Tuwon Shinkafa
A ƙarƙashin 5.9 da ke babi na biyar an kawo bayani game da tuwon shinkafa. Yadda ake sarrafa shinkafa a gargajiyance ya bambanta da yadda abin yake a zamani. Gumi ko sussukar shinkafa da ake yi a zamanance ya sa shinkafar zamani ta fi tsafta da kyan gani sama da ta gargajiya.Dalili kuwa shi ne, an samu kayayakin zamani da ake amfani da su wajen sarrafawa. Takan kasance mai haske da tsawo tare da tsafta. A ɓangaren tuwo kuwa, ɗan bambanci da ake samu bai fi a wajen kayayakin da ake amfani da su ba. A zamanance, akan sanya manyagyaɗa a wajen kwasar tuwon. Bayan haka, ana iya naɗewa a leda.
Tuwon Alkama
i. Alkama
ii. Ruwa
Yadda ake tuwon alkama kusan ɗaya
yake da na gero. Sai dai wani lokaci akan yi talge
guda biyu a tuwon alkama. Sannan akan ma iya sanya ta ba tare da talge ba. Wato
a tuƙa haka nan bayan ruwa ya tafasa. Nau’i
ne na tuwo da ke da ƙara
lafiya ga jikin ɗan Adam. Wannan ne ma ya ake shawartar
marasa lafiya da tsofi su riƙa
cin wannan tuwo.
Tuwon Acca
i. Acca
ii. Ruwa
Tuwon acca ya fi kama da na shinkafa. Ana iya tuƙa tuwon ba tare da an kai niƙa ba, kamar dai yadda ake na shinkafa. Sai dai idan aka kai niƙa ɗin ma ba laifi. Bayan ruwa ya tafasa, haka ake sanya ta domin ta dafu sosai kafin a tuƙa. Ana cin wannan tuwo da nau’o’in miya daban-daban.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.