Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halatta Musulmi Yaci Abincin Kirsimeti?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Allah ya karama rayuwar Malam albarka, shin ko ya halatta Musulmi yaci ko ya sha duk wani abu da kiristoci suka kawo masa na bukukuwan su kamar chrismas, New Year, Good Friday, Easter Monday da dai sauransu. Wassalam.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

A matsayin ka dai na musulmi, ya zamo wajibi ka kƴamaci kafirci da kafiri, kamar yadda Annabi Ibrahim da mutanen sa suka koyar mana, ballantana wani idi na su ko abin da za'a girka saboda idin, Allah yace

قَدْ كَانَتْ لَكُمْ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ فِي إِبْرَاهِيمَ وَالَّذِينَ مَعَهُ إِذْ قَالُوا لِقَوْمِهِمْ إِنَّا بُرَآءُ مِنْكُمْ وَمِمَّا تَعْبُدُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ كَفَرْنَا بِكُمْ وَبَدَا بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمُ الْعَدَاوَةُ وَالْبَغْضَاءُ أَبَدًا حَتَّىٰ تُؤْمِنُوا بِاللَّهِ ...

Lalle abin kõyi mai kyau ya kasance a gare ku game da Ibrãhĩm da waɗanda ke tãre da shi a lõkacin da suka ce wa mutnensu, "Lalle mũ bãbu ruwanmu daku, kuma da abin da kuke bautãwa, baicin Allah, mun fita batunku, kuma ƙiyayya da jiyewa jũna sun bayyana a tsakãninmu, sai kun yi ĩmãni da Allah Shi kaɗai."  [Surah Al-Mumtahana 4]

Wasun mu na ɗaukar cewa rashin karɓar su ko abincin su, ko taya su murnar arnancin su, yi masu laifi ne, ko nuna mummunar zamantakewa ne da dai sauran su, a'a, ba haka bane. "LAKUM DINIKUM, WA LIYA DINI". Hakan ba laifi bane ko mummunan zama ba, domin ba zai hana kuma ka gaisa da shi ko ka ci abincin sa a wata ranar ta daban ba. Don haka ya kamata mu wayar da kan ƴan'uwan mu dangane da haka, don kawai kana cewa da ni happy sallah, bai zamo ni kuma na ce da kai happy Christmas, don ina kan gaskiya ne, kai kuma kana kan ƙarya ne, kuma asali ban da bukatar ka saka man baki cikin sha'anin addini na ba.

Bayan wannan, abinci dai iri biyu ne, wanda yake bukatar haɗa shi da gyara shi da yin aiki a kan sa, kafin ayi amfani da shi, kamar shinkafa, taliya, farfesu, nama, soye, zoɓo, kunun zaƙi, da sauran su.

Akwai kuma irin wanda baya bukatar wata ɗawainiyar mutum kafin ayi amfani da shi, kamar  gwaba, ayaba, lemu, gwanda, biskit, minti, cakulat, jus, lemun kwalba, da sauran su. Babu saɓani a tsakanin Mallamai kan cewa ya halasta mutum ya ci ko ya sha irin wannan nau'i na kayan abincin na biyu.

Amma a wancan irin nau'in abinci na farko, akwai maganganu Mallamai a kan sa. Da farko dai babu saɓani a kan halascin cin shinkafa, taliya da duk abin da baya bukatar yanka ko da yana bukatar gyaran mutane. Amma irin abin da yake na sha, sai an duba, idan basu haɗa shi da giya ko wani sinadarin da shari'a ta haramta wa musulmi ba kafin a sha, ya halasta musulmi ya sha. Hakan yasa wasu ke ganin cewa barin kunun zaƙin su da abin da yayi kama da shi, shine aula da zama lafiya.

Amma akwai saɓani tsakanin Mallamai dangane da halascin cin abin da sai an yanka, kamar farfesu, soye ko gasashshen naman da arna zasu baka. Ga bayani filla-filla, Mallamai sun kasa irin wannan nama kashi biyu, akwai irin naman da ba don wani idi daga cikin idin su suka yanka shi ba, irin wannan ya halasta musulmi ya ci.

Akwai irin naman da ahlul kitabi ya yanka, amma ya ambaci sunan wanin Allah, wasu Mallamai sun ce bai halatta ba. Masu irin wannan fahimtar ta haramci, sune Hanafawa, Shafi'iyya, da Hanabila, amma Malikiyya suka ce karahiya ne. Imamu Ibn Rushd, a littafin sa, Bidayatul Mujtahid, ya ambata sababin saɓani su, shine, samun ayoyi biyu da suka yi ta'arudhi. Ɗaya dake Ma'idah da ta halasta yankan ahlul kitabi, da kuma ɗayar ayar ta An'am da ta haramta cin yankan da aka ambaci sunan wanin Allah. Waɗanda suka game ma'anar ta Ma'idah, sai suka haramta, waɗanda suka game hukuncin ta An'am sai suka halasta cin kowane yanka na kirista, na idi, da wanin sa, saboda ƙa'idar Usulu, ta rajjaha Khas a kan Amm.

Amma yankan da aka yi don wani idi daga cikin idin su, Mallamai sun kasu gida uku, wasu sun ce Haramun ne, ita mazhabar Shafi'i da ɗaya daga Hanabila, kuma shine ra'ayin Ibn Taimiyyah. Koma ga maj'mu'ul fatawa 8/409.

Karahiya ne, wannan ita ce mazhabar abin da ya inganta na Hanabila da Malikiyya. Koma ga manhul Jalil 2/414.

Halas ne, wannan ita ce mazhabar Hanabil koma ga Al'insaf 10/307.

A taƙaice dai kuma daga ƙarshe, yankan ahlul kitabi yana haramta ga musulmi ya ci, idan ya ambaci sunan wanin Allah, ko na idin su ne, ko ba don idin su bane. Amma cin yankan su na zama karahiya ne, idan anyi yankan don girmama idin, ko da ba tare da an ambaci sunan wanin Allah ba.

WALLAHU TA'ALA A'ALAM.

 Amsawa

 Malam Aliyu Abubakar Masanawa

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments