Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Wakar Bello Gedawa Ta Tsaro

 Takardar ƙara wa juna sani da aka gabatar a ajin ALH 400: Seminars, a Sashen Nazarin Harsuna Da Aladu, Jamiar Tarayya Gusau, Nijeriya, (2022/2023 Academic Session).

Federal University Gusau (FUG) Nigeria

Nazarin Wakar Bello Gedawa Ta Tsaro

NA

MUSTAPHA YAKUBU

LAMBAR WAYA: 07067899456

Email: Mustaphayakubu202020@gmail.com

Tsakure

manufar wannan binckiken ita ce nazarin ƙwaƙƙwafi domin jigo da salo da kuma gano tasirin da wakar bello geɗawa ta tsaro tayi wajen kawo cigaba a harkar tsaro. An dora aikin kan fahimtar hausawa ta “hausa ba dabo ba ”, sakamakon biciken ya gano tasirin waka a cikin al’umma hausawa, da kuma banbance-banbancen da ke akwai a tsakanin rubutattun wakoki da kuma wakar baka.

Gabatarwa

takaitaccen tarihin wanzuwar rubutattun waƙoƙin hausa shi ne binciken yi tsokaci a kai kasancewar aikin akan rubutacciyar waka yake.

rubutacciyar waka ko kuma ince rubutattun wakokin hausa abu ne mai gajeren tarihi zuwa yanzu watakila babu aibi idan aka ce shekarun da aka fara nazarin rubutattun waƙoƙin hausa ba su wuce kirga su cikin sauki ba.

wata kilama a takaitasu zuwa lokacin zuwan turawan mulki. a lokutan baya mutane ba su damu da yin nazarin waƙoƙin ba, illa kawai su karanta ko su juye su da hannu ko su saurara domin nishadi ko don jin wani saƙo ko wata manufa.

bayan ma’anar rubutacciyar waka binciken bai tsaya iya nan ba zai zaƙulo muna jigo da salonda dake cikin waƙar tsaro ta bello geɗawa wanda shi ne makasudin wannan binciken.

1.1 Dabarun gudanar da bincike

wannan bincike ne wanda ke da tsarin tsurar bayani (qualitive form of

research).

an yi amfani da lura (observation) a mastayin babbar hanyar tattara bayanai daga tushe na farko (primary source) zuwa babbar hanyar tattara bayanai daga majiya ta biyu (secondry source) da ke yin amfani da ita ta kasance binciken rubuce-rubucen magabata

bayan haka an yi amfani da hira (interview) a matsayin hanyar tabbatar da ingancin bayanai.

an samu bayanai game da wadansu rassa na rubutacciyar waƘa daga malamai masana adabi.

1.2 Waka kadadar bincike

anan yakamata mu tuna cewa waƙoƙi iri biyu ne: rubutacciyar waƙa da waƙar baka ta maƙaɗa. mecece waƙa? waƙa wani saƙone da aka gina shi kan tsararriyar ƙa’ida ta baiti, dango, rerawa, kari(bahari), amsa-amo(kafiya), da sauransu ƙa’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, zaɓensu da amfani da su cikin sigogiin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba..

abdulƙadir dan gambo (2007) daurayargadon fyede waƙa. haka kuma bayan yahya ya kawo ma’anar waka a cikin littafinsa mai suna “ jigon nazarin waƙa ” ga kunnuwan bahause (anan ana nufin wanda ba mawaƙi ba, ba kuma masani ko manazarcin waƙa ba) kalmar waƙa tana kawo masa tunanin maganar da ake rerawa wadda ke da dadin ji har ga zuciya, mai fayyace gaskiya kuma mai kawo nishadi. magana ce da ake shishshirya kalmominta cikin a zanci, ta yarda wajen furtawa ana iya amfani da kayan kiɗa, wayennan kayan kiɗa suna iya kasancewa kalangu ko ganga ko kwarya ko hannuwa ko ma bugawar zuciya.

wannan kuma nau’i ne na ma’anar waƙar baka, domin waka rubutacciya ba ta zuwa da ƙida lokacin rera ta.

ta bangaren mawaƙa kuma suna ganin wadansu kalmomi ne da aka ƙuƙƙullasu a cikin a zanci.

