Hukuncin Cin Abincin Kirsimeti

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Shin ko ya halatta Musulmi ya karbi abincin kirsimeti yaci?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Alalhaƙiƙa an samu saɓanin Malamai dangane da hukuncin musulmi yaci abincin da Ahlulkitabi (yahudawa da kiristoci) sukayi dan saboda murnar wani biki daga cikin bukukuwansu kamar misalin irin bikin kirsimeti.

    Wato asali dai ya halatta idan kafiri ya bawa musulmi kyauta ya karɓa, domin hakan na iya janyo hankalinsa ya sanya shi yaji yana sha'awar musluncin, kamar yadda aka ruwaito cewa Mαnzσn Allαh Sallallahu alaihi Wasallam yana karɓar kyautar da kafirai suka ba shi. Haka nan asali ya halatta musulmi ya bawa kafiri kyauta musamman ma da nufin janyo hankalinsa zuwa ga muslunci, amma bai halatta ba musulmi ya bawa kafiri wata kyauta a ranar idin su (kafirai) ko bukukuwansu, domin yin hakan kamar yayi taimakekeniya ne a kan shirkar da sukeyi, haka nan ba ya halatta ga musulmi ya bawa ɗan'uwansa musulmi wata kyauta a ranar da kafirai suke idinsu (bukukuwansu) idan ya ba shi ne da nufin taya kafirai murna a wannan ranar da kuma girmama wannan bikin da sukeyi.

    Haka nan ba ya halatta ga musulmi ya sayarwa da kafirai dukkan wani abinda za su yi amfani dashi na shirka awajen bautarsu.

    To sai dai Malamai sunyi saɓani game da kyautar da kafiri ze yiwa Musulmi a ranar wani biki daga cikin bukukuwansu kamar ranar kirsimeti. Wasu daga cikin Malamai sukace babu laifi Musulmi ya karɓi kyautar da kafiri yayi masa a ranar kirsimeti amma da sharadin ya kasance abinda a kayi kyautar da shi dama asali halal ne a wajen musulmi yayi amfani da shi, sukace karɓarsa ba ta nufin cewa ya yarda da abin da sukeyi, haka nan kuma karɓar kyautarsu ba ta nufin an temake su akan shirkarsu ba, sai dai abin lura a nan shi ne, Malaman da sukace ya halatta a karɓi kyautar kirsimet to suna magana ne akan abinda ba yanka ba ne, wato suna magana ne akan kamar abincin da suka dafa ko 'ya'yan itatuwa da makamantansu.

    Amma idan suka yanka wata dabba da nufin bikin idin su (kirsimet) to bai halatta musulmi ya ci ba, duk da cewa asali a shari'ance ya halatta a ci yankansu kuma a auri matansu, to amma a nan ya zama haramun ne saboda sunyi yankan ne da nufin wannan bikin na su.

    Sai dai kuma a gefe ɗaya akwai Malaman da sukace haramun ne musulmi ya karɓi dukkan wata kyauta da wani kafiri zai ba shi a ranar idinsu (kirsimet), kuma ko da mene ne in dai an yi shi ne ko an tanadeshi saboda wannan rana ta kirsimet to bai halatta ya karɓa ba, waɗannan Malamai sukace idan Musulmi ya karɓi kyautar kafiri a ranar idinsa, to kamar yayi taimakekeniya da aikin ɓarna ne.

    Sannan kuma girmamawace a garesu da ƙarfafarsu akan suci gaba da yi da kuma tayasu murna da farin ciki a kan ɓarnarsu.

    шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

               Mυѕтαρнα Uѕмαи

                  08032531505

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.