (Dibila Ko Dibilon)

Kayan haɗin da za a tanada su ne:

i. Fulawa

ii. Mai

iii. Ruwa

iv. Suga

v. Yis

Fulawa da yis za a haɗe, sai a saka ruwa da mai a kwaɓa a niƙe su sosai kamar za a yi mitfayit, sannan a naɗa. Daga nan, sai a dafa suga da tsamiya  a saka a sama. Daga nan za a riƙa soyawa cikin mai. Bayan an kammala soya ta, za a narka suga sannan a riƙa tsoma shi a ciki. Wasu ma zuma suke sanyawa idan da hali.

Alkaki

Kayan haɗin da za a tanada su ne:

a. Alkama

b. Fulawa

c. Ruwa

d. Suga

e. Yis ko Nono mai tsami

Za a ɓarza alkama sannan a samu fulawa, sai a haɗe su tare da yis a kwaɓa kamar za a yi cincin. Za a ajiye shi sai ya tashi sannan a dunƙula da ƙarfi. Akan yi amfani da ƙarfe yayin dunƙula shi. Ana kiran sunan ƙarfen da ake dunƙula alkaki da shi aska. A maƙera ake samun sa. Bayan wannan  ya samu, sai batun suya. Bayan an kammala soyawa za a zuba dafaffen suga tare da tsamiya  a samansa.

Akwai kuma nau’in alkakin da ake samarwa ta hanyar niƙa alkama a inji. Akan saka nono a ciki a bar shi ya kwana. Bayan ya kwana, za a sake zuba ƙullin a turmi  a daka. Daga nan ne kuma za a yi masa ƙwaɓin alkaki.

Nakiyar Shinkafa

Kayan haɗin da za a tanada su ne:

i. Kayan yaji (citta, barkono/tonka)

ii.  Ruwa

iii. Ɗ anyar Shinkafa

iv.  Suga

v. Tsamiya ko lemon tsami

Da farko, za a wanke  shinkafar a bar ta har sai ta tsane sosai, sai a kai ta niƙa. Bayan an niƙa ta, za a tankaɗe da rariyar fura. A gefe guda kuwa, za a dafa suga sai ya koma kamar zuma. Daga nan sai a wanke turmin daka mai kyau, sai a saka garin tare da kayan yaji a ɗauko dafaffen sugan nan a zuba a turmi  a kirɓa. Za a riƙa daka ana zuba wannan  dafaffen suga har sai ya haɗe gaba ɗaya, sannan a kwashe. Za a iya sanya tsakin shinkafa ciki idan ana buƙatar ya ɗan yi tsaki -tsaki.

 Wasu kuma suna yin nakiyar gero  ko maiwa  ko ta dawa . Za a kai ta wurin ni ƙ a a ɓarza, sai a sanya garin a cikin tukunya  a aza bisa wuta . Daga nan za a riƙa juya garin sannu a hankali har sai ya soyu. Za a sanya tsamiya  ko lemon tsami  a haɗa da suga a yi ta motsa shi har sai ya fara yauƙi, sai a haɗa da soyayen garin a kwaɓa.

Tsattsafa

Kayan haɗin da za a tanada su ne:

i. Bakin foda

ii. Fulawa

iii. Mai

iv. Ruwa

v. Suga

Za a haɗa fulawa da suga da bakin foda, sannan a kwaɓa su tare da ruwa. Za a yi kwaɓin ruwa-ruwa. Ita tsatsafar ba a barin ta ta tashi kamar sauran. Da an kwaɓa ta za a fara soyawa. Daga nan sai a hura wuta  a saka mai a tukunya . Idan ya yi zafi , sai a ɗauko gwagwa a ɗora ƙulun a kai, ruwan ƙullun za su shiga cikin mai ɗigo-ɗigo. Za a riƙa yi ana juyawa domin ɗigon su haɗe wuri ɗaya. Za kuma a riƙa yi ana juyawa. Bayan an kammala suya za a daka suga a zuzzuba a kai.

Hikima

Kayan haɗin da za a tanada su ne:

i. Bakin foda

ii. Fulawa

iii. Mai

iv. Ruwa

v. Suga

Za a haɗa fulawa da bakin foda (baking powder) da suga a wuri ɗaya, sannan sai a saka ruwa a kwaɓa. Daga nan sai a ɗora mai a wuta . Za a a riƙa ɗaukar ƙarfe ana sakawa cikin mai. Idan ya yi zafi , sai a saka cikin ƙullun a mayar cikin mangyaɗa a soya.