2.1 Salo

salo yana nufin dabara ko wayo wanda mawaƙi zai iya amfani dashi wajen jawo hankalin jama’a, yayin isar da saƙonsa, hakan ya sa biciken zai iya gano mana cewa

1)      salo wani yanayi ne da ya ƙunshi zaɓi cikin rubutu ko furuci

2)       salo ƙari ne na daraja /armashi a cikin rubutu ko furuci.

da yake an ce dabara ce ta ke isar da saƙo ya sa mawaƙa suna dabara masu yawa domin cusa sha’awa da jin daɗi ga mai karatu, ko sauraren waƙoƙinsu.

ta hakane kuma zaisa a fahimci irin saƙon da ake son sadarwa daga ciki a kwai

·         Kwatantawa

 ita ce hanya ta kwatanta abu biyu domi a banbance irin. dangantakarsu.

·         kamantawa : dabarace ta kwatanta abubuwa biyu ko fiye da haka masu halayya iri daban-daban a kwatantasu wannan kwatance zai iya zama na dai dai ne ko kuma na fifiko

 ana amfani da kalmomin dai-dai irinsu

 (1) kamar

 (2) sai kace

 (3) iwa (4) daidai

 (5) tamkar da sauransu.

sai salo na fifiko shi kuma kamance ne in da za a fito da wani abu ace yafi wani.

kalmomin da ake amfani da su a fifiko sune

v  wane

v  ya zarce

v  yafi

v  ya shiga

v  tafi

Sai salon kasawa

shi kuma wannan salo ne da mawaƙa ke yin amfani da shi ta hanyar kwatanta abu biyu ko fiye da haka su ce dayan bai cimma dayan ba.

kasancewar binciken zaifi karfi ne akan jigo hakan ya sa ba’a buda sosai a kan salo ba sai a dubi littafin bayaro yahya mai suna “salo asirin waka”

2.2 Jigo

jigo saƙone mai manufa ko abin da waƙa ta ƙunsa, wato abin da take magana akai ana gano jigo ne ta hanyoyi guda uku wayennan hanyoyin uku sune

1.0  furucin gundarin jigo : ƙwayar jigo da ake iya samu ƙunshe a kan baitocin waƙa da ke iya ba da tabbacin manufar marubucin

2.3 Jigo a gajarce

wurine da ake taƙaita abin da mawaƙi ya faɗa baiti bayan baiti, ba tare da yin sharhi ko ƙarin bayani ba.

3.0 Tasirin waƙa

waƙa na da matuƙar tasiri da muhimmanci a cikin al’umma, saboda hanya ce ta isar da saƙo kai tsaye kuma cikin sauƙi, wacce jama’a za su iya jurema dogon lokacin da za’a ɗauka ana isar da shi, matukar an yi amfani da salo mai ƙayatarwa.

ba lalle ne ba a ɗauki lokaci mai tsawo ana jiran mutum ya isar da saƙo nai ba, amma ta hanyar amfani da waƙa wajen isar da saƙo za’a iya jimirin jinsa har i zuwa ƙarshe.

3.1 muhimmancin tsaro ga al'umma

 tsaro na nufin kiyaye rai da lafiya da kuma dukiya game da salwanta. hakan ya sa tsaro ya zamnato rayuwa gun al’umma, kasancewar babu wata al’umma da zata iya rayuwa ba tare da tsaro ba. muhimmancin hakan ya sanya "bello geɗawa" yayi waƙarsa ta tsaro a cikin wannan lokacin da muke ciki na rashin tsaro a jaha domin samu gyara da mafita a cikin ƙasa.

3.2 Babban jigon waƙar

duba da yana yin hanyoyin na zarin da an kai amfani da su biciken ya nuna muna babban jigonn wannan waƙar ta "bello geɗawa" shi ne tsaro, haka kuma tana da baiti arba’in da takwas, an shirya ta ne bisa ta farkin ɗango biyar. a baiti na biyar tun a ɗangon farko ya fito da jigon waƙarsa ƙarara, in da ya ce matsalar tsaro a arewa gida hudu zani tattaunata bt-5 rashin tsaron kuma kansa nauo’insa zan lissafata. ɗango na uku duk dai a baiti na biyar.

 Ƙarshe zani bayyana mafita kan matsalar tsaro a arewa. ɗango na biyar duk dai a baiti na biyar baiti na shida duk yan kunanan in ka duba babu tsaro a cikin ta arewa. ɗangon karshe na baitin bt-38 ɗango na biyu sanadiyar wannan rashin tsaro a arewa ya shafi kowa.

bt-47 ɗango na hudu, a tabbatar da tsaro a arewa yanda mutane zasu wadata.

bt-48 babban burinsa a wannan waƙa a tabbatar da tsaro a arewa.

wadannan sune wuraren da anka samu,

jigon wakar babba wanda akansa anka shirya waƙar, bayan wannan babban jigon tana da kananan jigogi kamar haka

o   nishaɗi

o   faɗakarwa

o   hannunka mai sanda

o   da kuma tanbihi.

3.3 Kananan sigogi

1)      nishadi waƙar ta nishaɗantar sosai ta hanyar amfani da kalmomin sokotanci da mawaƙin yayi amfani dasu da kuma salon saɓi zarce wajen isar da saƙonsa cikin sigogin hikima tare da rera ta cikin sanyayayyar murya wandawayennan sune mabuɗan da zasu sa mai saurare jin nishaɗi kasancewar an rerata akan murya mai da taushi.

2) fadakarwa mawakin

mawaƙin ya fadakar sosai ta in da yace “yan arewa su farko a bacci domin in basu tashi tsaye ba to arewa zata rushe wannan jan hankaline da fadaƙarwa yakeyi a baiti na 28.

3.4 Rumbun kalmomin bello geɗawa

mawaƙin yayi amfani da yawaitar kalmomi ta hanyar yin yawa cikin kare-karen harsuna in da yayi amfani da harshe daban-daban a cikin waƙarsa, domin ya samu walwalar harshe wanda zai sa sakon ya isah cikin gamsarshiyar hanya.

 4.0 Nason jigon waƙa

wannan shi ne nason da jigon waƙar yayi ta ta hanyar babban jigon "tsaro" duk ya nashe kananan jigogin, daga bisani kuma ya yi ɗauraya wadda ta sanya an samu ganin ƙananan jigogin.

haka zalika yana da kyau a banbance tsakanin rubutacciyar waƙar da kuma wakar baka. ta makaɗa duk da yake suna kamanceceniya a wani guri amma a kwai inda suke saɓawa kasancewar ita rubutacciyar waƙa tana tafiya ne bisa tsarin kafiya da kuma baiti.

yayin da wakar baka ba ta tafiya da wannan tsarin, suna kamanceceniya amma ta fuskar kari (bahari) kowace waƙa daga cikin biyu din ba sa reruwa ba tare da an daidaita kariba.

 5.0 Sakamakon bincike

sakamakon binciken ya gano tasirin waƙa a cikin al’umma da kuma muhimmancinta da kuma rabe-rabenta haka kuma biciken ya gano kamanci da kuma rashin kamanci dake cikin rubutacciyar waƙa da kuma waƙar baka ta maƙada. binciken ya nuna a rubutacciyar waƙa ba a sanya mata kiɗa ya yin da wakar baka ake sanya kiɗa ya yin gudanar da ita

 5.1 Kammalawa

sakamakon wannan bicike ya ci karo da hasashen da binciken yayi tun farko.

hasashen da aka gina na son farko da “yan uwana ɗalibbai kan nazarin waka",, domin fito da waɗansu abubuwa wanda shi kansa marubucin bai san lalle ne ya fito da suba.

 

Post a Comment

0 Comments