Ticker

6/recent/ticker-posts

Zinar Mai Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Matar aure ce ta yi zina, daga baya kuma ta tuba, kuma ta nemi mijinta ya yafe mata. To tambaya ita ce: Yaya hukuncin aurensu? Taubatun Nasuuhah na iya kankare mata zunubanta duk da ba a yi mata haddi ba? Menene matsayin mijin da ya cigaba da zama da ita bayan ya yafe mata, domin wai ya rufa mata asiri kuma don kar ’ya’yansu su tozartu? Menene matsayin abin da mijin ya yi a mahangar shari’a?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Da farko dai Ubnagiji Ta’aala ya ce

ٱلزَّانِی لَا یَنكِحُ إِلَّا زَانِیَةً أَوۡ مُشۡرِكَةࣰ وَٱلزَّانِیَةُ لَا یَنكِحُهَاۤ إِلَّا زَانٍ أَوۡ مُشۡرِكࣱۚ وَحُرِّمَ ذَ ٰ⁠لِكَ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِینَ

Mazinaci ba ya yin aure sai da mazinaciya ko mushirika, ita kuma mazinaciya babu mai auren ta sai dai mazinaci ko mushiriki, kuma an haramta hakan ga muminai. (Surah An-Nuur: 3).

Saboda dalilin wannan ayar da makamantanta ne malamai suka yarda cewa: Ba ya halatta a ɗaura aure da mazinaci ko mazinaciya, haka ma a tsakanin su kansu mazinatan har sai sun tuba, kuma sai matar ta gama istibra’i.

Amma idan a bayan an ƙulla auren ne wani daga cikinsu ya afka cikin wannan masifar ta zina, to a nan malamai suna ganin auren bai warware ba saboda hakan. Sai dai idan su maauratan ne da kansu suka warware shi, kamar idan mijin ya saki matar, ko kuma idan ita ta zaɓi rabuwa da shi.

Idan kuma suka zaɓi su cigaba da zama tare, to wajibi ne su nisanci saduwa da juna har sai matar ta yi istibra’in da zai nuna cewa babu komai a cikin mahaifarta bayan zinar da ta yi.

Tuba ta-gaskiya (Taubatun Nasuuhah) ta isa ta kankare kowane irin zunubi, in shaa’al Laah. Kuma haddi yana zama wajibi ne a lokacin da maganar ta kai gaban alƙalin musulunci. Amma kafin nan, ba za a ce wajibi ne sai mai laifi ya kai kansa don a tsayar masa ba.

Cigaba da zama da matar da mijin ya yi daidai ne, bai yi laifi ba a shari’ance. Kamar dai yadda ita ma matar take iya haƙurin cigaba da zama da shi idan shi ne aka samu da laifin.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments