Ticker

6/recent/ticker-posts

Masana’antar Ƙyanƙyasar Jarirai

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Menene hukuncin addini a kan masana’antar ƙyanƙyashe jarirai da turawa suka ƙirƙiro a kwanan nan? Ko ya halatta musulmi su bi wannan hanyar maimakon hanyar da aka saba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Tun tuni da ma akwai wannan shirin da waɗansu azzalumai daga cikin shugabannin turawa ’yan jari-hujja suka somo shi, na ƙirƙiran wannan masanaantar da manufar ƙera jarirai. Dalili wai domin taimaka wa mawadatan da suke buƙatar a dasa musu waɗansu sassan jikinsu da suka lalace, kamar ƙoda ko hanta ko zuciya da makamantan hakan. A shekarun baya an yi ta raɗe-raɗin cewa, daga maza da mata baƙaƙen fatar Afirka - musamman Najeriya - za a samo miliyoyin ƙwayayen haihuwar da za a yi amfani da su a waɗannan masanaantun.

Wannan kuwa mummunan ta’addanci ne da ya saɓa wa dokokin ƙasa-da-ƙasa bayan kuma saɓawansa ga dokokin Ubangiji Tabaaraka Wa Ta’aala. Musamman dayake za a yi amfani ne da hanyar takurawa da yunwatarwa har sai dole mutane sun yarda sun karɓi la’antaccen shirin. Wannan kuwa babbar hanyar take haƙƙin ɗan Adam ne, kamar yadda ya ke a fili. Don haka bai halatta wani ko waɗansu su taimaka wa wannan sheɗanin shirin ba, ko da me kuma ko don me.

Amma idan za a yi amfani da irin wannan masana’antar domin taimaka wa ma’auratan da suka kasa samun haihuwa ta yadda aka saba ne kaɗai, ba tare da wata mummunar manufa a ɓoye ba, to ba za a hana hakan ba, in shaa’al Laah. Saboda a nan akwai ƙaidar da malaman Fiqhu suka kafa mai nuna cewa: Asali a kan abubuwa irin waɗannan shi ne halacci, ba a hana komai sai abin da Allaah Ta’aala ya hana a cikin Alqur’ani ko kuma a kan harshen Annabinsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam).

A gaskiya abin da ya fi kawai, gara matan musulmi su yi haƙurin ɗauka da goyon cikin jariransu a cikin cikunnansu kawai yadda Allaah ya tsara kuma aka saba, yadda kuma iyayensu suka ɗauke su har kuma suka haife su. Musamman datake kuɗaɗen da za a kashe wurin amfani da sabon injin ƙyanƙyasar ba ƙanana ba ne. Maƙudan kuɗaɗe ne da talakawan ƙasashen musulmi masu yawa suke da buƙatarsu domin cigaba da rayuwa.

Haka kuma maimakon neman haihuwa ba ta hanyar da aka saba ba, kar a manta da abin da muka ambata a cikin amsar Tambaya ta A339 cewa, abin da ya fi ga ma’aurata a irin wannan halin shi ne: Su yi haƙuri, su mayar da alamarin ga Allaah Ubangijin Halittu, su yi ta roƙonsa don ya ba su na-gari daga falalarsa. Haka manya, irinsu Annabi Zakariyya (Alaihis Salaaam) ya yi a cikin Surah Al-Imraan

هُنَالِكَ دَعَا زَكَرِيَّا رَبَّهُ قَالَ رَبِّ هَبْ لِي مِنْ لَدُنْكَ ذُرِّيَّةً طَيِّبَةً إِنَّكَ سَمِيعُ الدُّعَاء

A can ne Annabi Zakariyya ya roƙi Ubangijinsa, ya ce: Ya Ubangijina! Ka yi mini baiwar zuriya kyakkyawa, lallai ne kai mai jin addua ne. (Surah Al-Imraan: 38).

Wannan shi ya fi alkhairi gare su a duniya da barzahu da lahira, fiye da su bijirar da kansu ga buɗe tsiraicinsu a gaban waɗanda ba muharramansu ba, kuma a kan abin da bai zama dole a kansu ba a shari’a.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RQbbrzgW

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments