Ticker

6/recent/ticker-posts

Daukar Ma’aikatan Sa-Kai Don Samar Da Tsaro A Zamfara

 Takardar ƙara wa juna sani da aka gabatar a ajin ALH 400: Seminars, a Sashen Nazarin Harsuna Da Aladu, Jamiar Tarayya Gusau, Nijeriya, (2022/2023 Academic Session).

Federal University Gusau (FUG) Nigeria

Daukar Ma’aikatan Sa-Kai Don Samar Da Tsaro A Zamfara

DAGA

SHARHABILU YA’U

LAMBAR GSM: 08146898484

IMEL: babanummee91@gmail.com

TSAKURE

Wannan muƙala ta mayar da hankali ne kacaukan ga yabo da faɗakarwa ga wasu daga cikin muhimmanci ma’aikatan sa-kai, tare da muhimman ayyukan da suka rataya a kansu, wanda hausawa ke cewa rashin uwa kan sa ayi uwar ɗaki, a kan haka ne aka yi bitar ayyukan magabata da suke da alaƙa ta taƙud-da-ƙud, tare da bibiyar ayyukan ‘yan sa-kai. A wurin tattara bayanai an yi amfani da dabarun bincike iri biyu, na tsaye da na zaune, wato bitar bugaggun litattafai da kundayen bincike – bincike a ɗakunan karatu, sai kuma dabara ta biyu wato ta tsaye, neman bayanai a kan aikin sa-kai birni da ƙauye wajen shuwagabanni, ma’aikata da kuma hukumomin da nauyin aikin yarataya a kansu tare da ziyarar gani da ido a wajen sarakuna, jami’an gwamnati, duka dai domin a samu ingantaccen sakamakon binciken.

1.0              GABATARWA

Kalmar tsaro a taƙaice, tana nufin ba da cikakkiyar kariya ga mutane, dukiya, gari, ƙasa da duniya baki ɗaya. Tarihi ya nuna cewa tsaro ya samo asali ne tun farkon lokacin da mutane suka fara wanzuwa a duniya matsayin ƙabila ta yanda suka ƙirƙiri garinsu da shugabanninsu da za suyi masu shugabanci da ba da umarni da hani tare da yin hukunci.

Tsaro shi ne ginshiƙin kowace al’umma da ƙasa baki ɗaya a duniya, shi ya sa ko a wannan ƙarnin da muke rayuwa, ƙasashen da suka fi ƙarfi da cigaban zamani na rayuwa sune ƙasashen da suke da wadataccen tsaro a cikin ƙasashen su. Shi ya sa duk wani shugaba da ya san mai yakeyi, farkon abinda zai fara ingantawaa ƙarƙashin shugabancinsa, shi ne tsaro domin sai tsaro ya inganta kafin a samu cigaba a cikin ƙasa da duniya baki ɗaya.

1.1              DABARUN BINCIKE

Domin ɗora wannan bincike ga sahihiyar hanya ne, ya sa aka yi amfani da hanyoyin tattara bayanai kamar haka

              i.       Bitar ayyukan da suka gabata

  ii.          Neman bayanai ta hanyar ziyarar gani da ido

iii.          Karance – karancen bugaggun litattafai

iv.          Nazarin kundayen bincike da maƙalu

  v.          Nemo waɗansu labarai na harkar tsaro daga wajen wasu shugabanni da jami’an sa-kai, ta amfani da wayar salula da kuma ziyarar kai tsaye.

2.0           WAIWAYEN KALMAR TSARO

 Kamar yadda wani masani a cikin ra’ayin aminiya ya faɗa cewa, ‘‘tsaro a ƙasa babban nauyi ne da ya rataya a kan kowace gwamnati dake kan mulki, ta yadda zata ɗauki nauyin al’umma a kowane bagire na rayuwa’’.

 Tsaron al’ummar ƙasa yana da ma’ana mai faɗi ƙwarai, jin daɗin jama’a ta hanyar gudanar da al’adunsu da sana’o’insu da sauran shirye-shiryen rayuwa ba tare da tsangwama ba, alama ce ta kyakkyawan tsaro a ƙasa, samun wannan kwanciyar hankali ba tare da tsoron kawo hari daga wani wuri ba, shi ne zai sa ƙasa ta cigaba musamman ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, da noma, da ilimi, da fasaha, da kimiya wanda da su ake tafiyar da harkokin duniya a halin yanzu.

 Idan an yi maganar tsaro, akasarin jama`a za su fahimci tsari daga kawo hari daga waje ko cikin gida. Wannan haka ne, amma kuma a cikin ƙasa ma akwai matsaloli da dama waɗan da sukan janyo babbar ɓaraka ga sha`anin tsaro.

 Daɗin-da-ɗa-wa kamar matsalar da ta addabi ƙasar nan da yankin-arewa maso yamma ƙasar a kan harkar tsaro, misali kamar haka: Faɗan kabilanci, rikicin addini, rikice-rikicen siyasa, yan fashin daji (yan bindiga) masu garkuwa da mutane, ɓarayin shanu da kuma shigowar baƙin haure a ƙasa. Saboda a tabbatar da zaman lafiyar jama`a, gamnati ta kafa hukumomin tsaro iri-iri a fadin kasar. Misali kamar: sojoji da yan sanda da kwastom da ma`aikatar shige da fice (immigration) da hukumar gidajen yari (prison) da DSS da NIA da NDLEA da EFCC da FRSC da NSCDC.

2.1           HUKUMAR TSARON CIKIN ƘASA(SSS)

Wannan ita ce hukumar tsaro ta cikin gida, tana da rassa a ko ina a jahohi da ƙananan hukumomi, baban ofishin ta yana Abuja. Harkokin da suka shafi sharri da kalamai marassa tushe don a janyo wa gwamnati baƙin jini da ɓarna a tattalin arzikin ƙasa da tayar da tarzoma. Babban aikin wannan hukuma shi ne, ta hango manyan laifuka ta hanyar bincike ta kuma hana faruwar su.

2.2           HUKUMAR SOJA

 Dokar soja da ta kafa hukumar tsaron cikin kasa ta ba ta ikon daukar matakan da suka dace, waɗan da dokokin ƙasa suka yarda dasu wajen gudanar da bincike da kuma mutanen da suke da laifi, domin a gurfanar dasu a kotuna don ayi hukunci. Haka ma hukumar tana da shirye- shirye da tsare-tsare waɗan da zasu ba ta dammar cimma burin tafiyar da ayyukan ta cikin nasara.

2.3                             HUKUMAR TARA BAYANAN TSARO A ƘASASHEN WAJE (NIA)

 Ita kuma hukumace ta tsaro dake kula da laifuka da ake yi wa Nijeriya a ƙasashen waje. Idan an samu wasu suna buga kuɗaɗen jabu don su shigo dasu ƙasa, aiko da gurɓatattun magunguna a cikin kasa domin a yiwa mutanen mu illa, ɗaukar sojojin haya domin su kawo wa ƙasar mu hari, baiwa mutanen Nijeriya tirenin irin na soja don su koma ‘yan ta`adda a cikin kasa tare da nema masu makamai, yin ɗabi`u marassa kyau a cikin ƙasa kamar, sace-sace, ta`addanci, kasha-kashe, kidinafin, shigo da muggan makamai duk nauyi ne daya rataya a kan wannan hukumar domin magance waɗannan laifukan a cikin ƙasa.

2.4           HUKUMAR TATTARA BAYANAN TSARO (DIA)

 Ita ma wannan hukuma ce ta sojoji, wadda ke kula da tsaro, tana ai`kawa da mutanen ta ƙasashen waje don su tattara bayanai kan al`amurran dake faruwa a duniya na harkokin tsaro, waɗan da suka haɗa da sababbin makamai da aka ƙera da kuma samu cigaba ta hanyar kimiya da dabarun yaki. Wannan hukuma tana kula sosai da irin waɗannan al`amurra, ma`aikatan hukumar a gida da waje sun haɗa da farar hula da sojoji.

2.5           HUKUMAR TARA BAYANAN SIRRI TA SOJA (DMI)

 Wannan hukuma ta sojoji ce tana kula da halayyar su baki ɗaya domin a tabbatar babu wata ɓaraka ta tsaro. Hukumar ta kasu gida uku, akwai ɓagaren sojojin ƙasa, na ruwa dana sama. Kowace akwai tsarin da take bi kuma shuwagabannin su sukan haɗu su dai-daita matakan tsaro a bisa labaran da ake samu. A kullum a shirye suke wajen samun horo da dabarun yaƙi don kare al’ummar ƙasa.

2.6           HUKUMAR TSARON FARIN KAYA (NSCDC)

 Muhimmanci tsaro shi ne a samar da walwalar al’umma. Wannan hukumar an kafa ta ne da niyyar tallafawa tsaro ta hanyar koyarwa da taimakawa jami`a, matakan da za su ɗauka don tsiratar da al’ummar ƙasa daga haɗurran da za su iya janyo mutuwa. Haƙƙin hukumar ta koyawa kamfanoni tsare-tsaren tsaro na zamani, domin rage munanan ayyuka da suke kawo cikas ga tsaron ƙasa.

 Daɗin-da-ɗa-wa, duk da irin waɗannan hukumomin da gwamnatin ƙasar take dasu an kasa magance matsalar tsaron da addabi ƙasar, sha`anin tsaro sai ƙara tabarbarewa yakai musamman a arewacin ƙasar. A sanadiyar haka ne, wasu gwamnoni a yankunan ƙasar suka bada ƙaimi wajen samar da jami`an tsaron sa-kai a yankunansu domin samar da ingantaccen tsaro da samar da dauwamammen zaman lafiya ga al’ummarsu da ƙasa baki ɗaya. Waɗannan shuwagabannin jihohin sun haɗa da: gwamnan jihar Katsina (Dr. Umar Dikko Raɗɗa) da gwamnan jihar Zamfara (Dr. Dauda Lawal Dare) da gwamnan jihar Sokoto (Ahmadu Aliyu). Duka waɗannan jahohi guda uku suna maƙwaftaka da juna, sune waɗan da harkar rashin tsaro ke cima tuwo a ƙwarya, rashin tsaro ya addabesu a kodayaushe harkar tsaron jahohin sai ƙara taɓarɓarewa takai saboda haka ko wannen su ya yanke shawarar ɗaukar ma`aikatan sa-kai domin taimaka ma jami`an tsaron ƙasar nan domin samar da zaman lafiya a yankunansu da ƙasa baki ɗaya.

 Binciken aikin mu ya karkata ne a kan muhimmancin ɗaukar jami`an tsaron sa-kai da gwamnatin jihar Zamfara ta ƙaddamar a faɗin ƙasar ta domin sama al’ummar ta zaman lafiya da kariyar dukiyoyin su.

3.0           KALMAR SA-KAI

 Yin wani abu na taimako ga wani ko al`ummar ko aiwatar da wani aiki ba tare da bin wani umurni ba na wani ko ansar na goro don aiwatar da abin domin biyan ka kuɗin aikin ko taimakon da kayi.

3.1           YAN SA-KAI

 Wato hukumace ko ƙungiya da matasa ko al’ummar suke haɗuwa su ƙiƙirata a cikin jama`ar su domin kariyar kansu da al’ummar su da yankunan su da garuruwan su da dukiyoyin su daga wajen ‘yan ta`adda, ‘yan bindiga daɗi, ‘yan fashin daji da kuma masu garkuwa da mutane domin ansar kuɗin fansa. Wannan ƙungiya ta sa-kai ma`aikatanta suna bayar da tsaro a yankunan su ba dare ba rana domin kariyar jama`a da tabbatar da zaman lafiya a kodayaushe.

4.0           GURBIN ‘YAN SA-KAI A ZAMFARA

           i.         Domin taimakama jami`an tsaron a jahar Zamfara.

        ii.         Daukar tsawon lokaci da aka shafe jihar tana fama da matsalar rashin tsaro.

      iii.         Domin samun nasarar gwamantin jihar na bayar da tsaro.

      iv.         Domin kariyar al’umma nan take, na harin ‘yan bindiga.

         v.         Samar da ingantaccen tsaro, don kawar da ta’addanci a Zamfara.

4.1 DOMIN TAIMAKAMA JAMI`AN TSARON A JAHAR ZAMFARA.

 Babu shakka jahar Zamafara ta ɗauki tsawon shekaru da lokutta tana fama da matsalar tsaro, jaha ce wadda ‘yan fashin daji suka mai da ita tudun mun tsira, wato sansaninsu inda suka mamaye yankunan ƙasar baki ɗaya. Da yawa yankunan ƙasar Zamfara suna ƙarƙashin ikon su, sanadiyar haka ne gwamnatin jahar ƙarƙashin jagorancin gwamnan jaha “Dr. Dauda Lawan Dare” ya ɗauki aniyar kawo ƙarshen ta`addanci a faɗin jahar, tare da ɗaukar ma al’ummar jahar alƙawali cewa, zai yi iya bakin ƙoƙarin shi wajen gani ya kakkaɓe du wani ta`addanci da ‘yan fashin daji suk yiwa jama`ar birni da ƙauyukan jihar Zamfara. Tare da kawo masu zaman lafiya a Zamfara da arewa haɗi da ƙasa baki ɗaya don haka ne majalisar jahar tare da gwamnan jahar suka aminta da daukar ma`aikatan sa kai a yankunan jahar domin haɗa hannu da jami`an tsaro wajen taimaka masu a kan matsalar tsaron da ta addabi yankin. Suna da matuƙar muhimmanci domin sune suka san lungu da saƙo na maɓoyar ‘yan ta`addar.

4.2 TSAWON LOKACI DA AKA A NA FAMA DA MATSALAR RASHIN TSARO.

 A sanadiyar haka ne, gwamnati jahar ta ɗauki sabon salo na ɗaukar jami`an sa-kai domin ɗaukar tsattsauran mataki ta yin amfani da Yaren da yan bindigar suke ji, ta wannan hanyar ne da gwamantin jahar ta ɗauka al’ummar jahar suke farin ciki suna ganin cewa ita ce hanyar tudun mun tsira ga al’ummar jahar Zamfara. Saboda suna ganin irin wannan mataki ne maƙwafciyar jahar su ta ɗauka kuma sun ga kwalliya ta biya kuɗin sabulu a cikin jahar, wato jahar Katsina ta ɗauki wannan mataki ne saboda tana ɗaya daga cikin jahohin dake fama da matsalar tsaro. Saboda haka gwamnatin jahar Zamfara tabi sahun takwarar ta jahar Katsina ta ɗauki ma`aikatan sa-kai a faɗin jahar domin ganin irin tsawon lokacin da jahar ta dauka tana fama da matsalar tsaro. al’ummar Zamfara sun ɗauki tsawon shekaru suna fama da matsalar ‘yan fashin daji na sace-sace da ɗaukar mutane tare da hana al’umma noma gonakinsu da kuma fargabar da al’ummar jahar suke ciki wajen hulɗar kasuwanci da sana`o`insu na yau da kullum. Da irin waɗannan matsaloli ne gwamnatin jahar ta yanke shawarar ɗaukar ma`aikatan sa-kai saboda suna muhimmancin gaske domin su zama jagorori ga jami`an tsaro wajen shiga lungu da saƙo na dazuzzukan jahar don kawo ƙarshen ta`addanci a faɗin jahar.

4.3 DOMIN SAMUN NASARAR GWAMANTIN JIHAR NA BAYAR DA TSARO.

 Sanin kowane a wannan kasar irin halin da jahar zamfara take ciki ba bakon abu ko ɓoyayyen abu wato rashin tsaron da take fama da shi kamar yadda hausawa ke cewa “idan ana babbakar giwa ba`a jin ƙaurin kusu” jahar Zamfara jaha ce wadda ta zarta kowace jaha a faɗin ƙasar shiga halin rashin tsaro. Hasali ma gwamnatin jahar tana tuƙa ana walwala a kan sha`anin, sanadiyar haka ne ta yanke shawarar ɗaukar ma`aikatan sa kai domin taimakamata wajen shawo kan matsalar tsaro, saboda ganin ta cimma cikar burinta na samar da zaman lafiya a faɗin jahar ganin yadda gwamnatocin baya suka yi da ‘yan ta`addan ta hanyar yin sulhu tsakanin su da su amma kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba duk da irin da ɗaɗa masu da sama masu walwala a cikin al’umma da cika masu dukkan alƙawullan da aka dauka a lokacin yin sulhun, amma duk da haka sun kasa riƙe alƙawalin sun karya alƙawullan da aka yi dasu tsakanin su da gwamnonin na wancan lokacin wato gwamna Yari da gwamna Matawalle sanadiyar haka ne gwamnatin Dr. Dauda Lauwal ta ɗauri ɗa marar ɗaukar jami`an sa-kai domin horar dasu dabarun yaƙi saboda tunkarar ‘yan ta`adda waɗan da suka dami al’ummar jahar. Domin su taimaka wajen yaƙar ‘yan fashin dajin tare da jami`a tsaro.

4.4 DOMIN KARIYAR AL’UMMA NAN TAKE, NA HARIN ‘YAN BINDIGA.

 Sanin kowa ne irin halin da jahar nan take ciki jami`an tsaron ƙasar nan da ake kawo wa a yankin, saboda ƙamarin da rashin tsaro yayi ba za su iya magance wannan matsalar ba nan take saboda irin tsawon lokaci da matsalar ta ɗauka amma an kasa shawo kan lamarin nan take. Bahaushe na cewa, “da ɗan gari kan ci gari” tabbas wannan magana gaskiya ce, sanadin haka ne gwamnati tare da majalisa suka aminta da ɗaukar ma`aikatan sa-kai a cikin jahar domin kawar da matsalar tsaron jahar. Wannan lissafi da gwamnatin jahar ta yi na ɗaukar jami`an tsaro na sa-kai, duba da cewa sune waɗan da za su tsare yankunan su da kuma jiran jira kodayaushe domin tunkarar yan fashin dajin sune waɗan da suka san hanyoyin da ‘yan bindiga suke biyowa domin kawoma garuruwa hari ta hakane gwamnatin ta ɗauke su domin kariyar al’umma da yankunansu don su riƙama jami`an tsaron ƙasa aiki na kare al’umma

4.5 SAMAR DA INGANTACCEN TSARO, DON KAWAR DA TA’ADDANCI A ZAMFARA.

 Irin yadda wankin hula yakai al’ummar jahar Zamfara dare, dangane da harkar rashin tsaro yayin da ‘yan bindiga suke yin abinda suka ga dama ta`addanci sai ƙara ta`azzara yakai a faɗin jahar. Sace al’umma garesu ba komai ba ne, kashe rayukan jama`a da kuma sace dukiyoyinsu ba dare ba rana a garuruwan Zamfara tare da yin gudun hijar ga al’umma domin tsirar rai da kwaucewa muggan hareharen su. Musamman irin tashe-tashen hankullan da gwamnatin jaha ta yanzu ta tsinci jahar a ciki na kashe – kashe da sace – sace da garkuwa da al’umma da ‘yan bindiga suke yi har ya haifar da da yawa garuruwa da dama sun tarwatse gudun hijira ya zama ruwan dare ga al’umma. A Zamfara babu wani yanki dake zaune lafiya wanda ba cikin fargaba yake ba na harin ‘yan ta`adda a kowane lokaci akwai ƙauyuka da dama sanadiyar ‘yan bindiga suna kai masu hare-hare sun gudanarda gudun hijira a cikin jahar Zamfara, a ƙaramar hukumar mulki ta Gusau akwai garuruwa kamar haka: Mada, Shemori, Ruwan Ɓore, Fegin Mahe, Gora, ‘Yar Geba, Kundumau, Nawaje, Bantsa, Totari, Gyatta, Yankin Magami Wanke Da Rijiya daɗin-da-ɗa-wa har da garin Damɓa da wasu sassa na cikin garin Gusau. Akwai ƙauyuka a ƙaramar hukumar Tsafe da dama hasali ma babu wata ƙaramar hukuma da za tayi iƙirarin cewa ba ta cikin matsalar hare-haren ‘yan ta`addda a cikin faɗin jahar saboda haka gwamnatin jahar ta ƙirƙiri horar da ma`aikatan sa-kai, nan take domin magance matsalar tsaron jahar. Sune waɗan da za su rinƙa yin sintiri lungu da saƙo a cikin jaha ba dare ba rana tare da jami`an tsaro domin daƙile hari na ‘yan bindiga a faɗin ƙasar ta Zamfara.

5.0              SAKAMAKON BINCIKE

Kamar yaddan bayanai suka gabata a sama, wannan muƙala ta yi tozali ne da muhimmancin ma`aikatan sa-kai tare da faɗakar da al`umma irin muhimmancin da suke da shi a cikin harkar tsaron jahar kuma don haka ne gwamnatin Zamfara ta ƙaddamar da su nan take domin taimakama jami`an tsaro a kai ƙarshen matsalar tsaro wadda ta daɗe tana cima kowa tuwo a ƙwarya, saboda a samawa al’ummar jahar zaman lafiya.

a)        An ƙara samawa jahar ta Zamfara ma`aikatan tsaro waɗan da zasu taimakama jami`an tsaro a kodayaushe domin kawo agajin gaggawa ga al’umma.

b)       Sanadiyar haka za`a gane ɓata gari da ke cikin al’umma musamman saboda irin matakin da gwamnati zata ɗauka a hukumance.

c)        Ta haka ne aka gano mafakar su da maɓoyarsu da kuma masu yi masu safarar makamai da abinci da kayan shaye-shaye.

6.0    SHAWARWARI

Bisa ga ababen da wannan muƙala ta binciko ake ganin akwai buƙatuwar a bayar da shawarwari kamar haka

  i.Shawara ta farko; kamar yadda su ma`aikatan sa-kai suka sanya kansu tare da ra`ayinsu na taimakon garuruwansu, jaharsu da ƙasa baki ɗaya yakamata su shiga wannan aiki da zuciya ɗaya kuma suji tsoron ALLAH, kuma su haɗa kansu su zama tsintsiya maɗauri ɗaya, kada ka zama ana yin tuƙa kana walwala, ka yaudari ‘yan uwan aikin ka, ka cutar da al’ummar da suka aminta dakai kaci amanar jahar ka kasani ALLAH bazai ƙyale kaba tun a duniya.

ii.Shwara ta biyu; ita ce gwamnati ta sani, aiki ya dawo gareta wato shaho ya ɗauki raƙumi, ta kula dasu wato ma`aikatan da ta ɗauka na sa-kai da kula da s haƙƙokin su da sama masu manyan makamai da haɗa su da jami`an tsaro da koya masu dabarun yaƙi tare da basu shawarwari kodayaushe da nuna masu soyayya da yaba masu idan sunyi ƙoƙari wajen aiwatar da aikin su. Dubon irin matsalolin da anka samu a baya ga gwamnatocin da suka gabata, sai bayan an horar dasu kuma yaudara ta shiga daga baya gwamnati tace ko ta amsa akan maganar sulhu da ‘yan ta`adda ta hakane suke bin su ɗai bayan ɗai suna kashewa, ta riƙe wannan alƙawali na babu sulhu tsakaninta dasu.

iii.Shawara ta uku; ita ce wannnan shawara ta faɗa ne ga al’ummar jahar suyi tsaye wajen yima gwamnati addu’a tare da waɗannan bayin ALLAH da suka sadaukar da kansu suka shiga wannan aiki na kariyar al`umma.

7.0 KAMMALAWA

 Wannan muƙala kamar yadda bayanai suka gabata wani yunƙuri ne na hasko muhimmancin ma`aikatan sa-kai a kan harkar tsaron jahar Zamfara da al’ummar jaha da ƙasa baki ɗaya wanda zai kawo ƙarshen ‘yan ta`adda da ta`addanci a faɗin jahar baki ɗaya.

Post a Comment

0 Comments