Cin-Cin

Kayan haɗin da za a tanada su ne:

i. Bakin foda

ii. Bota

iii. Fulawa

iv. Madara ta gari

v. Mai

vi. Ƙwai

vii. Ruwa

viii. Suga

ix. Yis

Za a haɗa fulawa da ƙwai da madarar gari  da suga da bota da kuma yis, sai a kwaɓa su da ruwa, amma ba sosai ba, ma’ana sama-sama za a sanya ruwan. Daga nan za a bar shi har sai ya kumbura, sannan a ɗauko a yayyanka. Da zarar an gama yankawa  sai batun suya.

Ƙuli-Ƙulin Fulawa (Doughanut)

Kayan haɗin da za a tanada su ne:

i. Fulawa

ii. Gishiri

iii. Mai

iv. Ƙwai

v. Ruwa

vi. Suga

vii. Yis

Za a zuba yis da suga da ruwa kaɗan a juya. Idan kuma ba a buƙatar haka, sai a dafa ruwan zafi  a zuba yis ɗin da suga a ciki a ajiye gefe. Sannan sai a ɗauko fulawa a zuba gishiri kaɗan, sai a kawo ruwan da ke haɗe da yis da suga a zuba cikin fulawa a kwaɓa. Idan ya kwaɓu, za a iya saka mai a ciki a sake kwaɓa shi don ya yi laushi sosai. Daga nan za a bar shi a wuri mai zafi ya ɗan tashi, sai a ɗauko shi a mulmula kamar ƙwallo a aje a gefe. Idan an iya yi, za a samo kwalba a saka bakinta a tsakiya, inda nan za ta cire tsakiyar ƙwallon da aka mulmula. Hakan zai ba da damar a huda tsakiyar. Za a hura wuta  a aza tukunya  da mai a soya. Idan ɓ angare ɗ aya ya soyu, sai a juya ɗaya ɓangaren shi ma ya soyu.

Kyak (Cake)

Kayan haɗin da za a tanada su ne:

i. Bakin foda

ii. Bota

iii. Fulawa

iv. Madara

v. Ruwa

vi. Suga

A samo roba mai girma, sai a zuba bota da suga a kwaɓe su sosai har sai sugan ya narke tare da botan. Sai kuma a ɗauko ƙwai a fasa a ciki, sannan a ci gaba da juyawa har sai ya haɗe wuri guda. Daga nan sai a zuba a roba a saka bakin foda da madara da kuma fulawa a ciki a juya sosai. Da zarar wannan  ya samu, sai a ɗauko haɗin ƙwai da suga da bota da tuni aka kwaɓa a zuba a ciki, sai a ci gaba da juyawa har sai sun haɗe sosai. Sannan a nemi gwangwani ko obun na gasa kyak a zuba a ciki. Kafin a zuba, za a riƙa shafa bota da ɗan wani ƙyalle. Har wa yau, za a shafe cikin obun ko gwangwanin da ake aikin da shi. Idan ya dafu, za a ga hayaƙi ya taso da ƙamshi ko’ina.

Kyak na Ayaba

Kayan haɗin da za a tanada su ne:

i. Ayaba

ii. Bakin foda

iii. Bota

iv. Busasshen dabino

v. Busasshen inibi

vi. Fulawa

vii. Gishiri

viii. Madara

ix. Ƙ wai

x. Ruwa

xi. Suga

A tashin farko, za a ɓare ayaba kamar guda shida, sai a markaɗe a bilanda. A gefe guda kuwa, an fasa ƙwai guda takwas wa ɗ anda za a haɗa da bota a roba ɗaya tare da suga rabin gwangwani. Sannan za a zuba gishiri rabin cokali ɗaya a juya sosai a yi ta buga shi har sai ya narke. Daga nan, sai a sanya busasshen  dabinon da aka cire ƙwallon aka gutsuttsure tare da busasshen inibi, sai a juya su a zuba fulawa a kwaɓa asake bugawa sosai. Daga nan sai a shafa mai a gwangwanayen yin kyak a riƙa zubawa ana sakawa ga obun domin gasawa. A wani nanzari ba gudu ba, akan iya yin sa kan tukunya . Za a iya gane ya nuna ta hanyar jin ƙamshinsa ko kuma ta hanyar sanya tsinke a cikinsa. Idan ya nuna, za a ga ƙullun bai maƙale a jikin tsinken ba.

Citation (Manazartar Littafin):   Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments