Ticker

6/recent/ticker-posts

Tijjaniyya Zan Bi, Ko Qadiriyya, Shi'ah Ko Ahlus Sunnah Wal Jama'ah

TAMBAYA (91)

Assalamualaikum warahmatullah MLM mene alaqar addini da dariqa, kamr kadiriyya tijjaniyya halissunnah shin yazama dole mutum seya kasance yna cikin Daya dga cikin wayennan NE ko y abin yake, sbd ni a iya sanina ban tabajin ance manzon Alalh Dan dariqa kaza ne Ko Dan dariqa kaza ba don Allah Karin bayani nke bukata ahuta lfia se naji amsa ta

AMSA

Alhamdulillah

Da farko dai, batu akan rarrabuwar kan al'umma abune wanda yake dole, ba makawa sai anyi shi kamar yanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya fada

Annabi (SAW) yace: "Duk wanda a cikinku ya rayu, bayan na rasu, to zai gai manyan fitintinu iri-iri"

Abu Dawud (4067), al-Albaani ya inganta hadisin a cikin Sahih Abu Dawud

Kungiyoyi sun bayyana a bangaren siyasa da kuma aqida, a bayan zamanin kalifofi shiryayyu wato Khulafa'ur Rashidun (Abubakar, Umar, Uthman da Aliyu, Allah ya kara musu yarda baki daya), kamar irinsu kungiyar Shi'ah, Murji'is da Khaawarij

Cikin rahamar Allah Azzawajallah, ya tsara cewar wadannan kungoyoyi zasu bayyana ne yayinda musulmai suka qyale hanyar daidai, suka kirkiro tsarinsu na son rai, kuma ana iya gane su ne ta hanyar sunan da suke dauke dashi. Don haka aqidar Ahlus Sunnah Wal Jama'ah da kuma aqidar mafi yawan musulmai babu wani kokwanto ko kuma shakku a cikinta sabanin sauran aqidun can na bidi'ah da suke alaqanta kansu da sunan wanda ya fara kafa kungiyar. Zaka gane haka a lokacin da ka kalli sunayen aqidojin kamar irinsu Shi'ah wanda su gaba daya ma suna danganta kansu ne da Kungiya kuma Allah Azzawajallah yace kada ku zamo Shi'an wato kada rarrabe ku zamo kungiya kungiya

Shahararren hadisin da yayi bayani akan rarrabuwar kungiya shine hujja akan hakan

An karbo daga Mu'awiyah Bin Abu Sufyan, yace: Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace: "Wadanda suka gabaceku daga cikin mutanen da aka bawa littafi sun rarrabu kaso 72, wannan al'ummar tawa kuma zata kasu kaso 73, kaso 72 duk yan wuta ne, kaso 1 ne kadai yan Aljannah, wadannan sune Jama'ah"

Abu Dawood (4597) da wasunsa; al-Haakim yace Sahih Hadith ne da yake nuna muhimmancin aqidah (1/128), Ibn Hajar al-Asqalani yace Sahih Hadith ne, a cikin Takhreej al-Kashshaaf (63). Ibn Taymiyah yace Sahih Hadith ne a cikin Majmoo’ al-Fataawa dinsa (3/345), haka ma Imam al-Shaatibi a cikin al-I’tisaam (1/430), da kuma al-‘Iraaqi a cikin Takhreej al-Ihya’ (9/133)

Malaman Ahlus Sunnah da yawa sun rawaito wannan hadisi, hakama Sahabbai da isnadai dayawa, akan cewar al'ummar nan zata rabu kaso 73

Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya kira su da "Jama'ah" ma'ana "Ijma'in malaman musulunci" a wata riwayar kuma "adadi masu yawa" kamar yanda yazo a cikin Hadisin Abu Umaamah da wasunsa, wanda aka rawaito daga Ibn Abi ‘Aasim a cikin al-Sunnah dinsa (1/34) da kuma al-Tabaraani a cikin al-Mu’jam al-Kabeer (8/321), da isnadi hasan li ghayrihi (saboda tarin hujjojin hadtarin

Haka kuma Annabi Sallallahu alaihi wasallam yayi bayaninsu a wani hadisin, yace: "Al'ummata zasu rabu kungiya 73, kowannensu zasu shiga wuta face kungiya 1". Sai sahabbai (Radiyallahu anhum) suka ce: Su wanene ya Rasulullah ?. Sai yace: "Sune masu bin abinda nake akai tare da sahabbai na"

Kamar yanda aka rawaito daga ‘Abdallah ibn ‘Amr ibn al-As, kamar yanda Imam al-Tirmidhi ya kawo shi (2641). al-‘Iraaqi yace Sahihi ne a cikin Ahkaam al-Quran (3/432), da kuma Takhreej al-Ihya’ (3/284) sannan kuma Imam al-Albaani ya hassana shi a cikin al-Tirmidhi.

Da wadannan hujjojinne musulmi zai gane hakikanin gaskiyar hanyar da ya kamata ya bi, ta malaman hadisi wadanda aka yarda da iliminsu, kuma hanyar Salaf-Us-Saleh wato mahangar Sahabbai, Tabi'ai da Tabi'ut'tabi'in, da kuma limaman shiriya na mazhabobinnan guda 4 (Imam Ahmad Bin Hanbal, Imam Malik, Imam ash-Shafi'i, Imam Abu Hanifa) da sauran magabata na kwarai tareda taka tsantsan don gudun fadawa hanyar yan bidi'a

Shaykh al-Islam Ibn Taymiyah (Rahimahullah) yace: "Alamun musulmi dan Bidi'ah shine zaka ga baya bin tafarkin Salaf"

Majmoo’ al-Fataawa (4/155)

Haka kuma yace (3/346): "Alamun wannan kungiyoyi guda 72 da suka barranta daga Ahlus Sunnah wal-Jama'ah sune zaka ga sun bar koyarwar Qur'ani, Sunnah da Ijma'in malamai. Duk wanda yake bin Qur'ani da Sunnah da Ijma'in malamai wannan shine wanda yake kan tafarkin Ahlus Sunnah wal-Jamaa'ah

Abune wanda bazai taba yiwuwa ba kace ai shiryayyu ko zababbu a cikin 73 dinnan sune kungiyar Shi'ah, ko kuma kace sune karkatattun Sufaye, ko Khawaarij ko Habashis. La, saidai su wadannan kungiyoyi ne na bidi'ah wadanda basa kan hanyar daidai. Gaba dayansu basu yarda da Sayyadina Abu Bakr, ‘Umar, ‘Uthmaan ko ‘Ali (Radiyallahu anhum) ba, ko kuma Imam Abu Haneefah, Maalik, al-Shaafa’i ko Ahmad ibn Hanbal ba.

Shin akwai wani a cikin yan Adam mai hankalin da zai ce wadannan bayin Allah din basa kan shiriya ?

Yi tunani da nazari akan wannan tambayar. Ko iya hujjojinnan ma sun isa su tabbatar maka cewar akwai banbanci mai girma tsakanin Ahlus Sunnah wal-Jama'ah da sauran kungiyoyin Bidi'ah

Ibn Taimiyya (Rahimahullah) yace

Ahlus Sunnah sal-Jama'ah sune kungiyar shiryayyu la'akari da sune mafi yawa (ta bangaren fahimtar addini akan sunnah), sauran kungiyoyin kuma suna bin zato ne da son zuciyoyinsu, kuma babu ko daya daga cikinsu wanda ya kama kafar kusantar adadin yawan kungiyar shiryayyu (Ahlus Sunnah) ballantana kuma yayi daidai dasu

Zaka gansu yan qalilan, kuma ana gane su ne ta hanyar yanda suke watsi da hujjojin Qur'ani da Sunnah da Ijma'in malamai. Masu bin Qur'ani, Sunnah da Ijma'i, wadannan sune Ahlus Sunnah wal-Jama'a

Majmoo’ al-Fataawa (3/346)

Imam Al-Shaatibi (Rahimahullah) ya zayyano sunayen wadannan halakkakun kungiyoyin a cikin littafin al-I'tisaam (1/453-460)

Na biyu kuma;

Malaman Ahlus Sunnah wal-Jama'a sun yi bayani a cikin littattafansu cewar sauran kungiyoyin sune karkatattun yan Bidi'a kuma sun cancanta su shiga wuta saboda bidi'o'in da suka shigar a cikin addinin Allah Azzawajallah. Saidai kuma duk da haka ba kafirai bane ba, musulmai ne wadanda bazasu dawwama a cikin wuta ba

Shaykh al-Islam Ibn Taymiya (Rahimahullah) yace: "Haka kuma, munafukan da suke a cikin kaso 72 din, wadannan Kafirai ne amman su ragowar wadanda ba munafukan cikinsu ba su ba kafirai bane ba duk da yawan zunubbansu. Wasun su suna da daya daga cikin rassan munafurci ko kuma ba su da kalar munafurcin da zai kai zu cikin wuta

Duk wanda kuma yace, kowanne daya daga cikin kaso 72 dinnan kafiri ne to maganarsa ta ci karo da Qur'ani, Sunnah da Ijma'in Sahabbai da kuma Ijma'in malaman mazhabobi 4 da sauransu. Babu wanda yace dukkan kaso 72 din kafirai ne saidai wasu daga cikinsu ne kafiran

Majmoo’ al-Fataawa (7/218)

Hakan na nufin ba kowanne mutum wanda ya kira kansa musulmi bane musulmi na gaskiya, a'a saidai zasu iya zama kafirai da kuma masu ridda kamar irinsu Shi'ah Raafidis, da kuma Sufayen da suka wuce gona da iri, da kuma kungiyar Baatiniyya kamar irinsu Druze, Nusayris da sauransu. Wadannan duk sun fita daga musulunci kuma ba'a saka su a cikin kaso 72 dincan na Hadisi

Na uku;

Dalilin samun rabuwar kan al'ummah kamar yanda hadisin ya tabbatar, yana da alaqa da addini da kuma aqeedah, bawai banbancin ra'ayi na fiqhu ba

Al-Shaatibi (Rahimahullah) yace: "Wadannan kungiyoyi ne saboda sun banbanta da shiryayyu ta bangaren addini da kuma shari'ah, bawai akan kananan abubuwa ba saboda samun banbanci akan kananan abubuwa ba ya kaiwa ga rabuwa, ana samun rarrabuwar kai ne silar banbance-banbancen da suka shafi addinin musulunci"

Al-I’tisaam (1/439)

Idan har wata kungiya ta musulmai ta ware kanta daga wasu saboda salon da'awah da kuma wasu ayyuka na addini, amman basu ci karo da aqidar Ahlus Sunnah wal-Jama'ah ba, hakan bazai sa a kira su da dulmiyayyu ba, saidai su shiryayyu ne, ma damar suna bin koyarwar Sahabbai da Tabi'ai a aqida da kuma ayyuka

Dangane da kungiyoyin Tijjaniyya, Qadiriyya da sauransu, wadannan suma suna bin abinda wadanda suka fitarda kungiyar suka tsara ne. Tijjaniyya suna bin abinda Ahmad Tijjani ya kawo, suna amfani da littattafai irinsu "Jawaahirul Ma'ani" da kuma "Jawaahirul Masa'id" wanda Ibrahim Inyas ya rubuta, kuma littafin cike yake da shirka kala-kala

Idan kana son gane mecece dariqar Tijjaniyya, ka je ka karanta littafin "ad-Dariqatut Tijjaniyya" da kuma "Shaikh Inyas as-Singali" wallafar Prof. Dahiru Maigari (wanda shi Prof. a gidan kaulaha ya taso, shine yayi project/thesis dinsa na PhD akan wannan dariqar)

Kungiyoyi 72 dincan sune suka fantsama suka kara fitarda wasu sabbin kungiyoyin masu zaman kansu a yanzu, ma'ana, kungiyar Sufanci itace ta haifi Tijjaniyya

Duk zaka ga sunan kungiyoyin yana komawa ga sunayen mutanen da suka kirkirosu, kamar Qadiriyya, asalinta, Abdulqadir Jilani da dai sauransu

Haka kuma idan muka duba littattafai irinsu "Then I was Guided" wallafar Muhammad al-Tijani, wanda da ya kasance dan Shi'ah ne amman daga baya ya koma dariqar Tijjaniyya, shine ya rubuta wancan littafin ma'anarsa shine: "Yanzu na shiryu", a tunaninsa shiriya tana cikin dariqar Tijjaniyya ba Shi'ah ba, zamu gane cewar indai ba Ahlus Sunnah wal-Jama'ah ka bi ba to dole zaka bi hanyar wadancan dariqun

Yakai dan uwa, mai tambaya, ina roqon Allah ya jikanmu da rahama, cewar baka taba jin Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya bi dariqa ba wannan haka yake amman ya dora Sahabbansa akan tafarki madaidaici wato bin sunnarsa

Ko dai mu bi sunnar sa ko kuma mu bi wata dariqar. Zabi ya rage ni da kai da sauran musulmai

Kuma mu sani cewar Munkar da Nakir, ba zasu tambaye ka Minhaj dinka a kabari ba, saidai za su tambaye ka: "Menene addininka", idan ka ce musu Izala to wuta zaka je, Tijjaniyya wuta, Qadiriyya, Shi'ah duk ba ruwansu da wannan amsar, saidai kace musu, addini na shine musulunci

Kenan Ahlus Sunnah ko kuma Salaf minhaji ne ma'ana hanyace ta neman ilimin addini ta yanda mutum bazai fada Bidi'ah ba

Duk da amsar zata ci karo da son zuciyar wasu to amman ita gaskiya daci ne da ita kuma bulalar kan hanyace, fyadi yaro fyadi babba. Ya kake tunani idan mai ciwo ko kurji yana son rabuwa da wannan gwalandon, idan aka kaishi asibiti dole ya hakura a diddirje wannan gwalandon ko zaiyi kukan jini kuwa, to kamar haka ne shi ma wannan rubutun, ana so a gyara aqidar mutane ne, kuma zafin gyaran yafi zafin wanda akewa dorin karaya, kuma hujjojine gasunan muraran a rubuce ga duk dalibin ilimi mai son gaskiya sai ya dubo su. Ban bada amsar nan da son zuciyata ba, tunda magana ake ta aqidah, sannan idan akwai gyara sai a sanar damu mu bi diddigi mu gyara

Ina fatan dan uwa ya gamsu da amsar tambayarsa

Allah ya tabbatar damu akan bin Sunnar Annabi Sallallahu alaihi wasallam bisa minhajin Salaf (magabata na farko)

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments